Pantami for a Better Gombe

Pantami for a Better Gombe

Share

𝗗𝗿 𝗜𝘀𝗮 𝗔𝗹𝗶 𝗜𝗯𝗿𝗮𝗵𝗶𝗺 𝗣𝗮𝗻𝘁𝗮𝗺𝗶 𝗳𝗼𝗿 𝗮 𝗕𝗲𝘁𝘁𝗲𝗿 𝗚𝗼𝗺𝗯𝗲✅

02/01/2026

WAYE NE Professor Isa Ali Pantami ?



Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami mashahurin malami, masani a harkar fasahar sadarwa (ICT), masani a tsaron intanet (Cybersecurity), malamin addinin Musulunci, kuma tsohon Ministan Gwamnatin Tarayya ne a Najeriya.
📌 Haihuwa da Karatu
An haife shi a ranar 20 ga Oktoba, 1972 a Pantami, Jihar Gombe.
Ya yi karatun Computer Science a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), inda ya samu Digiri (B.Tech) da Digiri na biyu (MSc).
Ya kuma samu MBA a Technology Management.
Ya kammala Digirin Digirgir (PhD) a Computer Information Systems a Robert Gordon University, Scotland.
Ya halarci manyan kwasa-kwasai da horo a jami’o’i irin su Harvard, MIT, Oxford da Cambridge.
🎓 Aiki a Ilimi
Ya kasance Malami (Lecturer) a Jami’ar ATBU.
Ya yi aiki a Islamic University of Madinah.
A shekarar 2021, aka nada shi Farfesa a fannin Cybersecurity a Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Owerri (FUTO).
💼 Aikin Gwamnati
A shekarar 2016, aka naɗa shi Babban Darakta (DG/CEO) na NITDA, inda ya ƙarfafa dokoki da tsare-tsaren ICT a Najeriya.
Daga 2019 zuwa 2023, ya zama Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital.
A lokacin mulkinsa, ya jagoranci shirye-shiryen:
National Digital Economy Policy and Strategy (2020–2030)
National Broadband Plan (2020–2025)
Wadannan sun taimaka sosai wajen bunƙasa intanet da tattalin arzikin dijital a ƙasar.
🌍 Matsayi a Duniya
Ya shugabanci World Summit on the Information Society (WSIS) a ƙarƙashin ITU a 2022.
Kungiyar African Union ta naɗa shi Co-Chair na African Scientific Research and Innovation Council (AU-ASRIC).
Yana da fellowship a ƙungiyoyi masu daraja k**ar British Computer Society da Nigeria Computer Society.
🕌 Addini da Al’umma
Farfesa Pantami shahararren malamin Musulunci ne kuma Babban Limamin Juma’a, yana haɗa ilimin zamani da koyarwar addini wajen wayar da kan al’umma.
⚠️ Muhawara
A wasu lokuta, kalamansa na sun jawo muhawara a kafafen yaɗa labarai.

Daga Alkalamin ✍️
Asmau

29/07/2025

ALHAMDULILLAH❤❤❤

06/12/2023

RUBUTACCEN AL AMARI
.

A Cikin Wannan Qanqanin Lokachin Ne Zaka Bi Umarnin Ubangijinka Ka Samu Rayuwar Jindadi Mai Tsayi A Rana Gobe Alkiyama…

A Cikin Wannan Qanqanin Lokachin ne Zaka Sa6awa Umarnin Ubangijinka Kasamu Mummunar Rayuwa Mai Tsayi A Rana Gobe Alkiyama…

"Zaka Iya Zuwa Duniya Ka Rayu Tsawon Shekaru 40,60,70 ko 90, Iya A Dadin Shekarun Da Allah Ya Dibar Maka A Duniya Zakayi.... Kwanciyar Kabari Kuma Kana Iya Shafe Shekaru 200, 400 ko 1,500 Ba'a yi Tashin Qiyama Ba".

"Kuma A Nan Duniya Ake So Kayi Tanadin Wancan Doguwar Kwanciyar".

