Isah Rabe Kambarawa

Isah Rabe Kambarawa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Isah Rabe Kambarawa, Educational consultant, Katsina.

13/05/2026

Allah Ya ƙara shiga lamuran Building Your Future Ambassadors

SANARWA GA MANEMA LABARAI

BYFA Ta Kafa Kwamitin Tuntuɓar Masu Ruwa-da-Tsaki Domin Shirya Taron Wayar da Kai Kan Haƙƙoƙin Ɗiya Mace da Tarbiyya

Ƙungiyar Building Your Future Ambassadors (BYFA) ta kafa Kwamitin Tuntuɓar Masu Ruwa-da-Tsaki (Stakeholders’ Engagement Committee) domin gudanar da shirye-shiryen babban taron wayar da kai na yini ɗaya mai taken:

“Haƙƙoƙin Ɗiya Mace, Tarbiyyantarwa da kuma Nauyin da ya Rataya ga Al’umma”
(Girl Child Rights, Moral Upbringing and Community Responsibility).

Kwamitin zai gudanar da tattaunawa da masu ruwa-da-tsaki daga ma’aikatu, hukumomi, masarautu, ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyin mata da masu zaman kansu domin samar da haɗin gwiwa mai ɗorewa wajen tabbatar da nasarar taron.

An tsara wannan taro ne ƙarƙashin shirin BYFA mai suna “Samar da Wurare Masu Tsaro ga Yara Mata da Mata Masu Rauni” (Safe Spaces for Girls and Vulnerable Women Initiative), wanda ke da manufar ƙarfafa kariya, tarbiyya da wayar da kai kan haƙƙoƙin yara mata da mata masu rauni a cikin al’umma.

Kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin makonni biyu, daga yau Laraba, 13 ga Mayu zuwa Laraba, 27 ga Mayu, 2026, in Allah Ya yarda.

Ana sa ran gudanar da ƙayataccen taron a Birnin Katsina ranar Lahadi, 7 ga Yuni, 2026, in Allah Ya yarda tare da halartar iyaye mata, yara mata, ƙungiyoyin mata, malamai, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa-da-tsaki.

Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda, CON, ne zai jagoranci taron, yayin da kwamishinoni, shugabannin hukumomi, shugabannin siyasa da sauran manyan baƙi za su halarta domin nuna goyon baya ga wannan muhimmiyar manufa ta cigaban al’umma, a ƙarƙashin Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka - Building Your Future Strategic Policy (BYFSP) wanda shi ne ruhin Gwamnatin Jihar Katsina.

Kwamitin ya ƙunshi membobin BYFA kamar haka:

1. Isah Rabe Kambarawa (Darakta Janar) - Shugaba

2. Sadiq Abdullahi (Daraktan Mulki) - Memba

3. Binta Isah (Daraktar Lamuran Mata) - Memba

4. Sama’ila Shu’aibu Marke (Daraktan Matasa) - Memba

5. Bello Aliyu Muri (Daraktan Bincike) - Memba

6. Barrister Fatima Tukur (Daraktar Harkokin Shari’a) - Memba

7. Shafi’u Ibrahim (Daraktan Shirye-shirye da Ayyuka) - Memba

8. Zinatu Babangida (Daraktar Haɗin Gwiwa) - Memba

9. Mubarak Saleh Bakiyawa (Ko’odinetan Shiyyar Katsina) - Memba

10. Muttaqa Garba Ɗangamau (Ko’odinetan Shiyyar Daura) - Memba

11. Yusha’u Zakariya Salisu (Ko’odinetan Shiyyar Funtua) - Memba

12. Hussaina Uzairu (Shugabar Mata ta Shiyyar Katsina) - Memba

13. Yahanatu Mustapha (Shugabar Mata ta Shiyyar Daura) - Memba

14. Hadiza Salisu (Shugabar Mata ta Shiyyar Funtua) - Memba

15. Abdullahi Magaji (Ko’odinetan Ƙaramar Hukumar Katsina) - Memba

16. Abdulhadi Rabi’u (Ko’odinetan Ƙaramar Hukumar Ingawa) - Memba

17. Aminu Sani Mu’azu (Sakataren Mulki) - Memba

BYFA ta bayyana cewa wannan taro wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙungiyar wajen haɗa manufofin gwamnati da muradun al’umma musamman a ɓangaren kare haƙƙin yara mata, inganta tarbiyya, da gina al’umma mai kyawawan ɗabi’u.

Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors (BYFA)
Laraba, 13 ga Mayu, 2026
25 ga Dhul-Qa’adah, 1447AH

Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Ibrahima Kaulaha Mohammed
Katsina State Government
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 11/05/2026

Dr. Dikko Umaru Radda

10/05/2026

Masha Allah

Photos from Mobile Media Crew's post 10/05/2026

Masha Allah

10/05/2026

Masha Allah
Dr. Dikko Umaru Radda

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 07/05/2026

Masha Allah
Dr. Dikko Umaru Radda

07/05/2026

Dr. Dikko Umaru Radda

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 05/05/2026

@36 - Mujallar Gina Makomarka

23/04/2026

Masha Allah

SAƘON TAYA MURNA

Dikko Vision Movement na miƙa saƙon taya murna na musamman ga Injiniya Dr. Muttaqa Rabe Darma bisa nadinsa da aka yi a matsayin Ministan Samar da Gidaje da Cigaban Birane na Tarayyar Najeriya.

Wannan babban matsayi da Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya ba shi ya zo ne a daidai lokacin da ƙasa ke buƙatar ƙwararru masu hangen nesa, nagarta da kuma kwarewa a fannin shugabanci. Injiniya Dr. Muttaqa Rabe Darma ya kasance gogaggen ɗan siyasa kuma jajirtaccen mai mulki, wanda tun bayan kammala aikinsa a matsayin Shugaban PTDF, bai gushe ba yana tare da al’ummarsa, yana sauraron buƙatunsu tare da tallafa musu ta hanyoyi daban-daban.

Hakazalika, ya kasance attajiri mai zuciyar bayarwa, wanda ya kafa Umaru Musa Yar’adua Capacity Centre a Jihar Katsina—wani gagarumin cibiyar da ke ba matasa da al’umma damar koyon sana’o’i, ilimi da ƙwarewa domin dogaro da kai.

Muna da cikakken yaƙini cewa, wannan sabon matsayi zai zama wata dama gare shi na ci gaba da nuna ƙwarewarsa da sadaukarwarsa wajen kawo cigaba mai ɗorewa a fannin gidaje da bunƙasa birane a faɗin ƙasar nan.

Muna addu’ar Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin wannan amanar da aka ɗora masa cikin nasara, tare da shiryar da shi a dukkan matakan aikinsa.

Sanarwa:
Daraktan Yada Labarai da Sadarwa
Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026
6 ga Dhul-Qa’adah, 1447

Dr. Dikko Umaru Radda
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State

15/04/2026

Allah Ya albarkaci abin da ta bari. Amin Ya Hayyu Ya Qayyum

Dikko Vision Movement (DVM) ta yi Alhinin Rasuwar Mai ɗakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati

Dikko Vision Movement (DVM) na miƙa saƙon ta’aziyya mai cike da alhini da jimami bisa rasuwar Hajiya Hawwa (Maijidda) Abdulƙadir Mamman Nasir, matar Shugaban Ma’aikata (Chief of Staff) na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina.

Lallai wannan rashi babbar asara ce ba ga mijinta da iyalanta kaɗai ba, har ma da al’umma baki ɗaya, duba da irin gudunmawar da ta bayar wajen tarbiyya, tausayi da kuma kyautata zamantakewa. Mutuwa gaskiya ce, kuma kowa zai ɗanɗana ta a lokacin da Allah Ya ƙaddara.

DVM na jajanta wa mijinta, Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnati, tare da iyalansu da sauran ‘yan’uwa, tare da addu’ar Allah Ya ba su juriya da haƙurin jure wannan babban rashi.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya yafe kura-kuranta, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarta. Haka kuma, Allah Ya ƙara haɗa zukatan waɗanda ta bari a baya, Ya kuma ba su ikon ci gaba da raya kyawawan halayenta.

Za a yi jana’izarta a gobe Laraba, 15 ga Afrilu, 2026, da ƙarfe 1:00 na rana bayan sallar Zuhr a Masallacin GRA. Muna kira ga al’umma da su halarta tare da yi mata addu’ar rahama.

Allah Ya jikanta da rahama, Ya sa Aljanna ce makomarta. Amin.

Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Dikko Vision Movement (DVM)
Talata, 14 ga Afrilu, 2026
26 ga Shawwal, 1447 AH

Dr. Dikko Umaru Radda
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Katsina State Government

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 14/04/2026

Masha Allah

Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Katsina