Nishadi koda yaushe

Nishadi koda yaushe

Share

+

13/07/2023

Rayuwa tana koya maka so, yau da gobe na koya maka wa kake so, matsalolin rayuwa na koya maka wa ke son ka.

10/07/2023

Duk wanda ya cuci kuruciyarsa, to tabbas tsufansa zai cuce shi.
Allah kaimana kyakykyawan karshe

28/06/2023

TALES TIME: GIDAN MU SUKE NUFI

Wata rana Shehu na zaune shi da danshi suna hutawa. Sai ga jama'a dauke da gawar mamaci zasu wuce, a can karshen baya kuma wata mata ce ke tsalle tana tuma tana kururuwa gami da fadin cewa "yanzu me gida shikenan za a kaika gidan da babu shinfida, ba katifa, babu gurasa ba zuma...."

Koda dan gidan Shehu Jaha yaji zantukan wannan mata sai ya waiwayo ya dubi uban nasa yace "Shehu wallahi gidanmu suke nufi zasu kaishi"

Rai a ɓace Shehu ya kalli yaron yace "Saboda mune muka yanke ma talauci cibiya ba."

14/06/2023

Tales Time: Sarki ya gayyaci Shehu Jaha.

Jama'ar gari suna yawan kawo ma sarki koken cewa hakima suna ha'intar sarki ta hanyar kwashe kayan Baitul Mali, sannan kuma idan sarki ya ba abu a Bama talakawa, basu bayarwa.

Wannan abu yina ɓata ma sarki rai ƙwarai da gaske, amma kuma sai dai, ya kasa gane ko waɗanne hakimai ne aciki b***e ya hukunta su.

Wata rana sai aka kai ma sarki labarin irin hikimomi da fasahar Shehu Jaha. Ai kuwa babu ɓata lokaci Sarki yasa aka kirawo Shehu.

Bayan sarki ya kammala Bama Shehu labarin duk irin matsalolin dake faruwa, sai Shehu yace a gayyato duk hakiman su zo gidan sarki domin suyi walimar cin abinci. Amma kafin su zo, a zuba kwabbai da zinari acikin buhuna a ajiye acikin zauren gidan sarki.

Ganin waɗannan kwabbai da zinari da hakimai s**ayi, sai marasa gaskiya daga cikin su s**a fara sata suna zubawa a aljihun su.

Bayan hakimai gaba ɗaya su sun taru an gama walima, sai Shehu yace ma sarki "Ranka ya dade tunda an gama cin abinci, yanzu kamata yayi kowa ya ɗan taka rawa ya girgije." Sarki yace ai kuwa haka za'ayi, a kira masu kalangu."

Bayan masu kalangu din fara kiɗa sai hakimai kowa ya tsaya cif babu mai rawa sai mutum biyu tare da shehu, sarki kuma na kallon su.

Sarki yace dole kowa sai yayi rawa ko kuma a kashe shi. Ai kuwa hakimai na fara rawa sai ga ƙaran kwabbai da zinari na tashi kacau-kacau acikin aljhunan su.

Shehu yayi dariya yace "ranka ya dade, yanzu kaga ɓarayin ka masu sace kayan Baitul Mali."

13/06/2023

Abu 3 basuda wata fa'ida
DUKIYA A Hannun marowaci
Takobi A Hannun Matsoraci
Alkalami A Hannun Munafiki.

10/06/2023

Babu Mai iya baka abinda Allah Bai baka ba,kuma Babu Mai hana ka Abinda Allah Ya baka

Allah ka ƙara mana wadatar zuciya🤲

08/06/2023

Samari 3 sun je "Interview".Shugaban kamfanin sai ya ce musu " 2 + 2 = 5 "!!??

Sai na farko ya ce, tabbas haka amsar ta ke ran kai daɗe.

Na biyu ya ce, ran kai daɗe in muka ƙara ɗaya 1 amsar zata zama 5.

Na uku ya ce, ran kai daɗe amsar ba daidai ba ce, 4 ita ce daidai.

Bayan kwana 2 sai aka kafe sakamako, na 1 da na 2 sun ci amma na 3 ya faɗi.