A Cikin Shekaru 40 Ko 60 ko 80 ko 100 Ake So Kayi Shirin Kwanciyar Shekaru 1000 Ko dubunnai

Wuni Daya Na Lahira Yafi Shekara 1 Na Duniya ( Innalillahi Wa inna Ilaihi Raju um )
Tabbas Masu Imani Ne Zasu Ci Moriyar Rahamar Allah In Sun Shiga Aljannah

Mushirikai Da Mujurumai da Fasikai Masu Sa6on Allah Tabbas Sun Shiga Mummunan Sak**ako A Rana Gobe Alkiyama…

Rayuwar Da Zaayi Bayan Kowa Yasamu Sak**akon Abinda Ya Aikata A Duniya Wato Yan Aljannah Sun Tafi Aljannah…

Yan Wutar Jahannama Sun Tafi Wutar Jahannama Allah Yayi Mana Tsari Da Ita Amen

Babu Rana Babu Dare Babu Sapiya Babu Wata Ballantana Shekara

Shekaru Ne Marasa Adadi Marasa Qarshe Shekaru Billion Nawa Za ayi A Lokachin Allah ( SWT ) Shine Yasani Allah Ubangiji Ka Yafe Mana Kasa Muna Da Rabo Mai Kyau A Rana Gobe Alkiyama… Amen Summa Amen

Duk Mai Tunani Wannan Rana Bazai Ta6a Shagala Da Wannan Duniyar Ba. Rana Ce Da Dan Adam Zai Gane Duniya Ba Komai Bace Kamar Mafarki Ce Ka Kwanta Da Safe Ka Tashi Da Yamma Dan Adam Zaiji Kamar Ma Bai Ta6a Rayuwa A Wannan Duniyar Ba Babu Abinda Zai Hana Wannan Ranar Tazo Maka Saidai In Kwanan Kane Na Duniya Bai Qare Ba
Allah Ubangiji Yasa Mudace Amen 😰😰😨😨😥😥😟😢😭

AMIN YA HAYYU YA QAYYU
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

05/12/2023

Takaitaccen Tarihin Sayyidina Umar dan Khadabi R.A -
by
Suleiman Inuwa

Wanene Sayyidina Umar ❓👇

Shine Umar Dan khadabi Dan Nufailu Bakuraishe, Ana Masa Alkunya Da Aba Hafsa, Mahaifiyarsa Hantamatu Bintu Hashim Dan Mugiratu.

Sayyidina Umar Yana Daga Cikin Sabiqina a Musulunci, Yana cikin Asharatu Biljanna, Na 2 Khalifa ga Musulmai Bayan Wafatin Annabi SAW, farkon Wanda Akayimasa Laqabi Da Amirul Muminina.

Annabi SAW yace: ”Umar Fitilar 'yan Aljanna".

Haihuwar Sa 👇

An haifeshi a Makka Bayan Shekarar Giwa Da Shekara 13.

Musuluntarsa 👇

Ya Musulunta Acikin Watan Zulhijja Shekara 6 Daga Annabata a Lokacin Yanada Shekara 26, Ya Musulunta Bayan Mazaje 45 Da Mata 11.

Ibn Abbas yace: Lokacin Da Sayyidina Umar Ya Musulunta Jibrilu Yasauka, Yace: Ya Annabi Muhammad SAW Halittun Sammai Suna Can Suna Farin Ciki Da Musuluntar Umar.

Darajarsa 👇

Kadan Daga darajarsa

Sayidina Umar Yana Musulunta (RA), Musulunci Yakara Daukaka, Yayi Hijira a Bayyane, Ya Halarci Dukkan Yakoka Tare Da Annabi SAW.

Farko Khalifa Da Aka Fara kira Da Amirul Muminina, Farkon Wanda Yafara Rubuta Tarihin Hijira, farkon Wanda Yatara Mutane Akan Sallar Tarawihi.

Yabude Iraki, Busra, Farisa, Mausul, Misra Da Askandariya, Shine Farkon Wanda Yafara Mubayi'a ga Sayidi Abubakar.

Annabi SAw Yace : Da Akwai Wani Annabi Bayana Da Yakasance Umar Dan Khadabi ne.

