16/05/2026
Menene tsutsan ciki (Intestinal Worms)?
Tsutsan ciki ƙananan ƙwayoyin cuta ne da ke rayuwa a cikin hanji ko ciki na mutum, suna shan abincin da jiki ke bukata, wanda hakan ke haddasa rashin lafiya.
--Nau’o’in tsutsan ciki da aka fi samu 👇
1. Ascaris (Roundworm) – yakan sa ciki ya kumbura, amai, ciwon ciki.
2. Hookworm – yakan janyo ƙarancin jini (anaemia).
3. Tapeworm – yakan sa mutum rage kiba da ciwon ciki.
4. Pinworm (Threadworm) – yakan sa ƙaiƙayi a dubura, musamman da dare
🚨 TAYAYA AKE KAMUWA DA TSUTSAN CIKIN?
🔸Cin abinci ko shan ruwa mai ɗauke da ƙazanta
🔸Rashin wanke hannu bayan bayan gida
🔸Cin ’ya’yan itatuwa ko kayan lambu ba tare da wankewa ba.
🔸Tafiya ba takalmi a ƙasa mai ƙazanta
🔸Rashin tsafta a muhalli
🛡️ MATAKAN KARIYA DAGA TSUTSAN CIKI
✅1. Wanke hannu da sabulu kafin cin abinci da bayan bayan gida(toilet).
✅2. Wanke kayan marmari da ’ya’yan itatuwa sosai kafin ci.
✅3. Shan ruwa mai tsafta kawai.
✅4. Guje wa tafiya ba takalmi, musamman a ƙasa mai datti.
✅5. Kula da tsaftar muhalli (share gida, da bayan gida).
✅6. Yawan yankan farce, musamman ga yara.
✅7. Deworming: Shan maganin tsutsa (kamar albendazole/mebendazole) lokaci-lokaci musamman ga yara.
---
Muhimmin saƙon wayar-da-kai
> Tsutsan ciki ba al’amari ba ne na raini, amma rashin tsafta ne ke janyo su, Semun Hadu A Post Na Gaba Fatan Zakuyi SHERE 🙏
⚠️ KUTINA RIGA-KAFI YAFI MAGANI Sannan zaku iya follow na page ɗinmu 👉 IT'S MUJAHEDEY don samun bayanan kariya ko tambaya akan LAPIYARKU.MEDICAL LABORATORY
20/12/2021