15/07/2026
SHIN LAIFINE MUSULMI YASHIGA COCIN KIRISTOCI ?
Allah madaukaki ya halicci yan Adam seyayisu Kashi biyu domin bayyana cikar ikonshi da hikamarshi;
1) Kaso nafarko Sune wadanda Allah yadatardasu dayin Imani
2) Kaso na biyu su ne wadanda Allah benufesu dashiriyaba.
Wannan wata irin hikimace ta Allah domin yajarrabi bayinsa yaga shin masu Imanin zasu dawwama cikin imaninsune ko zasu sauya. Shiyasa Allah yace:
يا أيها الذين آمنوا اتقوا الله حق تقاته ولا تموتن إلا وأنتم مسلمون
"YAKU WADANDA KUKAYI IMANI DA ALLAH KUJI TSORON ALLAH GASKIYAR TSORONSA KUMA KADA KUMUTU FACE KUNA MUSULMI"
Allah yahada alaqa tazamantakewa tsakanin Musulmi da wadanda ba musulmiba domin jarrabawa. Kuma domin Musulmi suyi dukkan meyiwuwa wajen ganin;
1) sun tabbata cikin musulunci
2) sunjawo wadanda ba musulmiba zuwaga addinin musulunci.
Wannan yasa Allah yatsara cewa waenda ba musulmiba, kafirai na amana suna cikin waenda musulunci ke baiwa zakka domin keutatawa garesu dakuma kokarin jawosu zuwaga addinin musulunci
والمؤلفة قلوبهم
Muamala mekeu danuna halayya takirki sunfi saurin jawo waenda ba musulmiba izuwa ga musulunci. Wannan yasa Allah yatsarkake mana annabinmu daga dukkan dauda, ko kazanta, ko tawaya, ko kaushin hali, ko rashin ladabi, shiyasama Allah yace
وإنك لعلى خلق عظيم
KUMA LALLAI KAI (ANNABI MUHAMMAD) KANA KAN DABI'AH ME GIRMA, DABI'AH MEKEU
ولو كنت فظا غليظ القلب لانفضوا من حولك
DA DAI ACE KA KASANCE (YA KAI ANNABI MUHAMMAD) MUTUM ME KAUSHIN HALI DA ZAFIN RAI DA WADANNAN SAHABBANNAKA SUN WATSE SUN BARKA.
Idan ka fahimci wannar shimfidar kenan dae keutatawa zuwaga kafirae yanada asali a musulunci Kuma kokadan besabama shariah ba. Ga misalai kamar haka;
1) ALLAH MADAUKAKI ya fadi acikin Alqur'ani, a suratul mumtahina
لا يَنْهَاكُمُ اللَّهُ عَنِ الَّذِينَ لَمْ يُقَاتِلُوكُمْ فِي الدِّينِ وَلَمْ يُخْرِجُوكُمْ
مِنْ دِيَارِكُمْ أَنْ تَبَرُّوهُمْ وَتُقْسِطُوا إِلَيْهِمْ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِين
Maana; Allah bai hana ku yin alheri da adalci ga wadanda ba su yake ku saboda addini ba, kuma ba su kore ku daga gidaddajinku ba. Lalle Allah yana son masu adalci.
2) Sahabi Anas Dan Malik ya riwaito mana Hadisi ingantacce daga bakin manzon Allah sallallahu alaihi wasallama Wanda Al imamul bukhary yazo dashi a sahih nashi cewa
كان غلام يهودي يخدم النبي ﷺ فمرض، فأتاه النبي ﷺ يعوده
WANI YARO BAYAHUDE YA KASANCE YANA HIDIMA WA MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA, SEYARON YAYI RASHIN LFY SEGA FIYEYYAN HALITTA YA KAI MASA ZIYARA DOMIN DUBA LAFIYARSHI
SHIN AKWAI LAIFI MUSULMI YAZIYARCI WAJEN BAUTAR KAFIRAI ?
