14/04/2026
Innalilahi wa innahi Raji un
Muna mika ta aziyyarmu Ga iyayan Rukayya Umar Yusuf
Da ma mukanmu GSSS KOFAR KAURA
Allah ta ala yagafarta mata yasa tahuta yasa chan tafiye mata nan zuriyyar da tabari ya albarkaceta 🙏🙏🙏
Team program Bakon Mako tana mika ta aziyyarta wa All members with School authority 😥😥😥😥😥
11/04/2026
We celebrated our Former Head of student and we prayer for him
Congratulations on your graduation! I wish you nothing but the best in your future endeavors.💪💪
Allah yakawo babban rabo
Muhammad M Sanee
10/04/2026
Boom💥💥💥💥💥💥
To masu sauraranmu brk mu da safiya dafatan Antashi lfy🙌
kada mu shafa ah ayau muna tafe da Hira ta musamman da
Daya daga cikinmu wato
Our Guest of the week
@Muhd kkr
Muhammad Sani Kankara
The former Headboy in Gsss kofar kaura 2020
Active Chairman in 2020 Organization Gsss kofar kaura,
Akaro na Biyu 2
Kada kasake ko kisake abaka lbr
TAMBIHI🥳🥳
✦ Chiarman dagaske ne a Organization 2020 candidate team
Sai wanda kukaso zaku jawoshi a tafiyar koko ya abin yake???
✦Zuwa yanzu ita wannan kungiya dakuka kafa wana irin tasiri ko rawa take takawa!???
✦Kataba latamar kasancewarka shugaba a Gsss kofar kaura!???
✦ Yaya kake kallon 2020 Organization team nan gaba???
✦ In da zaka samu damar zama governor katsina mai zaka fara yaki da shi a jahar
✦ Shin dagaske ne kataba yiwa soyyya kuka!???
Dama sauran tambayoyin da zasu biyo baya kukasance damu Atattaunawar mu ta yau
kukasance da na ku Akoda yaushe wato
03/04/2026
Assalamu alaikum waramatullahi ta ala wabarakatuh🙏
⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Al'ummar wannan gida mai albarka phatan kunyi sallah lafiya.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡
k**ar yadda muka saba kawo maku wannan Shirin namu mai dogon zango mai suna *Bakon mako*
Wannan lokacin ma shirin Bakon mako zai zo maku k**ar yadda aka saba duk ranar Juma'a da misalin kare 08:30 na dare, acikin wannan gida namu Mai albarka .ayau munyi babban kamu daya daga cikin jiga-jigan wannan gida mai kishin wannan gida chief Editor namu presenter
Wato @Sunnah Boy👨 Sirdeeq :
