02/02/2024
Komai rashin lissafin mutum, daga wannan cece kucen kadai ya kamata ya fahimci manufar gayyatar da aka yi wa Shehu Dr.
Donmin maimakon mu ji bisharori kan Gazza da rahotanni masu dadi. Kawai sai muka ga sabanin haka
Ana dira tun daga airport aka fara da zagin yan uwansa masu da'awa, cewa duk wanda ya ce ya je Iran ne karbo kwangila munafuki ne.....gabar farko ke nan, tun ma da yawa basu san ina yaje ba
Aka zo gaba ta biyu, aka zagi Saudiyya da kasashen larabawa aka Yabi Iran da mutan kasar.
Aka zo gaba ta uku, aka fara yin kamfen na tura yara qasar Iran wai su koyo karatu.
Aka zo gaba hudu, cewa sabanin da ke tsakanin sunna da shi'a siyasa ce ba akida ba..
Aka zo gaba ta biyar, cewa zagin Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ba kafirci ba ne ai ...
Aka zo gaba ta shida, aka ce Ahulussunna suma suna zagin ahlul bait, kamar yadda yan shi'a ke zagin Sahabbai....
DON ALLAH INA LABARIN GAZZA YAKE?
KO SAU DAYA JUN JI AN FADI WANI ABU AKAI
ME ZAI HANA A BAR WANNAN GABAR HAKA , A FADI ME AKA CIMMA A TARON KAN GAZZA.
WACCE NASARA AKA SAMU DAGA TARON ZUWA YANZU
ME AKE SO MUSULMAI SU YI GA YAN UWANSU WANDA AKA YANKE A TORON
Magaji F Ishaq Zarewa