Malamai sunyi bayanai mabanbanta danganeda wannar mas'alar. Duka bayanansu sundogara da abubuwa 2
1) Manufar ziyarar COCIN: idan Manufar itace karfafa hadinkai da fahimtar juna dajawosu zuwaga musulunci danunamusu kyawawan dabi'u na addinin musulunci, to ya halasta Bal ma Yana iya zama wajibi.
2) Abinda yafaru yayin ziyarar; idan mutum na tsoron samunsu adede lokacin suna gabatarda abubuwansu na ibada Kuma bazai iya kaucemusuba to baya halasta yashiga cikin ibadarsu. Idan ze iya zuwa Kuma batareda yashiga cikin hidimar ibadarsu ba to makaruhine yaje.
HALASCIN SHIGA WURIN BAUTAR KIRISTOCI
* Idan har shiga COCIN zejawo Kiran wadannan Kiristocin zuwaga Addinin musulunci to ya halatta bal ma wajibine.
* Yin jaje saboda wani iftilai dayafaru dasu a wurin bautarsu ko agidajensu ko agurin kasuwancinsu inde ze karfafa dangantaka mekeu Kuma baya kunsar shiga cikin addininsu da hidimominsu dasukashafi addininsu to ya halasta. Wannar itace fahimtar IBN Uthaymin
* Manyan malamai magabata sunyi fatawowi dake nuna halascin kekkyawar muamala da kiristoci dayimusu jaje dakuma mika ta'aziya zuwa garesu. Domin takaitawa ga fatawowin malaman kamar haka;
1)Ibnul Qayyim acikin LITTAFIN Ahkamu Ahlizzimmah yake cewa: Amma yi musu ta aziyya ya halatta idan akwai maslahar shari'ah. Amma ba a yi wa mamacinsu addu'ar neman gafara daneman rahama agurin Allah idan ya mutu a kan kafirci.
وأما تعزيتهم فجائزة إذا كان فيها مصلحة شرعية، ولا يدعى لميتهم بالمغفرة والرحمة إذا مات على الكفر
2) Antambayi sheikh IBN Bazz game da ta'aziyyar wadanda ba Musulmi ba, sai ya ce: Idan bukata ko maslaha ta sa a yi musu ta ziyya, babu laifi, domin hakan yana jawo zukata kuma yana taimakawa wajen kiran su zuwa Musulunci.
إذا دعت الحاجة أو المصلحة إلى تعزيتهم فلا بأس بذلك، لما في ذلك من تأليف القلوب والدعوة إلى الإسلام
3) Ash shayk IBN Uthaimin yake cewa; idan yi musu ta ziyya yana da maslahar shari'ah, kamar ana sa ran musuluntarsu ko hana cutarsu, to babu laifi.
إذا كان في تعزيتهم مصلحة شرعية، كرجاء إسلامهم أو كف شرهم، فلا بأس بذلك
NA iya yiwuwa kace To in malami yaje don gyara siyasarshi fa ? Ai kenan ba ya je ne don kiransu zuwaga musulunci ba ?
SE muce dakai:
* Ita kanta siyasa tanada asali a musulunci
* Musulunci Yana bawa shugabanci muhimmanci me girma
* Idan baku aminta daga kiristocin dakuke zaune dasuba to ko kunkafa gomnati bazasu bari Asamu daidaito atsakaniba b***e asamarda ayyuka na raya qasa.
* Don hakadai jawosu ajiki dahikima dakuma yimusu waazi dakiransu zuwaga musulunci shi ne babban aikin Musulmi.
Jinginama Wanda yashiga COCI kalmar RIDDA tabbas abune me hatsarin gaske. Allah yashiryar damu yadatardamu da daidai yahanama duga duginmu zamewa daga tafarkin gaskiya.
Wallahu A'alamu
✍️ Aminu Ali