*Dan Tsokaci:*
1. Wanene sadiq Lawal , minene tarihinsa ya ya rayuwar ta gudana a da dakuma yanzu?
2. Ina ya samu sunan sunnah boy da kuma Dan china
3. Miye dalilin da yasa Sadiq yake tsoron Mata.
4. Wacece sana'a Sadiq yake yi
Wannan dama wasu tambayoyin zakuji acikin shirin namu na yau ku kasance tare da ni
*Nazifi salisu (Ana)*
Domin jin yadda firar zata kasance
👋🏻👋🏻👋🏻
24/03/2026
Breaking update🔥🔥🔥🔥
Alhmdllh
Alhmdllh
Alhmdllh
Gsss kofar kaura 2020 Organisation
tanayiwa daukakin wannan gida barka da sallah da fatan Anyi Shagulgulan sallah lfy Allah ya karba mana yasa munyi karbabiya
baya da haka muna Masu farincikin sanar daku cewa
munan zamu fara shirye shirye na yadda zamu yi taron babbar sallah wanda mukayi a waccan shekarar in sha Allah
munan munata tattunawa da kuma tsara yadda wannan babban taro zai gudana
Zamu dawo shirin bakon mako by Next week in sha Allah muna nan munfara daukar wanda ko wacce hirarta tabada tausayi ko al ajabi ko darasi ko nishadi
domin muyi A warding dinsu aranar taro k**ar yadda mukai last year dafatan in aka sake gayyato zaka ko zaki bamu labari mai ma ana dake
Tsokaci
Ga wanda ko wacce take ganin ko yake ganin yanaso yabada tasa gudummawar Agamada wannan babban taro Kofa Abude take pls MD me in private
katuntubeni a chat dina domin jin yadda zata kaya Allah yabamu ikon wannan taro fiyeda na waccan shekarar
ngd naku akullum
Ameenu Sunusi Ak
19/03/2026
Alhmdllh Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda yanuna mana karshan wannan program da wannan azumi lafiya k**ar yadda muka fara lfy haka muka kammala lfy
Alhmdllh godiya ta musamman ga team dinmh das**a jajirce wurin ganin sungabatar da shirin duk ranar dasuke presenting muna godiya🙏🙏
godiya gareku members na wannan gida dakuke sauraranmu kuna bamu sport
fata Abinda muka fada daidai Allah yabamu lada kuskuranciki ya yafe mana
JANKUNNE👂👂👂
daga cikin tunatarwar damukai a shirin Azumi Amanar Allah All
munasan kowa yarika k**antawa yana aiki dasu badole sai a azumiba🤗🤗
Kada kiga ko kaga azumi yawuce kace ko kice ai shikenan aa Allah ta ala yace
suratu Duha 51:55
وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَىٰ تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَ﴾
So kunga duba da wannan aya Allah yana cewa Atunstar domin ita tuntarwa tana temako wa mumini
Allah yabamu ikon bin iyakokinsa🙏🙏
Wanda s**a dena wani abu marakyau zuwan Axumi su daure suyi yaki da zukatansu kada su bari sucigaba
inayiwa kowa fatan Alkhairi
da Adduar wanda s**a rasu Allah kagafartamusu
marasa lfy mu kabasu lfy
mudamuke da lfy kakaramana ita da kwsnciyar hankali
wanban shine karshan wannan program na Azumi Amanar Allah saikuma in Allah yakara nuna mana wata shekaran hausawa nacewa
mai raban ganin badi ya gani😭😭
Ramadan Kareem
💫💫💫💫
18/03/2026
Jama Assalma Alekum
Gamu acikin shirin azumi Amanar Allah
Day 29
Topic
MUHIMMANCIN HAKURI DA JURIYA
HAKURI DA JURIYA YANA TASIRANTUWANE AWAJAN DANDA YAKE KOYI DA FIYYYAN HALITTA DAKUMA KOYARWAR MUSULINCI
ALLAH YAKIRA HAKURI HAKURI A AYOYI MA BANBANTA
