KK INFRA

KK INFRA

Share

KK Infra is a leading educational consultancy in Nigeria. We secure your admission and effective medical tourism in India.

We treat our customers as kings and queens throughout their educational and medical journeys.

Kano State Resumes Scholarship for postgraduate studies – KK INFRA NIG LTD 10/07/2023

Scholarship for first class students

Kano State Resumes Scholarship for postgraduate studies – KK INFRA NIG LTD Posted on June 18, 2023 / 0 / buhafran Resumption of Postgraduate Scholarship for Kano State Indigenes with First Class Honours Degree. Invitations are open for applications from highly qualified graduates for the Kano State Postgraduate Foreign and Local Scholarships for the 2023/2024 Academic Sess...

23/02/2023

Babu wani rikakken dan PDP a kudu da ya wuce Edwin Clark, Wike da Fayose a kudan cin Najeriya. Duka yakar Atiku za suyi. Bawai "yan-ba-ruwana-bane.
Tabbata Kudu ba za su zabi Atiku ba. Lokaci yayi da yakamata shi da magoya bayansa su janyewa Kwankwaso.

18/10/2022
01/10/2022

Admissions are still ongoing. Contact us +91 87002 40912

Enjoy a 50% scholarship.

21/09/2022

A shekarar 2013 lokacin da gwamnatin Jihar Kano ke fitar da dalibai kasar waje karatu, manyan ka’idoji biyu da aka shimfida, sune, sai me shakaru kasa da 30 sai kuma wanda makin CGPA dinsa yakai 3.00 a cikin ma’unin 5.00. A lokacin saura wata 1 rak in cika shekaru 30 sannan da CGPA 3.01 na gama BUK. Ka iya cewa na tsallake rijiya da baya kuma a rufe-ido.

Da visa ta fito aka bawa kowa, banda ni. Da na tuntubi me kula da lamarin, Director quality assurance, na maaikatar ministry for higher education. Babu wani gamsashen bayani, sai dai jeka-ka-dawo. Bayan an gana da kwamishinan ma’aikatar na wancan lokacin wato, Umar Haruna Doguwa da director Quality assurance da kuma Lawan Hussaini (danmajalisar jiha maiwakiltar karamar hukumar Dala a yanzu) sannan PA na ministry din a lokacin. Sai su kace ai nayi Magana da agent din da yasamo mana makarantar maimakon in biyo ta ma’aikatar. Dalilin haka, an soke sunana. Ana kokarin canza sunana da na wata yarinya.

Wacce irin Magana mukayi da agent ba’indiye?

Na cewa agent (Mr. Pasad) na fara masters a BUK har na kammala course work dina na shekara 1 kuma result dina yayi kyau, shin zaiyiyu a maimakon masters inyi Ph.D. Agent yace zai tambayi makarantar in turu mishi da takarduna. Duk takaddun dana turawa agent, sai ya turawa director, shi kuma ya turawa commissioner. Haka s**ayi ta tsarawa abinda agent zai tambayeni. Karshe dai, har cikin manyan abokanaina aka sami daya akace ya dinga bugar cikina yana tatsar bayanai. Kai kace kasurgumin dan-fashi ne ni ko kuma wani Hushpuppi.

Abinda yafi damuna shine, nagama zagaye dangi nayi musu sallama zanyi tafiya. Gashi kuma an soke sunana
Wadannan bayin-Allah kawai chaza suyi zaiyiyu ko baziyiyu ba, amma aka dinga kukulla abubuwa saboda a sami hujjar chanza sunan.

Ashe an bawa wani masinja a KASCO labarin abinda ya faru dani. Watarana naje, sai yace min ai akwai Hon. Lawan Hussaini a maaikatar. Yana da kirki da son taimakon Al’ummar sa. Yau zanyi mishi Magana, gobe ka same shi a office din. Nace to nagode sosai.

Gari na wayewa, sai ministry, wajen Hon. Ga tambayar daya fara yi min.

Hon. : Daga wacce karamar hukuma?
Ni: Kano Municipal.
Hon. : Ashe kai ba dan Gwale bane bama.
Ni: Hon. Ina Gwale ina Municipal, duk abinda akeyi ai muna iya tsallakowa.
Hon. : shiga kasami commissioner, kace kaine

Kafin na shiga office din kwamisha, na leko da charbina ta aljihun rigata na gefe. Kwamishina na gani, yace yanzu wannan charbin duk akaina yakare. Jeka za a maida sunanka.

