23/08/2026
🚨 NAF TA ƘARA ƘARFAFA AIKI A SARARIN SAMANIYAR SAKKWATO DOMIN YAƘI DA ’YAN TA’ADDA
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ƙara ƙarfafa ayyukan sama a Jihar Sakkwato, domin tallafa wa ayyukan haɗin gwiwar jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a yankin Arewa maso Yamma.
Rundunar ta bayyana cewa ƙarin ayyukan sama zai taimaka wajen sa ido, gano wuraren da miyagun ƙungiyoyi ke fakewa, dakile motsinsu tare da samar da tallafin gaggawa ga dakarun ƙasa.
NAF ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Daga: Ashir Mai Jama’a, Sokoto
📰 GM HAUSA NEWs