HAKA YAKIRA JURIYA
SABODA HAKA YAKAMATA MUJAJIRCE TSAYINDAKA MUKOYESU DOMIN SUXAMAR MANA JIKI SAI ALLAH YATEMAKU
ALLAH YADATAR DAMU🙏🙏🙏
Ramadan kareem
💫💫
17/03/2026
Assalamu alaikum mun yini lpy y ibada dafatan mun Sha ruwa lpy barkanmu da sake kasancewa daku acikin wannan shiri Mai Albarka Mai suna AZUMI AMANAR ALLAH
*MAUDU’I HUKUNCIN MASU AZUMI, MASU UZURI, DA MASU CIYARWA (FIDYA)*
*Azumin watan Ramadan farilla ne akan duk wani Musulmi baligi, mai hankali, mai lafiya, wanda ba ya cikin tafiya (mazaunin gida). Allah Maɗaukaki Yana cewa “…Wanda ya ga wata a cikinku, to ya azumce shi…” (Suratul Baqarah 185)*
*Ga rabe-raben mutane dangane da azumi gida uku (3)*
*RUKUNI NA (1) WAƊANDA AZUMI YA WAJABA A KANSU (BABU UZURI)*
*Wajibi ne su yi azumi, kuma idan s**a sha da gangan sun aikata babban zunubi. Su ne:*
*1. Musulmi Baligi mai hankali.*
*2. Mai lafiya (wanda ba shi da ciwon da zai cutar da shi).*
*3. Mazaunin Gida (Ba Matafiyi ba).*
*4. Mace mai tsarki (Wacce ba ta Haila ko Binin jini).*
*5. Yaro ƙarami ba wajibi ba ne a kansa, amma ana horar da shi domin ya saba.*
*Hujja Manzon Allah (S.A.W) ya ce “An ɗaga alƙalami (na rubuta zunubi) daga mutum uku daga mai barci har sai ya farka, da yaro har sai ya yi mafarki (balaga), da mahaukaci har sai ya yi hankali.” (Abu Dawud, 4403).*
*RUKUNI NA (2) WAƊANDA AKA YARDA SU SHA, AMMA DOLE SU RAMA (QADA)*
*Waɗannan suna iya shan azumi yanzu saboda uzuri, amma bayan Ramadan dole ne su rama kwanakin da s**a sha. Ba sa yin ciyarwa (Fidya), ramawa kawai suke yi.*
*1. Matafiyi (Musafiri) Wanda zai tafiya mai nisa.*
*Hujja “Duk wanda ya kasance majiyyaci ko yana kan tafiya, to (ya sha) ya biya adadin kwanakin a wasu ranakun na daban.” (Suratul Baqarah 185).*
*2. Marar lafiya (mai ciwon da ake sa ran warkewarsa) Ciwon da azumi zai ƙara masa tsanani ko ya jinkirta warkewa. Ko mai ciwon yau yana da lafiya, gobe bai da lafiya.*
*3. Mace mai Haila ko Nifasi Haramun ne ta yi azumi, kuma dole ne ta rama bayan ta yi tsarki.*
*Hujja Nana A’isha (R.A) ta ce “Hakan yana samun mu (Haila), sai a umarce mu da rama azumi, amma ba a umarce mu da rama Sallah ba.” (Sahih Muslim).*
*4. Mai ciki da mai shayarwa (idan suna tsoron cutarwa ga kansu ko jaririn) Malaman Fiqhu sun yi sabani, amma fatawar da ta fi rinjaye ita ce idan suna tsoron cutarwa ga kansu, za su sha su rama.*
*RUKUNI NA (3) WAƊANDA BA ZA SU YI AZUMI BA, KUMA BA ZA SU RAMA BA, SAI DAI CIYARWA (FIDYA)*
*Waɗannan su ne waɗanda ba su da ikon yin azumi har abada saboda tsufa ko ciwo mai tsanani. Allah Ya ce “…Ga waɗanda suke iya yin sa (da kyar da wahala matsananciya), akwai fansa (Fidya) ta ciyar da miskini…” (Suratul Baqarah 184)*
*Su ne:*
*1. Tsoho ko tsohuwa mai rauni Wanda tsufa ya sa ba zai iya azumi ba, kuma ba zai taɓa komawa ƙuruciya ba.*
*2. Mai ciwon da ba a sa ran warkewarsa (Chronic illness) Kamar mai ciwon siga (Diabetes) mai tsanani, ko ulcer da ta ci ƙarfinsa, wanda likita ya tabbatar cewa azumi zai cutar da shi sosai. Ba za su rama ba (saboda ba zai warke ba), sai dai ya ciyar.*