Daga Bisani,
Bayan da muka gama karatun Masters a Sharda University India, sai memakarantar Watou P.K gupta, ya bani damar cigaba da Ph.D kyauta dalilin project dina. Saboda haka da kowa ya tafi ya banni.

Director Quality, Assurance
Bayan na dawo gida, naje ministry din, Director Quality assurance ya karbi takardar scholarship din da aka bani, ransa bai so ba.
Haka kuma ya taba kawo ‘yarsa asibiti makarantarmu, Sharda, muka hadu dashi, ya dafa kafadata cikin yanayi na tausasawa, yace "mun dauka bazaka zauna ba, allowance din da aka baku zaka cinye ka gudu". Ni kuma nace masa, kasan akwai yaron da yayi haka, shi yasa hankalinku bai kwanta ba. Karshe dai yayi min fata alheri.

Commissioner Doguwa
Tun kafin mu tafi, India ya nuna min in manta da komai, kar in damu.

Lawan Hussaini
Wata rana nazo hutu, na kirashi a waya, nace masa, na kawo mishi tsaraba, don inyi godiya. Yace kada na damu, ba sai na kawo mishi komai.

Masinja
Na sami labarin, Hon. Lawan na nuna kamar yayiwa ‘yan gidan su masinja alfarma, sbd haka yana bukatar a ramawa kura aniyarta. Gashi kuma duk ‘yan gidan nasu bbu wanda yasanni, bbu dangin iya b***e na baba. Masinja ne kawai yasani. Shima ba wani sanina yayi sosai ba. Ganina kawai yake ina zuwa ma’aikatar su.

Yau gashi, kusan shekaruna goma a India, inzo in kuma. Mun bude ofisoshi
1. Ploti number 10 Gwarzo Road, Kano daura da Treztech CBT Center, Kano
2. No. 205 Kofar Nassarawa daura Nuhu Bammalli Maternity Hospital, along Emirs Palace Road, Kano
3. Kano State Polytechnic, Central Administration, BUK Road, Kano, kusa da Suraj Global Ventures

Mun nemawa sama da yara 200 admission a makarantu daban-daban a kasar India ba tare da chajinsu ko sisi ba. Saidai kamasho da makarantun suke bamu. Kullum tururuwa ake zuwa ofisoshin mu. Bamu taba kai marasa lfy India ba a sami nasara ba. Muna tsayawa tsayin daka mutabbatar likitoncin sun fada mana, idan bamaiyiwa bane. Mukama mu fadawa mara lfy.

12/09/2022

Do you want to study abroad or medical tourism for your health?
1. Free processing charges
2. Facilitation of visa issuance
3. Scholarships offered by some universities
4. Free course sponsored by the Indian government - Visa issued on gratis, free flight ticket (to and fro), accommodation, and feeding allowance.
5. More than 3000 courses
6. Affordable fee option
7. Competent doctors and better medicine

Feel free to contact us

* Whatsapp: +91 87002 40912
call: 07020482338, 08060820401

*Address: Plot NO. 10 Gwarzo road, Kano. Near Trez computers
*Suraj Ventures, Kano State Polytechnic, Central Administration, BUK road.

KK INFRA KK Infra is a leading educational consultancy in Nigeria. We secure your admission and effective medical tourism in India. We treat our customers as kings and queens throughout their educational and medical journeys.

15/04/2019

Hukumar IMF, me lura da bunkasa tattalin arzikin duniya kullum na bawa kasashe shawara da su cire tallafin mai. To amma yawancin kasashen da s**a janye tallafin, suna da wasu hanyoyin na samar da makamashi, basu dogara kacokam akan makamashin man-fetir da iskar gas ba. Misali Kasar Argentina, Brazil, Amurka da Chana suna a gaba wajen amfani da kayan gona kamar su masara, rake da gero wajen samar da makamashin da suke amfani dashi a motonci da baburan sufuri. Ita kuma kasar Jamus tana amfani da duk wani abu dake iya rubewa ko kuma dagwalo wajen samar da makamashin. Kasar Denmarak na amfani da karfin iskar maliki yaumiddini domin chaja motocin su na sufuri. A takaice ko da fetri ko ba fetir, harkokin sufurin su na gudana.

A ganina, bai kamata Najeriya ta dauki waccan shawarar ta hukumar IMF din ba. Ganin yadda rayuwar talakawa ta ta'allaka akan makamashin man-fetir.

Hakan zai jefa talaka cikin halin ni'yasu da Kunchi ba tare da samun ingantaccen sakamako ba.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kano
70021