Sunnatur RASUL

Sunnatur RASUL

Share

Musulunci addinin Allah

05/05/2018

KAI BA KOMAI BANE DAN UWA

kai ba kowa bane dan uwa illa bawan Allah kada ka dinga ganin kanka kmar kafi wani saboda Allah ya ma wani nasibi na dukiya ko ilimi ko wata sarauta ka dauki kanka wani Abu

Kullum ka dinga tuna kai fa daga kasa aka yika kuma kai mutum ne bawan Allah kamar kowa

Malam mujahid yana cewa:- duk Wanda yake kallon kansa wata tsiya wato shi wani abune to ya tauye addininsa (ya kaskantarda kansa wajen Allah) , Wanda kuma ya kaskantar da kasansa ya dauki kansa ba komai ba to ya daukaka addininsa ( Allah xai daukakashi )

قال مجاهد : من أعزّ نفسه أذل دينه ، ومن أذلّ نفسه أعزّ دينه .

- جواهر من أقوال السلف

Ka sani cewa girman kai sifface ta ubanjiki idan ka shiga cikinta to tabbas xaka halaka halaka bayyananna

Wallahi bayin Allah muji tsoron Allah

22/02/2018

SHA'AWA (1)

قال بعض السلف : خلق الله الملائكة عقولاً بلا ش**ة ، وخلق البهائم ش**ة بلا عقول، وخلق ابن آدم وركب فيه العقل والش**ة ، فمن غلب عقله شهوته التحق بالملائكة ، ومن غلبت شهوته عقله التحق بالبهائم .

Magabata suna cewa;- an halicci mala,iku da hankali amma ba sha,awa

- an halicci dabbobi da sha,awa ba hankali
-an halicci Dan Adam aka bashi hankali da sha,awa

Wanda hankalinsa ya rinjayi sha,awarsa to xai xaiyi aiki irin na mala,iku Wanda kuma sha,awarsa ta rinjayi hankalinsa to xai dinga aiki kamar dabba

Allah yasa mu dace

15/08/2017

*KUYI AURE SAMARI DA YAN MATA*

DARASI NA DAYA 1

Wan nan magana ta fitone daga bakin manzon Allah yake cewa

يا معشر الشباب من استطاع منکم الباءة فليتزوج فإنه أغض للبصر وأحسن للفرج، ومن لم يستطمطع فعليه بالصوم فانه له وجاء

*Yana cewa* yaku taron matasa maza da mata Wanda ya samu damar aure to yayi aure domin shi xaisa kakame daga kallace kallacen banza da rudin shedan akan zinace zinace

San nan kuma shi yafi kyau ga farji (al'aura ) domin shine yafi tsafta da nishadi

Idan kuma baka samu damar aure ba to manzon Allah yana shawartarka da azumi domin axumi akwai kamewa a cikinsa

Matasa ya kamata mu bawa aure muhimmanci a rayuwarmu domin shine xai maida mu cikakkan mutane xai kara mana tunani ,kwarjini ,kamala da sauransu

San nan idan xamuyi auren muyi Dan Allah bawai dan sha'awa ba domin yanzu a rayuwarmu babu abinda muke dubawa sai kyau ko kudi

Mu auri masu addini shine isharar ma"aiki (saw)

Allah yasa mu dace,muna rokon Allah ya aurar da samarinmu da YAN matanmu baki daya ga Wanda s**a dace da xabin fiyayyen halitta ameen

Mu hade a darasi na biyu

*Ameenu BB*

07067671557

DAGA ZAUREN *WaSa KwALwA A mUsLinci*

Domin Shiga

07067671557

Ku tayamu yada sakon manzon Allah ta hanyar *share*

30/06/2017

. INSTAGRAM

Nasan a yanzun da wahalar gaske ka fadi wannan sunan a samu wanda bai sani ba.


Samari da 'yan mata hakazalika matan aure, zan taba 'yan matan saidai yau magana ta yawancinta kan matan aure suke.

Yan mata
Na bude Instagram ne dan inga menene a cikinshi da kowa yake tururuwar budewa.

Ta hanyar haka naci karo da handles da dama kaman su arewa finest, Arewa girls, Arewa swaggs, 9ja cuties dama wasu da ba zasu lissafu ba.

Hotunan da nagani akai yasa nake da tambayoyi guda uku ga yan matan mu da suke Instagram

1. Saboda me k**e Instagram yar uwa?

2. Hotunan da k**e sakawa Da sunan sexy ko hot pictures menene amfaninsu?

3. Wa k**e so ki burge?

Yar uwa ko kinsan wadan nan hotunan da k**e sakawa da kaya a matse surarki a bayyane me suke nufi?

Dan arewa finest su saka hotonki?
Ko kuwa dan ace kina da kyau?

Ina kikabaro al'adunmu da addininmu?
Ina kikabar darajarki ta 'ya mace?
Ina kikabar killace jikinki da akace kiyi?

Ko kin manta da mutuwa ne? Kin dauki hoto rabin kirjinki a waje? Haka zaki mutu wani ya dauki wannan hoto ya saka R.I.P a jiki.

