Tsangayar Alaranma Mahuta: Darasi Na (16)
Sharhi Akan Manufofin Dr Radda ( 6)
3. Quduri Na (3) :Social Care:
Abinda ake nufi da 'social care', shine wani tallafi na kai tsaye da gwamnati za ta ba da ga yara kanana, matasa da kuma dattawa ma su wata bukata ta musamman ko ma su rauni. A wannan bangaren, gwamnati Dr. Radda ta ce za ta:
1. Ware kashi 5% na kasafin kudi na kowace shekara domin gudanar da ayyukan da ke karkashin wannan shiri.
2. Gina cibiyoyin kula da mutane ma su bukata ta musamman a guda sha biyar (15) zuwa shekarar 2025
3. Gina irin wadannan cibiyoyi a kowace karamar hukuma (kila zuwa karshen 2027)
4. Gina gidaje dari biyar (500) a kowace shekara a karkashin wannan shirin
5. Hada hannu da bankuna da kuma hukumomin ba da lamuni domin saukakawa talakawa mallakar wadannan gidaje
6. Tabbatar da cewa dokar 'Universal Social Care Act' , watau doka ta duniya da ta yi tanaje tanaje na musamman domin yan kasa ma su bukatu na musamman, ta zama doka a jihar Katsina.
7. Kirkiro da wani department na gwamnati na musamman domin Kula da wannan shiri.
8. Hada hannu da kungiyoyin NGO, CSO, na addini da masu zaman kan su domin aiwatar da ayyukan rage radadin talauci a tsakanin al'umma.
9. Samar da wadatacce kuma ingantaccen abinci musamman ga yara yan kasa da shekara biyu, ta hanyar habbaka ayyukan noma
10. Hada hannu da kungiyoyi ma su zaman kan su domin inganta ilimin yara kanana.
11. Kaddamar da shirin sa-kai domin koya ma matasa dogaro da kai da kuma ba su kwarin guiwa wajen gudanar da ayyukan kin kai da taimakon al'umma.
Shawara:
1. Da alama Dan takara na chudanya ayyukan 'Social services' da 'Social Care'. While social services ya kunshi dukkan wasu aikace aikace da gwamnati za ta gudanar domin al'umma baki daya, shi 'Social Care' ya na nufin ayyuka na musamman wanda gwamnati za ta gudanar da su domin ba da tallafi Kai tsaye ga masu rauni a cikin al'umma.
2. A maimakon a kirkiro sabon department, mai zai sa ba za a inganta social welfare department da mu ke da shi ba domin Kula da wadannan ayyuka na musamman,
3. Gina gidaje 500 duk shekara anya kuwa ba su yi yawa ba???
Tsangayar Alaramma Mahuta
Educating the people on current affairs and other social issues
Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Katsina