*COPIED* *01*
*Maiyake kawo idan masoya sunyi rigima shiryawa take gagara, har take jawo rabuwa?*
*Kafin muje abin da yake jawo rashin shiryawar masoyan bayan saɓani, zai matuƙar kyau mu fara da abubuwan da suke jawo ɓatarwa ma tukuna.*
*- idan masoyinki bayason ya ganki da wani ko wata, kika ci gaba da saurararsu zai jawo kuyi rigima.*
*- idan kullum kina cisguna masa zaku ɓata*
*-idan kina jamasa aji dayawa zaku rabu, domin bakowane yake iya jure jan dayawa ba. Wani ajin ana taleshi sai ya tsinke kat.*
*-idan kuna yawan samun saɓanin ra'ayi (abin da yake so kina ƙinsa, ko abin da takeso kullum kasokeshi)*
*-idan kina nuna masa rashin damuwa dashi, ko abin da ya shafeshi.*
*-idan bakya muhimmantar da manyansa ko duk abin da ya ɗaukeshi da muhimmanci*
*-idan kika cika roƙon shi dayawa*
*-idan kina yawan gyara masa kuskurensa. Komai yayi ki nuna bai iya ba ko ba haka yak**ata yayi ba. Shi zai rinƙa ganinsa a raini ne. Kekuma ƙila har ga Allah gyara kikeson yi.*
*- idan kina ɓoye masa wasu abubuwa da ya cancanci ya sani, duk lokacin da ya sani agurin wani ko wata, zaiga ko bashi da kima a gurinki, ko kokuma kina munafuntarsa.*
*-munafunci*
*-ƙarya*
*-mugunta*
*-son kai*
*-cin fuska*
*-cin mutunci*
*-wulaƙanci*
*-raini da rainin wayo ko aji*
*-idan kina nuna masa shifa ana sonshi ne amatsayin wucin gadi. Da original ya fito zaki masgeshi gefe.*
*-idan ya gano ke ba ta aure bace zaku rabu, matuƙar shiɗin da niyyar aure yazo*
*- idan yaga bakya ɗaukar alaƙarku da muhimmanci, ko yanason turowa ki nuna masa a,a*
*- idan ya hanaki abu kiyi ƙememe abin ki.*
(Halayyar yawancin mata a yanzu kenan su sun iya komai kuma ba za'a yi musu gyara ba)
*-idan yaga sirrinsa baya ruƙuwa*
*-idan yaga suna dayawa 'yan takara agurinki kuma shi da gaske yake, amma ko kusa da yazo na farko ma azaɓinki baiyi ba.*
*Dsr*
*Haka kaima idan kana yimata waɗannan abubuwan zasu iya jawo muku rabuwa*
*-taita nuna ta damu dakai, amma kana yimata halin ko in kula*
*-cutarta*
*-ƙarya mai ƙarfin gaske*
*-zagi*
*-musgunawa*
*-cin amana*
*-wulaƙanci*
*- tara mata abokai kala-kala kullum, k**ar wata hajar sayarwa. Ko kace k**ar tana kotu.*
*-ɗaukar ta amatsayin kayan ado, ko rashin kimantata*
*-Rowar tsiya da maƙo da ƙamƙamo kazama banban tsogo kuma matsolo*
*-rashin tura magabata gashi kun ɗau lokaci. Son naka sai ya sane, muddin ta ƙosa tayi aure.*
*-Nuna mata alamomin yaudara ƙiri-ƙiri*
*-Nuna mata kai ɗin ba dagaske kake sonta ba*
*-Rashin kishinta*
*Dsr*
*Waɗannan bubuwan yawanci sune suke jawo rigima da faɗa tsakanin masoya.*
*Idan mun ganosu to mai yake jawo ƙin shiryawar bayan anyi faɗan ko rigimar?*
*Zan cigaba a rubutu na biyu*
*MUNA MARABA DA SHARHI GYARA KO KARIN HASKE GAMI DA TAMBAYA*
Soyayya Jigon Rayuwa
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Soyayya Jigon Rayuwa, Dala, Kano.
*❤ SOYAYYA JINGON RAYUWA❤*
*🥰DAN TSOKACI GA MASOYA🥰*
*A wanan rubutun zamu fahimci wasu abubuwa kadan wadanda budurwa zata gani a wajen saurayi taji ta kamu da son shi da sauri.*
Abubuwan su ne:
*1. 'Yan mata na saurin kamuwa da soyyayar Saurayin da yake gwanin iya kwalliya koda kuwa bashi da karfin sanya sabbin kaya ko kaya masu tsada*
*SHARHI*
*Yawancin 'yan mata na son saurayin da ya iya saka kaya, matukar kana daga cikin samarin da s**a iya ado da kwalliya tabbas 'yan mata za su soka cikin sauki, domin zaka dinga burgesu ita kuma mace tana fara soyayya ne daga ganin abinda ya burgeta*
*2.Wani abu dake sanya budurwa jin soyyayyar Saurayi ta shiga ranta shi ne yayin da saurayin ya kasance mai bada dariya ma'ana barkwanci ko raha ko sanya su nishadi*
*SHARHI*
*Kusan kowace mace tana san saurayi ko namijin da zai dinga sanya su dariya a lokuta da dama, ba wai Ina nufin ka zama cali cali ba ko soko ko bugun shaho a wajen mata, a'a Ina nufin ka zama ma'abocin sanya ta nishadi raha ta yadda zata dinga bukatar ku hadu domin ta tabbata kuna haduwar zatayi nishadi.*
*3. Namijin da yake yawan kasancewa cikin kamshi, kana sanya turare ko kuma koda kazo Inda take ba zataji yanayin iskar wajen ta canza ba ka kasance koda tana tare da kai ba zata ji warin hammata ba, ko warin gumi ko warin rana b***e uwa uba warin baki, hakan zai sa 'yan mata su soka.*
*SHARHI*
*Magana ta gsky mata suna matukar kokari da juriya akan da yawa daga cikin mazaje ta hanyar jure wari kala kala daga wasu mazan da basu damu da gyaran jikinsu ba, haka zata yi ta hkr sbd tana sanka ko kuma tana neman mafitar kawai ka aureta sbd auren take so a lokaci guda kuma tana rainaka*
*4. Dukkanin mata suna san namijin da yayin da kake hira da it's kana iya warware abubuwa ko matsaloli cikin sauki da kwanciyar hankali, babu hayaniya ba fada, kana gamsar da itta abu yake dai-dai da warware mata kowace irin matsala, wannan halayya nasa 'yan mata suji suna kaunar namiji.*
DAGA: BABAN AMINATU
KOWA YA DIBA DA ZAFI // 02
⭐ A gabansa take tsayuwa da wasu samarin, wani lokaci sai ta bar su sannan ta zo wajensa, tunda ta ce babu k**arsa sai ya share, amma fa ta ce kar ya yi wata alaqa da iyayenta sai ta gama shiryawa.
