21/12/2025
HIRAR MASUSSUKA DA DW 🤔
Duk wanda ya saurari hirar DW da s**a yi da Yahaya Masuss**a zai fahimci cewa wallahi da’awar sa ta zama kame-kame da wasa da hankalin jahilai. Domin kowa ya san cewa tun farko, lokacin da ya bayyana, akidar sa ita ce “Al-Qur’ani zalla, duk wani Hadisi ƙarya ne.” Wannan magana tasa ta shahara, kuma ita ce ginshiƙin kira da ya yi tsawon lokaci yana yadawa.
Sai dai a yau, saboda yadda Musulmi masu bin Musulunci na gaskiya suke ƙalubalantar sa da tambayoyi masu ƙarfi—musamman game da yadda yake yin wasu abubuwa na addini alhali ya ce bai yarda da Hadisi ba—aka fara tambayar sa kai tsaye:
Idan ba ka yarda da Hadisi ba, to daga ina ka samo waɗannan ayyuka da fahimtofi?
A nan ne aka ga raunin hujja, domin sai ya koma kame-kame da kwane-kwane, babu amsa madaidaiciya, babu hujja tabbatacciya, kuma duk mai hankali na iya gane haka.
Da ya fahimci cewa wannan matsayi nasa ba ya tsayawa da hujja, kuma ya ga ba sarki sai Allah, sai ya sassauta daga matsanancin ƙaryata Hadisai, ya koma wata dabara cewa wai ba kowane Hadisi yake ƙaryatawa ba. Ya ce duk wani Hadisi ko labari muddin ba ya cin karo da Al-Qur’ani, ko ba ya cin mutuncin Annabi ﷺ, ko ba ya koyar da ta’addanci, to shi yana yarda da shi.
Amma wallahi wannan magana ba sabuwa ba ce, kuma ba hujja ba ce. Domin ai wannan shi ne matsayar dukkan Ahlus-Sunna—ko Izala ko ’Yan Ɗariqa—tun ƙarni-ƙarni. Duk Hadisin da ya tabbata sahihinsa kuma ba ya cin karo da Al-Qur’ani, ba ya zagin Annabi ﷺ, kuma ba ya koyar da zalunci ko ta’addanci, ana karɓarsa. Don haka ikirarin Masuss**a ba wani sabon bincike ba ne, sai dai tsohuwar magana da aka saka mata sabon suna.
Babbar matsalar da yake nan ita ce:
Wa ke da ikon tantancewa ya ce wannan Hadisi ta’addanci ne, ko wannan cin mutuncin Annabi ne, ko wannan ya ci karo da Al-Qur’ani? Shin kowane mutum zai fassara addini yadda zuciyarsa ta so? Idan aka bar haka, to addini zai koma ruɗani da son rai.
Tsawon shekaru sama da dubu ɗaya, Al-Qur’ani da Hadisi suna tafiya tare. Manyan malamai masu tsoron Allah—na Izala, na ’Yan Ɗariqa, na Ahlus-Sunna gaba ɗaya—sun yi nazari mai zurfi kan Hadisan Bukhari da Muslim. Sun tantance, sun fassara, sun kare mutuncin Annabi ﷺ, kuma ba su ce akwai ta’addanci ko cin mutunci a cikinsu ba. Shin hankali zai yarda cewa dukkan waɗannan malamai sun yi kuskure, sai yanzu Masuss**a shi kaɗai ya gano gaskiya?
Bugu da ƙari, Al-Qur’ani da kansa ya umarci Musulmi da biyayya ga Annabi ﷺ, kuma wannan biyayya ba za ta yiwu ba face ta hanyar abin da ya faɗa, ya aikata, kuma ya yarda da shi—wato Hadisi. Wanda ya ce zai bi Al-Qur’ani amma ya ƙi Hadisi, to a zahiri ya karya umarnin Al-Qur’ani da kansa, domin Qur’ani ya ɗaure biyayya ga Manzon Allah ﷺ.
Saboda haka, duk mai hankali da Allah Ya buɗe masa zuciya da shiriya ya san cewa wannan tafarki ba zai kai ga gaskiya ba. Sai dai mai bin son rai ko wanda aka ruɗe ne zai tsaya yana bin irin wannan kira.
Ya Allah, Ka shiryar da bayinka zuwa ga shiriya, Ka kare su daga ruɗin shaiɗaniyyu, Ka kuma tsare Musulunci daga masu ɓata masa suna. 🤲