Yayin da wani ya kalla yai miki addu'a wani kallo zai ki daga mishi hankali. Shin zaki so Mahaifiyarki ko Mahaifinki wani yaga irin wannan hotunan?

Zan tsaya anan saboda kaman yanda nace yau *Matan aure zanfi tabawa.

*Matan aure*
1. Me yakai hotonki *Instagram?*

2. Wa k**e so ki burge?

3. Ina kika ajiye igiyoyinki ukku na aure da suke kanki?

4. Ina kikai cilli da darajarki?

5. Ina kika adana iliminki?

6. Ina kikai watsi da koyarwar addininki?

7. Meye amfanin tarin followers dinki?

8. Me k**e so ki samu?

9. Yabon wa k**e bukata?

10. A ina aka halarta surar jikinki ta fita a ganta?

Inada tambayoyi akalla sunfi sama da hamsin. Ganin yanda hotunan matan aure ke yawo a Instagram yafi komai kona mun rai.

Ina da yaqinin 80% cikin 100% na kalar hotunan da matan masu aure suke sakawa a Instagram ko mazajensu ba kasafai suke ganin irin wannan kwalliyar ba.

Sai dai in za'aje unguwa, bance dan kina matar aure ba sai kiqi yin Instagram. Bandai ga amfanin saka hotonki akai bane ba kawai.

Wallahi muji tsoron Allah. Daga irin hotunan nan barna take kara yaduwa. Daga irin hotunan nan k**e taimakawa wajen yada barna.

Kinje kinsa hoto da surarki a bayyane. Abokin mijinki ya kalla wani abu ya darsu a ranshi. Bama shi kadai ba da maza da yawa.

Wani zaki masa kyau yai snapping ya ajiye. Daga nan kuma Allah kadai yasan inda zai yadu.

Bansan me k**e ji ba, ko dadin me hakan yake miki, wasu mijinsu yasani bai damu ba saboda rashin kishi ko kuma yana dauka hakan wayewa ce oho?

Karin lalacewa shine mata da mijin da suke daukar hotunan su rungume da juna wasu ma an hada baki da juna a saka a Instagram.

Allah kai mana tsari da irin wannan wayewa, me kuke so ku nunawa duniya?

Cewar ku masoya ne ko kuma me? Shin kun manta da Hadisai da dama da s**a zo kan muhimmancin boye sirrin aure?

Nikam kalamaina sun kare wallahi. Na fadi iya abinda nake son fada a yanzun.

Allah ya bamu ikon gyarawa ya rabamu da kalar wayewar da zata kaimu ga halaka.

Amin Ya Rabb.

Masu free wedding yake ko pre wedding banma sani ba. Ina nan zuwa gareku

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

21/05/2017

MADUBIN DUBAWA
**************************
Turawan Yamma sun chanza tunanin
Al'ummah. Sun dauki mace
amatsayin Wata "Na'ura" wacce aka
halicceta kawai domin Jima'i! (S*X
DEVICE).
Su kuma matan sun yarda da hakan,
Kuma wannan tunanin yayi tasiri
sosai azukatansu. Shi yasa kowanne
lokaci Mafi yawan Qokarinsu ko
yunkurinsu duk akan Harkar Jima'in
ne. ko dai don suja hankalin namiji,
ko kuma don Namiji yaji da'din
saduwa dasu, Ko kuma yadda zasu
asirce Namiji su mallake zuciyarsa.
Idan sun hadu da junansu sun
kebance agidajen Biki ko wuraren
ayyuka, Ko gidajen gaisuwa, duk dai
zancen kenan. Daga gulma sai
wannan.
A kafafen sadarwa kuwa, wasu har
groups suke Qirkira ko shafuka a
facebook ko Whatsapp don koyar da
jima'i ko sayar da Maganin Mata
domin jima'i!
Har da wasu Qarti samari wadanda
ko auren fari basuyi ba, wai su zasu
koya ma matan aure yadda ake
jima'i!. Su kuma Matan suna kwashe
sirrin Mazajensu suna gaya ma
Qartin (SUBHANALLAH).
Wannan shi ake kira "WANKIN
KWAKWALWA". Domin kuwa a
addinin Musulunci Mata su aka fi
sani da kunya, tausayi, Ladabi, da
kuma biyayyar Allah da biyayyar
Mazajensu.
Amma ayanzu an wanke musu
wancan Kyakkyawan tunanin neman
yardar Allah da yardar Mazajensu.
An chusa musu tsananin son shagala
da burgewa da neman biyar bukatar
sha'awa ta kowanne hali.
Acikin Matayen Farko an samu irin
su Nana Khadijah, Nana Fatimah,
Nana A'ishah, Nana Hafsah, Nana
Juwairiyyah, Nana Ummu Salamah,
Ummu Waraqah, Ummu Kulsum,
Ummu Sulaym, Ummu Hiram da
sauransu (Allah shi yarda dasu).
Daga bayansu an samu Manyan
Waliyyai acikin Mata irin su Sayyidah
Nafeesah, Fatimah Bintul Husayn,
Rabi'atul Adawiyyah, Zubaidah, da
sauransu.
Maimakon Matan zamanin nan su
nemi sanin tarihin wadannan domin
suyi koyi dasu, A'a kullum sunfi son
karanta Labaran Batsa, Maganin
Mallakar Miji, ko kuma Gulmace-
Gulmace..
Sun dena kokarin gyaran zukatansu
sai dai gyaran Jiki. Basu damu da
neman yardar Allah da Manzonsa
(saww) ba, Sai dai neman yardar
Mazaje... Ko ba Mazajen aurensu ba.
Idan kaga Matar aure ta cha'ba ado
ta fesa turare mai Qarfi, ta sanya
Atampa mai tsada to gidan Biki zata
je. Ko kuma wurin aiki, Ko Jami'ah
(University).
Su turawan da kuke koyi dasu, yanzu
acikinsu 'Ya'yan Zina sunfi 'Ya'yan
aure yawa.. Matan auren dake harkar
Kwartanci da wasu Mazajen sunfi
yawa fiye da wadanda basu yi.. A
kasashen Turai.. To menene abin
sha'awa acikin irin wannan rayuwar?.
Wannan kira ne daga Zauren Fiqhu,
domin mu gyara mu gudu tare mu
tsira tare..
*GYARA KAYANKA BAI ZAMA SAUKE
MU RABA BA...*
ALLAH KA SHIRYAR DAMU .

