24/07/2026
BABU ALHERI A CIKIN YAKI
Daga jiya zuwa yau yaki tsakanin Amurka da Iran ya kara muni sosai
Iran ta umarci mutanen da suke kusa da kadarorin Kasar Amurka a Kasashen Larabawa su kauce daga gurin, domin zata fara amfani da manyan kayan aiki
Sannan mayakan Houthi na Kasar Yemen sun kai hari kan wata kadara na Amurka dake Saudiyya, ita ma Saudiyya ta kai hari wa wata cibiya na mayakan
A fakaice Shugaban Amurka Donald ya shigar da Saudiyya cikin yakin, domin mayakan Houthi kayan Iran ne, kuma shekaran Jiya Iran ta tura wasu kwararrun Sojojinta masu sarrafa makami mai linzami zuwa Yemen
Kasar Ingila ta amince wa Kasar Amurka fara amfani da sansaninta domin kai hari zuwa Iran, wato yakin yana ta yaduwa
Akwai wani mummunan hari da Iran ta kai kan kayan leken asirin Amurka a Jordan, Amurka tace Iran bata da fasahar da zata iya harin gurin, ta zargi Russia da tallafa wa Iran
A kan wannan Shugaban Amurka ya gargadi Russia da China akan kar su kuskura su sayar wa Iran makamai
Wannan yakin fa kai tsaya yana shafarmu a Nigeria, an fara yakin nan muna sayan litar man fetur kasa da Naira 700, amma yanzu ya taba Naira 1400 duk a dalilin yakin
Allah Ka mana maganin duk wanda yake hannu a wannan yakin
Daga datty assalafiy