Mataimakin Shugaban Kamfanin da ya ga haka, sai ya tambayi Shugabansa, ya haka? bayan na 3 shi ya amsa tambaya daidai...!!!

Shugaban ya ce: Na 1 maƙaryaci ne, kuma ya san shi maƙaryaci ne amma yana son abin da zai burge mu, irinsu abin buƙata ne a wurin aiki.

Na biyu ya yi amfani da ƙwaƙwalwarsa, shi ma abin buƙata ne. Na 3, mai gaskiya ne, kuma ya san akan gaskiyarsa yake, ba zai canza ba, irinsu suna bamu wahala wajen aiki.

Ya kalli mataimakinsa ya ce, in ka fahimci abin da nake nufi, shin 2 + 2 = 5?

Mataimakin ya ce, ran kai daɗe bayan na saurari bayananka; mutum mai ƙaramar ƙwaƙwalwa kamar ni ba zai iya amsa tambayarka ba.

Shugaban sai ya ce, irin nau'inku su ne munafukai, kuma muna ƙaunar aiki da ku...!!!

06/06/2023

IDAN YA KAWO KUDIN A BA ALKALI
SHEHU JAHA!😂

Wata rana Shehu Jaha yana cikin tafiya sai wani matashi ya mareshi don haka yace ba zai yarda ba, da aka je gaban alkali sai alkali yace “mu anan kasar idan aka mari mutum za a bashi fam daya”

Don haka ya umarci wannan yaro da yaje yazo da kudi a ba Shehu. Ashe yaron dan ammin alkali ne don haka yayi mai inkiya da kada ya dawo.

Shehu yayi jira har ya fara gajiya yaro bai dawo ba, don haka sai ya lallaba kusa da alkali ji kake tasss !! Shehu ya kwashe alkali da mari yace “idan ya kawo aba alkali kudin”

Shehu mai Abin mamaki!😅

04/06/2023

🤣🤣🤣🤣

*Wani mai gidane yayi sabuwar Amarya, 💃🏼💃🏼💃🏼sai rannan suna cikin cin abinci, sai Uwargida 💁🏻💁🏻💁🏻tace Maigida wai don Allah a tsakanin mu wakafi so? Amarya tayi karaf tace yauwa ka fada mana! Sai Maigida yace dukkan ku inason ku da bana sanku ai da ban auroku ba. Uwargida gaskiya sai kafada mana! Amarya gaskiya kam kafada kawai, can sai Amarya tace yauwa yanzu ace mun hau jirgin ruwa sai yayi hatsari kuma daya daga cikin mu kake da damar*
*dauko wa wazaka dauko? Can sai Maigida ya kalli Uwargida yace ke dama kin iya ruwa ko?😂*😂😂😂😂😂😂😂

03/06/2023

Wani yaro ne a Makaranta baya gane lissafi,akace masa 2 a debe 2 Ma'ana 2-2 Sai Yaron ya kasa. Sai malamin su yabashi fanke guda 2, Sai a karbi su akace yanzu saura me
Sai yaro yace saura maiko 🤣🤣🤣🤣🤣🤣

03/06/2023

Nishadi 😂
Wani Dan Fulani ne bashida lafiya sai aka kaishi asibiti to a dakin da aka kwantar dashi akwai gadaje guda hudu akwai mutum biyu agabansa shine na uku sai kuma wani abayansa wato cikon na hudun

Wata rana sai na farko ya mutu washe gari sai na biyun ya mutu akwana na ukun Dan Fulani yaje yin fitsari kafin yadawo yaga na hudun ya mutu !
Aikuwa yana zuwa ya tattara kayansa ya gudu yabar asibitin yana zuwa kauyensu sai ya hadu da Dan uwansa yace jauro har an sallamoka ne ?

Nan take yabude baki yace aradu mutuwa ce take bin layi tana daukewa tadauke na farko tadauki na biyu natafi fitsari datazo Bata ganni ba ta dauke na hudun

Sai dan uwan nasa yace kaii jauro aradu gwara da kagudo kaikam ka auna arziki fitsarinka ya ceceka 😂😂

01/06/2023

Duk wanda ya gaji da haƙuri to ba haƙurin yayi ba,domin gajiya da haƙuri Shima Rashin haƙuri ne.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kano