⭐ Mutumin naka har da haka bai gane ba, wata jumu'a da ya yi mata waya cewa yana kan hanya sai ta ce masa ya zo gobe da Azuhur ba za ta iya fitowa ba, kuma gaskiya ta gaya masa, amma da ya zo din sai ya halarci daura aurenta, ashe gayyatarsa ta yi!
Zamu cigaba insha Allahu.
Rubutawa:- Baban Manar.
KOWA YA DIBA DA ZAFI // 01
⭐ Don qauna ina qaunarka, sai dai ina so ne ka sani ba bauta zai kai ni gidanka ba, ko a gidammu akwai mai mana aiki, kuma mu iyayemmu ne ma suke taimaka mana wasu abubuwan.
⭐ Wannan in dai soyayyar kake nema ba sha'awace ta dabaibaye ka ba ta gama isar maka da saqo, sauran ya rage naka.
Zamu cigaba insha Allahu
Rubutawa:- Baban Manar
DAN SAURARA👂// 05
🤜🏻 Qaryar arziki na aron mota, kayan sanyawa, sunan wasu, ko gidajen zama na daya daga cikin dalilan sabalbalcewar wasu auratayyar.
Zamu ci gaba insha Allah.
Rubutawa:- Baban Manar.
DAN SAURARA👂// 04
🤜🏻 Kar uwaye su taimaki shaidan, baligi da baliga a manne da juna, cikin duhun dare, nesa da idanun jama'a, me kake tsammani?
Zamu ci gaba insha Allah.
Rubutawa:- Baban Manar.
DAN SAURARA👂// 02
🤜🏻 Duk lokacin da kuka bar wa uwaye mata maganar auren 'ya'yanku mata, to ku shirya wa abin da zai biyo baya.
Zamu ci gaba insha Allah.
Rubutawa:- Baban Manar.
DAN SAURARA👂// 01
🤜🏻 Isa aure a wajen mace ba girman jiki ba ne na hankali ne.
🤜🏻 Kar ka ce don tana son ka sai ka aure ta, dubi tsawon rayuwar da za ku yi tare.
Zamu ci gaba insha Allah.
KOWA YA DIBA DA ZAFI // 03
⭐ Ta ce tana qaunarsa, kuma ta dauki alqawarin za ta aure shi, duk kuwa da sanin cewa ba ita za ta ba da kanta ba, a dai-dai wannan lokacin, ta bayyana cewa iyayenta ba sa so, yallaboi kuma ya san da haka amma ya ci gaba.
⭐ To bayan 'yan watanni ta zo wurinsa da kukanta har da hawaye, ta gaya masa cewa mahaifinta fa ya ce zai ba wani, sai dai a dada dagewa da roqon Allah, gogan bai dau haske ba, sai da ya ji ta auri wani sai ya ce Allah ya isa an yaudare shi, anya haka ne kuwa?
Zamu cigaba insha Allahu.
Rubutawa:- Baban Manar.
KOWA YA DIBA DA ZAFI // 01
⭐ Don qauna ina qaunarka, sai dai ina so ne ka sani ba bauta zai kai ni gidanka ba, ko a gidammu akwai mai mana aiki, kuma mu iyayemmu ne ma suke taimaka mana wasu abubuwan.
⭐ Wannan in dai soyayyar kake nema ba sha'awace ta dabaibaye ka ba ta gama isar maka da saqo, sauran ya rage naka.
Zamu cigaba insha Allahu
Rubutawa:- Baban Manar.
MASU HIKIMA SUNCE:
👉🏻 Hankali: Karancin magana shi ke sa ta yi dadi. Karancin cin abinci shi ke sa lafiya. Karancin hulda da jama'a kuwa shi ke kawo aminci.
*
*
👉🏻 Kyau yana jan hankalin idanu ne, halin kwarai da magana mai dadi su ke k**a zukata.
*
*
👉🏻 Ambaton Allah: Hamdala tana yaye damuwa. Hailala tana karfafa zuciya. La haula tana warware matsaloli, Istigfari yana kawo arziki. Salati yana daga darajar mutum a cikin aljanna.
*
*
👉🏻 Sukari guda daya yana canja dandanon shayi. Haka ne kalma daya take canja dandanon zukata.
*
*
Yaɗa bayani daga naku:- king
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Culinary Team
Attire
Telephone
Website
Address
Dala
Kano
234