29/08/2025
KA KIYAYE FURUCIN KA.
-
Na sani. Wasu halin ɓacin rai kan sasu su furta mummunar magana ga wani abokin rayuwarsu, wasu kuma domin tsokana ko zalunci, amma koma dai a wane hali ne, kuma ko a wane dalili ne, yana da kyau mutum ya iya harshensa, domin shi harshe haɗarinsa nadama ce ƙarshensa.
-
"Baka san yadda baƙar maganarka guda ɗaya rakk za tayi tasiri a cikin zuciyar wanda ka furtata gareshi domin girman muninta gareshi ba, sabida haka ka dinga tsaftace harshenka kafin ka jefa magana ga ɗan-uwanka koda kuwa a cikin halin fushi kake, domin sau da yawa zaka iya yin magana a cikin halin fushi daga baya kuma kazo kana mai yin nadama a kanta"
-
Har kullum ana so shi musulmi ya zamto cewa alkhairi ne kaɗai yake fita daga bakinsa, kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya umurce mu da cewa mu faɗi alkhairi ko kuma muyi shiru.
-
Allah ya sa mu dace.