Imam Abdalla School For Arabic And Islamic Studies

Imam Abdalla School For Arabic And Islamic Studies Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Imam Abdalla School For Arabic And Islamic Studies, Education, Sharada Road, Kano.

01/09/2024

HUKUNCIN ASKE GEMU

Tambaya :
Malam menene hukuncin tsayar da gemu shin wajibi ne ko mustahabbi?, sannan aske shi haramun ne ko makaruhi ne ?

Amsa :
To dan'uwa Annabi s.aw yana cewa : (Ku sabawa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki), k**ar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta : 5553 da kuma Muslim a lamba ta : 259.
Wannan yasa da yawa daga cikin malamai s**a tafi akan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman k**ar Ibnu Hazm sun hakaito ijma'in malamai akan haka, k**ar yadda ya zo a littafinsa na maratibul ijma'i shafi na : 157.
Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai k**ar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da alhaji yakan yi bayan ya gama aikin hajjinsa.

Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke karawa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana k**a da tsohuwar da kyanta ya disashe, k**ar yadda Sa'adi ya fadi a Bahjatu kulubul abrar shafi na : 50 .

Saidai malamai suna cewa idan mutum yana garin da za'a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, saidai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta .
Don neman karin bayani duba littafin : Wujubu I'ifa'ul liha .
Allah ne mafi sani .

Jamilu Zarewa

29/03/2023
29/03/2023
13/07/2020

Address

Sharada Road
Kano
700

Telephone

+2348099482068

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Abdalla School For Arabic And Islamic Studies posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Imam Abdalla School For Arabic And Islamic Studies:

Shortcuts

Share

Category