14/07/2020
(2,077)
===============
16/11/1441
07/07/2020
Assalammu Alaikum malam barka da warhaka ALLAH ya kara maka lafiya da dau kaka duniya da lahira.
Malam ina so'a irgumin ayuyi war wari sihiri, kuma da mai akey amfani dan war wari sihiri.
Wassalamu Alaikum
======
Farko ina so kasan Dukkan Aayoyin Al qur'ani warakane na kowane irin cuta, na zuci wato Tawhidi ko Shubhah, ko Shakka.
Hakanan kuma warakane na Ciwon Gabobi da shuran su.
Ibnul Qayyim (r) ya bude babi Guda a cikin Littafin sa:
الجواب الكافي لمن سأل عن الدواء الشافي.
Babi guda ya kira da:
فصل: القرآن شفاء.
Ya kara da cewa:
Fadin Allah (swt):
"وننزل من القرآن ما هو شفاء ورحمة للمؤمنين".
Yace: Wannan (من) don bayanin (جنس).
Duk inda ka dauka a Qur'ani don waraka to In shaa Allah zai zama waraka.
Amma akoi Malamanda s**a ware wadansu Aayoyi a masayin Aayar warware Sihiri, don Alakan da yake cikin Aayar da Cutar.
A takaice: Suratul Fatihah Annabi ya tabbatar tana magani.
Aayatul Qursiy Annabi (saw) ya tabbatar yana kariyane.
Suratul Baqarah ya tabbata yana korin Aljanu.
Suratul Ikhlasi da Falaqi da Nasi, duk suna Maganin Sihiri, kuma ya tabbatar a Nassi.
Kana da dama kayi amfani da su, amma kar ka manta da cewa: Qur'ani ko ina warakane.
Allah shine masani