*Hujja Ibn Abbas (R.A) ya ce game da ayar nan (Baqarah 184) “Wannan ayar tana kan tsoho da tsohuwa waɗanda ba sa iya azumi, za su ciyar da miskini guda ɗaya a madadin kowace rana.” (Sahih Al-Bukhari, 4505).*
*MUHIMMIYAR SHAWARA DA JAN HANKALI GA MASU SAKAINAR KASHI*
*Yana da matuƙar muhimmanci mu fahimci cewa Fidya (ciyarwa) ba ta maye gurbin azumi ga duk wanda yake da damar ramawa. Muna ganin wasu ’yan uwa (musamman mata) suna yin gaggawar biyan kuɗin ciyarwa saboda ciki ko shayarwa, ko kuma wani namiji da ya yi rashin lafiya na ɗan lokaci, sai kawai ya ce zai yi ciyarwa. Wannan kuskure ne babba!*
*Ciyarwa (Fidya) tana kan wanda ba a sa ran zai warke har abada, ko tsohon da ba zai sake komawa ƙuruciya ba. Amma idan rashin lafiyar ta ɗan lokaci ce, ko ciki ne da shayarwa, wajibi ne a rama (Qada), koda kuwa sai bayan shekara ne. Biyan kuɗi ko ciyarwa ba ya ɗauke wannan nauyi matuƙar akwai lafiyar da za a iya ramawa a gaba.*
*Kada mu bi son zuciya mu ɗauki hanyar da ta fi sauƙi (ciyarwa), alhali Allah Ya ɗora mana ramawa. Azumi ibada ce ta jiki, ba ta kuɗi ba, sai ga wanda ya gaza gaba ɗaya.*
*Allah Ya ba mu ikon sauke nauyin da ke kanmu, Ya karɓi ibadunmu, Ya kuma sa mu kasance cikin bayinSa na gari.*
16/03/2026
Barkmu dashan ruwa sannun mu da sake kasancewa daku acikin wani saban shiri mai suna Axumi Amanar Allah
Topic
Abubuwa uku daya k**a ta musa su a rayuwarmu
1. Hakuri
Hakuri matakin nasarane nakowanane Al amari na rayuwa duk hakuri yana tare danasara da samu saboda haka mukasance masu hakuri
2.Jajircewa Duk wani abu na rayuwa saikasa jajircewa sannan abunyake yuyuwa saboda haka maza da mata muzamo masu juriya akan duk wani abu narayuwa komai zamuyi komai wahalarsa musa aranmu zamu iya shine bature ke cewa
Never Give up
shukuma masu fashin baki s**ace Gobe ta Allah ce
Saboda haka duk abinda xamuyi mujajirce muyi addua🫸🫸
3. Gaskiya dokin karfe inji bahaushe
Indai zakarike gaskiya arayuwa to karike matakin duk wata nasara Arayuwarka
duk abinda zaka kazama mai gaskiya haka Allah zai temakeka kaga komai xakai ana marhaba dakai👌👌
Allah ta Ala yadatar damu
fatan munsha ruwa lfy
Ramadan Kareem💫💫💫
15/03/2026
ASSALAMU ALAIKUM AL'UMMAR WANNAN GIDA MAI ALBARKA BARKANMU DA SHAN RUWA SANNUN MU DA SAKE KASAN CEWA DAKU ACIKIN SABON SHIRIN MU NA *AZUMI AMANAR ALLAH*
WANDA NI *NAZIFI SALISU (ANA)* ZAN GABATAR
*Daren Lailatul Qadr dare ne mai girman gaske wanda Allah Ya fi so a yawaita ibada da addu’a. Ga wasu muhimman addu’o’i da za a rika yi:*
1️⃣ Addu’ar Neman Karɓar Ayyuka
Wannan addu’a tana cikin Alƙur’ani (Suratul Baqarah 2:127). Annabi Ibrahim (AS) da ɗansa Isma’il (AS) sun karanta ta lokacin da suke gina Ka’aba.
رَبَّنَا تَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Rabbana taqabbal minna innaka Antas-Sami’ul-‘Alim.
Ma’ana:
Ya Ubangijinmu, ka karɓa daga gare mu. Lalle kai Mai ji ne, Masani.
Lokacin yin ta:
A rika karanta ta bayan an yi wani aikin alheri, sallah ko wata ibada domin roƙon Allah Ya karɓa.
