Addua makamin mumini

Addua makamin mumini

Share

Wannan page anyishine dan yan uwa musulmi

13/12/2023

"Duk Zuciyar Da Babu Ayoyin Al-Qur'an Babu Hadisi, Mayunwaciyar Zuciya Ce, Talakar Zuciya Ce, Dan Karamin Abu Sai Mutum Yaji Kamar Ya Rataye Kansa."

20/06/2022

Allah muna tuba kayi afuwa ga bayinka

05/04/2022

FALALAR ZIKIRI
Allah Madaukakin Sarki ya ce:
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِ
Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni.
Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152].

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً
Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran.

Ya ku wadanda s**a yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41).
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً
Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman.
Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35]
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ وَلاَ تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna.
Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205].
Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, k**ar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa k**ar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).)
Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? S**a ce ka

05/03/2021

ALHADITHUL AUWALU (1)
An amiril mu'iminina Abi Hafsin Umara Ibn Khaddabi, (RA) Kala: Sami'itu Rasulallahi (SAW) yaKulu: "Innamal a'amalu binniyati wa'innama li kulli imiri'in ma nawa, faman kanat hijratuhu ilallahi wa Rasulihi, fahijratuhu ilallahi wa Rasulihi waman kanat hijiratuhu lidunya yusibuha aw imra'atin yankihuha fa hijiratuhu ila ma hajara ilaihi". Rawahu Imamal muhaddithina Abu Abdullahi Muhammadu Ibn Isma'ila, Ibn Ibrahima, Ibn Mugirata, Ibn Bardizbah Al-bukhariyyu, wa Abu Hussaini, Muslimu Ibn Hajjaji Ibn Muslimin Al-Kushairiyyu Annaisaburiyyu fii sahihaihima alladhaini huma asahhul kutubi almusannafati.

HADISI NA DAYA (1)
An rawaito daga Sarkin Mu'uminai Abi Hafs, Umar dan Khattab, (RA) ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Dukkanin ayyuka ba sa yiwuwa sai da niyya, kuma kowane mutum akwai abin da ya niwaita ya tabbata gare shi. Wanda hijirar sa ta kasance saboda Allah da Manzon sa to, hijirarsa ta tabbata izuwa ga Allah da Manzonsa, wanda kuma hijirarsa ta kasance don duniya, ko kuma wata mace don ya aureta, to haKiKa hijirarsa ta tabbata izuwa abin da ya yi hijirar izuwa gare shi".
Shugabannin masu ruwaito hadisai ne s**a rawaito shi, su ne Abu Abdullahi Muhammadu dan Isma'ila, dan Ibrahima, dan Mugirata, dan Bardizba, Al-Bukhari, da kuma Abu Husaini Muslimu dan Hajjaju da Muslim Al-Kushairi, Al-Nisaburi a cikin ingantattun nan guda biyu wadanda su ne mafi ingancin littatafin ababar tsarawa.

19/02/2021

Salati Ga Annabi, Tsira da Amincin Allah Su Tabbata A Gare shi, bayan Tahiya;

اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.
Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, k**a sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, k**a barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed.

Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, k**ar yadda kayi salati ga Ibrahimu da alayen Ibrahim, lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, k**ar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu, da alayen Ibrahimu, lallai kai abon godewa ne, mai girma.

اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ. وَبَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ. إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.
Allahumma salli AAala Muhammad wa-'ala azwajihi wathurriyyatihi k**a sallayta 'ala ali Ibraheem, wabarik 'ala Muhammad, wa-'ala azwajihi wathurriyyatih, k**a barakta 'ala ali Ibraheem. innaka Hameedun Majeed.

Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa, k**ar yadda ka yi salati ga alayen Ibrahim. Kuma ka yi albarka ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa, k**ar yadda ka yi albarka ga alayen Ibrahim. Lallai kai abin godewa ne, mai girma.

اَللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ فِتْنَةِ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ.
Allahumma innee a'u'zu bika min 'athabil-kabr, wamin 'azabi jahannam, wamin fitnatil-mahya walmamat, wamin shari fitnatil-maseehid-dajjal.

Ya Allah ina neman tsari da Kai daga azabar kabari

28/12/2020

Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu).

Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura k**ar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (say your need) khayrun lee fee deenee wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.

Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da

18/12/2020

Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci

اللّهُـمَّ اجْعَـلْ فِي قَلْبِـي نُورًا، وَفِي لِسَـانِي نُورًا، فِي سَمْعِي نُورًا، فِي بَصَرِي نُورًا، مِنْ خَلْفِي نُورًا، وَمِنْ أَمَامِـي نُورًا، وَ مِنْ خَلْفِي نُوراً، فِي نَفْسِي نُوراً، وَأَعْظِمْ لِي نُوراً، وَعَظِّمْ نُوراً، وَاجْعَلْ لِي نُوراً ، وَاجْعَلْنِي نُوراً، اَللُّهُمَّ أَعْطِنِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي عَصَبِي نُوراً، وَفِي لَحْمِي نُوراً، وَفِي دَمِي نُوراً ، وَفِي شَعْرِي نُوراً، وَفِي بَشَرِي نُوراً ". "اَللَّهُمَّ اجْعَلْ لِي نُوراً فِي قَبْرِي .. وَنُوراً فِي عِظَامِي، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراً، وَهَبْ لِي نُوراً عَلَى نُوراً.
Allahumma j'al fi kalbi nuran, wa fi lisani nuran, wa fi sam'i nuran, wa fi basari nuran, wa min fawki nuran, wa min tahti nuran, wa 'an yamini nuran, wa 'an shimali nuran, wa min amami nuran, wa min khalfi nuran waj'al fi nafsi nuran, wa a'zim li nuran, wa 'azzim li nuran. Wa j'al li nuran, wa j'alni nuran. Allahumma a'tini nuran, wa j'al fi 'asabi nuran, wa fi lahmi nuran, wa fi dami nuran, wa fi sha'ri nuran, wa fi bashari nuran. (Allahumma j'al lin nuran fi kabri, wa nuran fi izami)
(wa zidni nuran, wa zidni nuran, wa zidni nuran) (wa hab li nuran 'ala nur).

Ya Allah ka sanya haske a cikin zuciyata, da haske a kan harshena, da haske a gabana, da haske a damana, da haske a haguna, da haske a gabana, da haske a bayana; Ka sanya haske a cikin raina, Ka girmama haske gare ni, ka girmama min haske, ka sanya haske gare ni, Ka sanya ni (na zama) haske, Ka sanya haske a cikin jijiyoyina, da haske a cikin namana, da haske a cikin gashina, da haske a cikin fatata, Ya Allah Ka sanya mini haske a cikin kabarina, da haske a cikin kasusuwana, ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka ba ni haske a kan haske.

24/11/2020

Addu'ar Yayin da za a yi Barci:
Idan mutum ya zo kwanciyar barci sai ya hada tafin hannayensa biyu, ya karanta wadannan surori na Alkur'ani, yana yin tofi cikin hannayen nasa;

(قل هو الله أحد)
(قل أعوذ برب الفلق)
(قل أعوذ برب الناس)
(Qul'huwallahu Ahad)
(Qul'a'uuzu Bi Rabbil Falak).
(Qul'a'uuzu Bi Rabbin Nas).
Sannan ya shafu su iy ainda zai iya na jikinsa; yana farawa da kansa, da fuskarsa da kuma gaban jikins.a ya yi haka har sau uku.

06/11/2020

[012] Going to the mosque

Search

[012] Going to the mosque



Allaahummaj'al fee qalbee nooran, wa fee lisaaanee nooran, wa fee sam'ee nooran, wa fee basaree nooran, wa min fawqee nooran, wa min tahtee nooran, wa 'an yameenee nooran, wa 'an shimaalee nooran, wa min 'amaamee nooran, wa min khalfee nooran, waj'alfee nafsee nooran, wa 'a'dhim lee nooran, wa 'adhdhim lee nooran, wafal lee nooran, waj'alnee nooran, Allaahumma 'a'tinee nooran, waj'al fee 'asabee nooran, wafee lahmee nooran, wafee damee nooran, wa fee sha'ree nooran, wa fee basharee nooran. [Allaahummaj'al lee nooran fee qabree wa nooran fee 'idhaamee.] [Wa zidnee nooran, wa zidnee nooran, wa zidnee nooran.][Wa hab lee nooran 'alaa noor.]

O Allah, place light in my heart, and on my tongue light, and in my ears light and in my sight light, and above me light, and below me light, and to my right light, and to my left light, and before me light and behind me light. Place in my soul light. Magnify for me light, and amplify for me light. Make for me light and make me a light. O Allah, grant me light, and place light in my nerves, and in my body light and in my blood light and in my hair light and in my skin light.1 [O Allah, make for me a light in my grave... and a light in my bones.](At-Tirmithi 5/483 (Hadith no. 3419).) [Increase me in light, increase me in light, increase me in light .](Al-Bukhari in Al-'Adab Al-Mufrad (Hadith no. 695), p. 258. See also Al-Albani, Sahih Al-'Adab Al-Mufrad(no. 536).) [Grant me light upon light.] (Al-Bukhari, cf. Al-Asqalani, Fathul-Bari 11/118.)

Reference: 1 Up to this point was reported by Al-Bukhari 11 / 116 (Hadith no. 6316) and by Muslim 1/526, 529-530 (Hadithno. 763).

Prev Intro Next

31/10/2020

Aslm ma'abota wan nan zaure zamu bude group na whatsapp nan da kwana kadan dan samun cigaba da taimakawa duk da haka muna son abamu gudun mowa sosai

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Kano