Tawaliunsa 👇

Yakasance Mai Tsoron Allah Da Adalci, Mai Yawan Azumi Da Tsayuwar Dare Idan Yana Limantar Mutane Sallah Zakaji Sautin Kukan Sa.

Siffarsa 👇

Jismiya Yakasancr Mai Tsawo, Farine Da Ja, Idan Yana Tafiya Kace Yana Akan Abin Hawa Yake.

Siffa Ta Dabia Mai Adalci, Da Tausyi, Mai Kaifin Hankali, Mai Cikakkiyar Imani Bayada Hassada ga Kishin Musulunci.

Wafatinsa 👇

Yayi Wafati Yana Da Shekara 63 Ranar Laraba 23 ga Zulhijja.

An birneshi Ranar Lahadi Adakin Nana Aishatu RA, Ya Zauna a Khalifa Shekara 10 Da Wata 6.

Wallahu A'alamu🙏🙏

Duniyar Musulunci Page

04/12/2023

Aboki guda daya ne zai taya ka kwanciyar kabari. Shi ne aikinka. Aikata alheri don ka samu aboki na kwarai a wannan kogo da ba shi da makawa.

04/12/2023

Wanda ya fi ka wadata ba lalle ne ya fi ka arziki ba. Wadatacce shi ne wanda ya ke samun biyan bukatunsa"

29/11/2023

Hukuncin yima mamaci kuka😭

" Jikar Manzon Allah s.a.w Umamatu ta rasu, sai akaga hawaye na zuba afuskar MANZON ALLAH s.a.w😭 alokacin da yake sata cikin qabari"

"Sai sahabbai s**a tambayi Manzon Allah " Ya rasulullah ka hanamu kuka, amma gashi kanayi, sai Manzon Allah yace " Ba wannan aka hanaku ba, kururuwa ko kuka mai kara shi aka hana. " Inji Manzon Allah.

Lallashin mai kuka abinsone, amma akyaleshi ya zubar da hawaye😭domin yana rage radadi.

Allah yajikan mamatanmu.

Duniyar Musulunci Page

28/11/2023

Dalilin dayasa MUNAFUKAI ke ganin cewa Sheikh Professor Isa Ali Pantami Dan INTER-FAITH ne:

Kowa yasan cewa sheikh pantami zallar ilimi yake bajewa awurin karatunsa, baya zagin kowa, baya cin mutuncin kowa, baya s**ar wata kungiya ko wata darika, baya k**a sunan kowane malami acikin karatunsa.

Kuma wannan shine koyarwa irin ta annabi muhammad SAW, koyarwa irin ta addinin muslunci.

Kuma wallahi duk masu s**ar wannan bawan Allah (sheikh isa ali pantami) wallahi hassada ce kawai suke masa, domin yafisu samun daukaka, yafisu ilimin addini, yafisu ilimin boko, yafisu daraja da kima acikin al’umma.

Kuma wallahi ina yima wannan bawan Allah kyakkyawan zato cewa duk da’awarsa don Allah yakeyi, ba don neman suna ko neman abun duniya ba.

Idan suna ne, wanne irin suna ne sheikh pantami beyi ba har kasashen larabawa alfahari sukeyi dashi.

Idan mukami ne ko matsayi, wane mukami ne yake nema yanzu?? Wanda yayi ministan sadarwa na shekaru hudu. Duk gwamnonin nigeria abokan shi ne, da senatoci, da yan majalissu.

Idan kudi yake nema, wane irin kudin ne bashida ahalin yanzu??

AMMA DUK MALAMIN DA KAGA:

1. Bashida aikin yi sai s**ar sauran malammai

2. Bashida aikin yi sai s**ar gwamnati

3. Bashida aikin yi sai zakulo laifukan mutane yana tada jijiyar wuya.

4. Duk malamin dake kallon kowa akan kuskure, shi kadai ne Wanda yake kan gaskiya.

To wallahi yasabawa koyarwar addinin muslunci, bahaka annabi saw yayi da’awa ba, ba haka addinin muslunci yazo ba.