2️⃣ Addu’ar Tsakanin Sujjada Biyu a Sallah
Wannan addu’a ce cikakkiya da ake karantawa yayin zama tsakanin sujjada ta farko da ta biyu a cikin sallah.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَاجْبُرْنِي، وَعَافِنِي، وَارْزُقْنِي، وَارْفَعْنِي
Allahummaghfir li, warhamni, wahdini, wajburni, wa ‘afini, warzuqni, warfa‘ni.
Ma’ana:
Ya Allah ka gafarta mini, ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka gyara halina, ka ba ni lafiya, ka azurta ni, kuma ka ɗaukaka matsayina.
3️⃣ Addu’ar Neman Gafara a Lailatul Qadr
اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي
Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa‘fu ‘anni.
Ma’ana:
Ya Allah, kai Mai gafara ne kuma kana son gafara, don haka ka gafarta mini.
4️⃣ Addu’ar Tsira daga Wutar Jahannama
رَبَّنَا أَعْتِقْ رِقَابَنَا مِنَ النَّارِ
Rabbana a‘tiq riqabana minan-naar.
Ma’ana:
Ya Ubangijinmu, ka ‘yantar da wuyoyinmu daga wutar Jahannama.
Ka yawaita waɗannan addu’o’i a daren Lailatul Qadr, domin dare ne da addu’a ke karɓuwa kuma rahamar Allah ke sauka.
Ramadan Mubarak 🌙
15/03/2026
Alhmdllh Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin sarki da yabamu ikon kai wannan azumi lfy Alhmdll
bayan haka zanyi amfani da wannan dama wajan taya jaje da murna wa dan uwanmu kuma abokinmu wato
Ismail Faruq Bello
Rannan nayi posting akan iftila ih da yafada na hannun masu garku da mutane Alhmadllh Anci nasara da adduo Allah yakubuto da shi yau
muna mika godiya da yan uwa da abokan Arziki wajan nuna alhini da tayamu jaje da addoi da s**arika yi mungode Allah yabar tare yaku tsare dukkan musulmi wassalama Alaikum
13/03/2026
Jama a Assalama Alaikum barka mu dasake kasamcewa daku acikin wani saban shiri mai suna Azumi Amanar Allah
wanda a yau Ni
Ameenu Sunusi Ak
zan gabatar da shirin
Day 24
Topic
ᴀʙᴜʙᴜᴡᴀ ᴜᴋᴜ sᴜɴᴀ ʜᴀɴᴢᴀʀᴛᴀ ᴛsᴜғᴀ ᴀʀᴀʏᴜᴡᴀʀ ᴅᴀɴ ᴀᴅᴀᴍ👂👂👂
1 FUSHI
2 HASSADA
YAWAN DAMUWA DA NI IMAR DA ALLAH YAIMA WANI KAI BAI MABA
IDan muka kalli duk wannan abubuwa
Allah tabaraka wata ala yai hani akansu duka
kuma fiyyan halitta wanda muke koyi dashi baya yinsu kuma yana fushi damaj yinsu
Wace hanya zamu magancesu!???
Babban maganinsu duka yafiya da fawwalawa Allah lamuranka
kayarda shine mai komai kuma shi zaiyi komai Asadda yaso🫸🫸
Allah tabaraka wata Allah yabamu ikon gayarawa
fatan munsha ruwa lfy
Allah yakarbi ibadinmu yabamu dacewa awannan wata yakawomana cigaba dazama lfy awannan kasa
Akwai dan uwanmu kuma Abokinmu wato
faruq bello da iftila ih yasamaishi yana hannun azzalimai masu garkuwa da mutane
ya Allah kaceceshi🙏🙏
Ya Allah ka kubuto dashi🤲
Ya Allah bazamu iya ba ka iya mana👏👏
Ya Allah kabashi kariya👏👏
Ya Allah muna tawasul da iyaka na abudu wa ika nastain👏👏
Ya Allah muna tawassul da ujibu da awatudda ih iza du ani 👏👏
Ya Allah muna tawassul da wannan wata 👏👏
Allah kanuna ikonka ka kubutk dasu da gaggawa👏👏
RAMADAN KAREEM💫💫