13/01/2022
Al'umma fa suna girmama Malamai ne saboda rigar dake wuyarsu ta Addini
Yaudarar kai ne Malami ya sauya rigar wuyarsa da ta campaign, tumasanci da maula ga ƴan siyasa sannan ya zaci zai cigaba da morar wancan ƙimar da mutunci ta malanta
10/01/2022
Munataya yan'uwa dalibai murnar saukewa da haddace Alqur'ani maigirma amakarantar madarasatu hizburrahim talamizatu shehi ibrahim inyas kahutu kar kashin jagorancin malam Gali Aliyu kahutu da malamin abin alfaharinmu afannonin ilimi Alhafiz malam sulaiman ladan kahutu
01/01/2022
Idan ba a babin mu'ujiza ko karama ba, rashin ladabi ga Sunnar Allah ne bawa ya dogara ga Addu'a ita kadai domin tabbatar abubuwan da Allah Ya baiwa bawa iko cikin aiwatarwa..
Dole ne mu haɗa Addu'a da Aiki
30/12/2021
Domin kawo ƙarshen ta'addanci;
Ba dole ne sai kowa ya ɗauki makami domin kare unguwarsu ba, amma dole ne kowa ya bada gudummuwarsa cikin wannan Jihadi na kare kai
Idan ba ka bayar da dubu goma cikin daɗin rai domin taimakawa a kare unguwarku ba, zai yuyu ka bada miliyan goma cikin tashin hankali domin taimakawa masu cigaba da kashe al'ummarmu
29/10/2020
محمد رسول الله صلى الله عليه وسلم