11/04/2023
An ruwaito daga Mu'az ɗan Jabal Allah ya ƙara yarda da shi, yace: Nakasance ina tafe tare da Annabi Muhammad صلى الله عليه وآله وسلم akan jaki yana goye dani, sai yace dani صلى الله عليه وآله وسلم: Ya kai Mu'az shin kasan haƙƙin Allah akan bayinsa?, da kuma haƙƙin bayi akan Allah?.
Mu'az É—an Jabal yace Allah da manzonsa ne s**a sani.
Manzon Allah صلى الله عليه وآله وسلم yace haƙƙin Allah akan bayi shi ne, su bauta masa batare da haɗashi da abokin tarayya ba, Haƙƙin bayi kuma akan Allah, shi ne bazai yiwa wanda baiyi shirka da shi azaba ba.
Mu'az É—an Jabal Allah ya kara yarda da shi yace, Ya Rasulullah, yanzu na yiwa mutane bushara da wannan magana?.
Annabi Muhammad صلى الله عليه وآله وسلم yace a'a kada kayi musu bushara sai su dogara da haka.
Wannan hadisi yana nan a cikin sahihai guda biyu (Bukhari da Muslim)
Barkanmu da shiga goman karshe, Allah ya karbi Ibadun mu ya gafarta mana.
Daga: Abdallah Amdaz