17/06/2021
Assalamu alaikum,
Yana ɗaya daga cikin manyan ƙudirin KESA wajen ganin ta tallafawa ɗaliɓai ta fannoni daban daban misali; taimakawa ɗalibai da shawara, shigewa ɗalibai gaba dan samar musu da guraben karatu, shiryawa ɗalibai bitar jarabawa da kuma yiwa ɗalibai hidima da asusun ƙungiya daidai gwargwadon iyawar ta.
Hakan neh ma yasa ƙungiya kwanukan da s**a shuɗe ta shirya shiri na wayar da kai ga ɗaliban masarautar akan jarabawar samun gurbin karatu a makarantun gaba da Sakandire wato (JAMB) inda ɗaya daga cikin manyan masu bawa ƙungiya gudunmawa kuma fasihin Malamin na'ura mai ƙwaƙwalwa wato Malam Murtala Kazaure ya gabatar da shirin a Polytechnic dake garin Kazaure, tare da kuma tabbatarwar Ƙungiya na daukar nauyin jarabawar duk ɗalibin da ya halarci taron wanda s**a fito daga yankin Kazaure, Roni, Gwiwa da kuma Ƴankwashi.
Malam ya gabatar da bayaninsa akan abubuwa kamar haka:
1- Muhimmancin yin karatu mai zurfi ga ɗaliban masarautar.
2- Bayar da shawarar akan haɗakar darussan da ɗalibai zasu haɗa domin samun gurbi a makarantun Jami'a.
3- Bayar da shawara akan neman karatu akan fanni da ɗalibi yake da ƙwarewa.
4- Daga ƙarshe Malam yabawa ɗalibai shawara akan dagewa wajen bitar darussa, domin cimma nasarar cin jarabawar.
Allah ya sakawa Malam da kuma duk wani wanda yake taimakawa wajen ganin Ƙungiya ta cimma burin ta na ɗaukaka martabar ɗaliban masarautar da kuma samar musu da cigaba mai ɗorewa. Sannan ƙofa a buɗe take da duk wani wanda yake ganin zai taimakawa Ƙungiya ta koh wane fanni.
Abubakar Masud,
Mataimaki na musamman kan cigaban Ƙungiya.
Imran Lawan,
Shugaban Ƙungiyar KESA.