28/04/2017

HANYOYIN SAMUN ILIMI

FASALI NA BIYU

DARASI NA BAKWAI

*LADDUBAN DALIBI GA MALAMINSA*

Ya kai dalibi cin ribarka yana ga malamin ka

1- Kiyaye mutuncin Malaminka.

2- Girmama Malaminka.

3- Tausayawa Malaminka.

4- Ka zauna tare da Malaminka.

5- Ka kyautata sauraro da tambaya ga Malaminka.

6- Kayi hira da Malaminka don kyautatawa.

7- Kyawun ladabi wajen bude littafi a gaban Malaminka.

8- Karka gabace shi wajan yin magana (shisshigi) ko wajan tafiya.

9- Karka yawaita magana a gaban Malaminka.

10- Karka nace sai ya baka wata amsa.

11- Karka kirashi da sunnan shi kaitsaye.

12- Karka kira shi da "Kai!"

13- Karka kira shi daga nesa.

14- Yin koyi da kyawawan aiyyukansa da manyan dabi'unsa.

15- Kyautata masa (Yi masa kyauta).

16- Yi masa addu'a ta alkhairi.

17- Karka mike kafafuwanka a gaba gareshi.

LADDUBAN ZAMA DA ABOKIN KARATU

Sai a darasi nagaba in shaa ALLAHU.

Rubutawa: Dan Uwanku: Abdullah A Abdullah Assalafeey

ku tayamu yadawa ta hanyar shire (fatanmu mu gudu tare mu tsira tare)

28/04/2017

KYAKKYAWAN ZABI

Kyakkyawan Zabi Tsakanin Namiji da Mace,

Fitowa Ta 1 Daya

_Allahu Subhanahu Wa Ta'alah ya halicci Jinsin Maza da Mata yasanyasu abokan rayuwa a tare,Yasanya Masu sha'awar juna da buratar kasancewa tare amatsayin miji da mata sannan yasanya Aljannar matar aqarqashin dugadugai Na mijin nata wato Idan ta kiyaye haqqoqinsa da haqqoqin Allah Na zamantakewar Ibadah ta aure zata samu aljannah,Dan haka ya zama wajibi ga Namiji yasan wa yakamata yazaba wacce zata zamo masa uwar yaya abokiyar rayuwa da Neman lada Har zuwa aljannah,haka ita mace yazama wajibi tasan wa yakamata ta zaba abokin rayuwa Wanda zaisota tsakani da Allah kuma Wanda Zai nusar da ita zuwa ga ayyukan alkairi Har s**aita zuwa aljannah

Zamu kebantu ga bangaren mata kawai kasancewar mata sune iyayen al'umma Su makarantace wadda ke karantar da duniya,Mata wani yanki ne daga cikin yankuna Na rayuwa wadanda duk al'ummar da ta ciresu wannan al'ummar zata samu naqasu,Mata sune jigo Na jindadin rayuwar mazaje Wanda samun mace tagari shine Babban alkairi ga namiji rashinta kuma babbar hasarace,dan haka yazama wajibi kafin kiyi zabi to ki zabawa kanki hanya tagari wacce zata mayar dake tagari domin zaba da samun miji nagari tahanyar Sanin wacece mace tagari

Mace tagari Mace tagari Kamar yadda Hadisin Annabi Saw ya fassarata acikin Hadisin Aba Hurairah Wanda imamu Nisa'i ya ruwaito Albani Ya ingantashi ita CE Macen da Idan ka Kalleta zata faranta maka rai,Idan ka umarceta zatayi maka da'a(Da'a cikin abinda baisabawa Allah da Manzonshi ba),Idan bakanan zata kiyaye maka kanta da dukiyarka

Allah yas mudace.

Dan'uwanku: Hassan Abu Ammar Ydm

Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Katsina