13/05/2026
Allah Ya ƙara shiga lamuran Building Your Future Ambassadors
SANARWA GA MANEMA LABARAI
BYFA Ta Kafa Kwamitin Tuntuɓar Masu Ruwa-da-Tsaki Domin Shirya Taron Wayar da Kai Kan Haƙƙoƙin Ɗiya Mace da Tarbiyya
Ƙungiyar Building Your Future Ambassadors (BYFA) ta kafa Kwamitin Tuntuɓar Masu Ruwa-da-Tsaki (Stakeholders’ Engagement Committee) domin gudanar da shirye-shiryen babban taron wayar da kai na yini ɗaya mai taken:
“Haƙƙoƙin Ɗiya Mace, Tarbiyyantarwa da kuma Nauyin da ya Rataya ga Al’umma”
(Girl Child Rights, Moral Upbringing and Community Responsibility).
Kwamitin zai gudanar da tattaunawa da masu ruwa-da-tsaki daga ma’aikatu, hukumomi, masarautu, ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyin mata da masu zaman kansu domin samar da haɗin gwiwa mai ɗorewa wajen tabbatar da nasarar taron.
An tsara wannan taro ne ƙarƙashin shirin BYFA mai suna “Samar da Wurare Masu Tsaro ga Yara Mata da Mata Masu Rauni” (Safe Spaces for Girls and Vulnerable Women Initiative), wanda ke da manufar ƙarfafa kariya, tarbiyya da wayar da kai kan haƙƙoƙin yara mata da mata masu rauni a cikin al’umma.
Kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin makonni biyu, daga yau Laraba, 13 ga Mayu zuwa Laraba, 27 ga Mayu, 2026, in Allah Ya yarda.
Ana sa ran gudanar da ƙayataccen taron a Birnin Katsina ranar Lahadi, 7 ga Yuni, 2026, in Allah Ya yarda tare da halartar iyaye mata, yara mata, ƙungiyoyin mata, malamai, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa-da-tsaki.
Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda, CON, ne zai jagoranci taron, yayin da kwamishinoni, shugabannin hukumomi, shugabannin siyasa da sauran manyan baƙi za su halarta domin nuna goyon baya ga wannan muhimmiyar manufa ta cigaban al’umma, a ƙarƙashin Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka - Building Your Future Strategic Policy (BYFSP) wanda shi ne ruhin Gwamnatin Jihar Katsina.
Kwamitin ya ƙunshi membobin BYFA kamar haka:
1. Isah Rabe Kambarawa (Darakta Janar) - Shugaba
2. Sadiq Abdullahi (Daraktan Mulki) - Memba
3. Binta Isah (Daraktar Lamuran Mata) - Memba
4. Sama’ila Shu’aibu Marke (Daraktan Matasa) - Memba
5. Bello Aliyu Muri (Daraktan Bincike) - Memba
6. Barrister Fatima Tukur (Daraktar Harkokin Shari’a) - Memba
7. Shafi’u Ibrahim (Daraktan Shirye-shirye da Ayyuka) - Memba
8. Zinatu Babangida (Daraktar Haɗin Gwiwa) - Memba
9. Mubarak Saleh Bakiyawa (Ko’odinetan Shiyyar Katsina) - Memba
10. Muttaqa Garba Ɗangamau (Ko’odinetan Shiyyar Daura) - Memba
11. Yusha’u Zakariya Salisu (Ko’odinetan Shiyyar Funtua) - Memba
12. Hussaina Uzairu (Shugabar Mata ta Shiyyar Katsina) - Memba
13. Yahanatu Mustapha (Shugabar Mata ta Shiyyar Daura) - Memba
14. Hadiza Salisu (Shugabar Mata ta Shiyyar Funtua) - Memba
15. Abdullahi Magaji (Ko’odinetan Ƙaramar Hukumar Katsina) - Memba
16. Abdulhadi Rabi’u (Ko’odinetan Ƙaramar Hukumar Ingawa) - Memba
17. Aminu Sani Mu’azu (Sakataren Mulki) - Memba
BYFA ta bayyana cewa wannan taro wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙungiyar wajen haɗa manufofin gwamnati da muradun al’umma musamman a ɓangaren kare haƙƙin yara mata, inganta tarbiyya, da gina al’umma mai kyawawan ɗabi’u.
Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors (BYFA)
Laraba, 13 ga Mayu, 2026
25 ga Dhul-Qa’adah, 1447AH
Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Ibrahima Kaulaha Mohammed
Katsina State Government
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State
11/05/2026
10/05/2026
07/05/2026
05/05/2026
23/04/2026
15/04/2026
14/04/2026