13/08/2025
Assalamu alaikum,
A ranar Lahadin data gabata 10/08/2025, uwar ƙungiyar tsofaffin ɗaliban GAC Gwale mai suna GATCOSA NATIONAL BODY bisa jagorancin *Prof Kabiru Dandago* ta gudanar da taro inda ta gayyaci kowacce CHAPTER don tattauna muhimman batutuwa. Ga kaɗan daga cikin batutuwan👇🏻
1. ZAMA ƊAN ƘUNGIYA: duk wanda ya gama wannan makaranta ta GAC Gwale ɗan wannan ƙungiya ne. Amma zama cikakken ɗan ƙungiya sai kayi rigista da uwar ƙungiya inda za'a baka Katin Shaida (Membership Card) wanda da shine zaka shiga dukkan wani tsare-tsare na ƙungiyar, ciki harda zaben shugaba ko tsayawa a matsayin wanda za'a zaɓa a wani matsayi idan lokacin hakan yayi.
2. Kundin tsarin mulkin ƙungiya ya samar da wasu kwamiti don gudanar da al'amuran ƙungiya:
* Congress Committee: shi wannan kwamiti ne daya hada dukkan wakilan Chapters don tattaunawa da zartar da muhimman al'amuran da s**a shafi ƙungiya.
* Standing committee: shi wannan kwamiti ne da zai dunga duba muhimman al'amura da tattaunawa akan su idan wasu abubuwa sun taso.
3. Samarwa ƙungiya ƙudin shiga: Ƙungiya zata dunga samun kuɗin shiga ne ta wannan hanya:
* Rigista da ƙungiya
* Biyan annual due
* Samar da Calendar mai hotunan shugabannin ƙungiya wacce ake sa ran ƴan kungiyar su siya.
Bayan haka, an tattauna akan kuɗin da za'ai rigista inda aka koma cikin kundin tsarin mulki inda yace a 1984, duk wanda zai zama halattacen member zai biya ₦2, a lokacin kuma Dalar Amirka dai-dai take da Kobo 80 na kuɗin Najeriya. Shine aka yanke cewar za'a biya dubu uku a yanzu.
4. Batun zabar shugabanni da kuma waya kamata ya tsaya a matsayin wanda za'a zaɓa da kuma masu zaben: wajibi ne ga duk wanda yake son tsayawa a matsayin wanda za'a zaɓa ko kuma yin zaɓe saiya kasance yana da katin shaida na ƙungiya.
BATUTUWA HUDU DA AKA CIMMA A TARON
1. Duk mai son zama halattacen ɗan ƙungiya zai karɓi kati kuma zai dunga biyan annual due
2. Gyaran kundin dokokin ƙungiya ( Constitutional Amendment)
3. Rubuta rohotan yanayin da makaranta ke ciki don miƙa shi zuwa ga gwamnati don samun gyara
4. Buga kundin tsarin mulki, sannan ko wacce chapter zata mallaki nata copy don samarwa ƴaƴanta.
*Duk shekara za'a dunga biyan ₦5,000*
Abba Ali Hassan
Chairman ADOBA2005
13/08/2025
20/06/2018