06/09/2024
Vaginal Discharge shine duk wani ruwa da yake fita a al'aurar mace.
Yanayin launin sa da qamshi ko warinsa nada alaqa da lafiya ko rashin lafiyar mace musamman larurar data shafi reproductive organs and health.
Duk da dama a yanayin halitta da lafiyar jiki bai kamata ace discharge yana qamshi ba, amma wasu lokutan irin kalar abinchin ko abun sha da mace ke amfani dashi kan shafi qamshinsa da kuma yawan sa lokacin da yake fita daga jiki.
Launin discharge kan iya nuna yanayin kusanci ko nisan kwanakin jinin Al'ada da kuma yanayin da mace zata iya saurin daukar ciki.
RABE-RABEN KALOLIN VAGINAL DISCHARGE
-Fari fat
Wannan kalar tana nuna lafiya qalau mace take,kuma organs dinta lafiya suke. Akan samu banbancin yanayin kaurinsa saboda yanayin halitta da kuma abinchin da abun sha da mace take amfani dashi. Akan iya samun sa da qamshi na daban amma ba wari ba tunda dama bai kamata wurin yayi qamshi ba.
Idan kuma yana zuwa a dunqule ko kuma kamar diddiga sannnan yana wari kuma akwai qaiqayi,hakan na nuna akwai Yeast infection (Candida Albicans) da sauran su
-Kalar ruwan qwai
Shima wannan yana nuna lafiya qalau mace take, kuma akan same shi da yauqi.
Yakan zo bayan wasu kwanaki da gama jinin Al'ada wanda yana nuna akwai sabon qwai a mahaifa. A wannan lokacin Idan ba ikon Allah ba,indai babu matsala kuma mu'amalar aure ta shiga to ciki zai iya samuwa. Shima baya wari.
-Kalar hoda
Wannan kalar akan same ta a farkon kwanakin da mace ta fara jinin Al'ada kafin jini ya fara zuwa.
Wasu kuma sukan same shi jini yadan sirka shi (spot bleeding) a lokacin da qwan da aka qyanqyashe ya samu wuri a mahaifa ya dasa kansa (Implantation bleeding) ko kuma lokacin akayi mu'amalar aure (Rough) da zai iya sakawa wata jijiyar ta tabu jini yadan zuba.
-Kalar ruwan qasa mai duhu ko mara duhu
Galibi anfi samun wannan a qarshen kwanakin jinin Al'ada lokacin da jini bai gama daukewa gaba daya ba.
-Kalar Kore ko kuma ruwan rawaya (Green/Yellow).
Akan samu wannan kaloli Idan akwai mats