Malami ya mayarda mimbari wurin cin mutuncin mutane, wurin cin mutuncin bayin Allah, wurin zagin gwamnati, wurin zagin sarakuna, wurin zagin sauran malammai yan uwansa.

Wannan ba mimbarin karatun addinin muslunci bane, sai dai mimbarin raba kan al’umma da cin mutuncinsu.

To ko shakka babu wannan malamin yana kan kuskure, ko kufito ku gayamai gaskiya ko kuyi shiru.

Yaku AHLUSSUNNAH kufito ku fadi gaskiya, ba abunda za’ayi muku, sai dai Allah yabaku ladan aikin alkhairin da kukayi.

Iya abunda kuke tsoro shine, kuna jin tsoron kuyi magana akansa ya hau mimbari yaci mutuncinku. Wannan shine abunda kuke shakka.

Allah yabamu ikon bin gaskiya da aiki da ita.

Alhassan Mai Lafia

27/11/2023

TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI(AMEEN)

(manzon Allah S. A. W) "yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al'umma ta"

Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu " usman" usman dan Amir dan Amir dan ka"abu dan sa"adu da taimu dan murratu dan ka"abu dan lu"aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka"abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya "Abdul ka" aba" daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi "Abdullahi" An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi"antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da "Atiku" shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Muhammad (S. A. W) shine yafara haduba a addinin musulunci. Shine abokin zaman kogo tare da manzon Allah na farko kuma shine nafarko cikin sahabbai goma da aka musu albishir da gidan Aljannah tun a duniya shine farkon Amirul hajji kuma yana cikin marubuta wahayin da akema Annabi Muhammad (S. A. W) An haifi Sayyidina abubakar (R. A) a makka bayan Shekara giwaye da shekaru uku (573 A. D) manzon Allah. Ya girma shi da shekaru uku. Yana cikin manyan shuwagabannin kuraishawa a lokacin jahiliya kuma a bakin manzon allah ne na kasa tun kafin aiko shi. Sau dayawa ma. Yakanje gidan shi su tattauna shine mafi sani duk larabawa game da tarihin nasabar kuraishawa.
Kuma yakira mutane da yawa zuwa ga addinin musulunci. Biyar daga cikin su suna cikin sahabbai goma. Da aka yiwa bishara da Aljannah sune k**ar haka :
Ya sha a zaba iri - iri daga kafiran makka saboda shigar shi musulunci
Har takai babu wani musulmai da azabtu k**ar shi. Duk da irin matsananciyar azabar da s**a sha suda sauran musulman farko daga kafiran makka. Bai yi kauraba zuwa kasar habasha ba. Ya tare ga manzon allah (S. A. W) lokacin kaura zuwa madina yana tare da Annabi Muhammad (S. A. W), tare s**a shiga kogo kafin suwuce zuwa madina shine cukon mutane biyu da Allah ya ambata a alkur"ani in da yace : " Idan baku taimakeshiba. ( Annabi), to ai Allah ya taimake shi yayin da kafurai s**a fitar da shi ( daga makka) na biyu (mutane) biyu yayi das**a shiga cikin kogo yake cewa da abokin shi (Abubakar)" kada kaji tsoro, Mu Hakika Allah ya na tare damu "( da taimako shi)" cikin suratul tauba:40, yayin da s**a isa madina. Sayyida Abubakar, A wurin kharijatu dan zaidu. Da shi kuma manzon allah yahada su 'yan uwantaka yayi da ya rinka hada yan' uwantaka (ta musulunci) tsakanin mutane makka ( muhajiruna), da na madina (Ansaru) Sayyida Abubakar shine tamkar Waziri ga Annabi Muhammad (S. A. W), wajan gudanar da al'amuran daular musulunci. Mai babbar hedikwata a madina: birnin manzo,,,

Abubakar saddik ( R. A) ya dukkan yake _ yaken daukaka musulunci da yada shi da Annabi Muhammad (S. A. W) a yakin badar shine kan gaba wajan kula da wurin da manzon allah yake. Yana shir yanda yake zai gudana tare da rokon allah. har dai allah ya amsa addu'ar Annabi, ya aiko da rundunar mala"iku. Musulmai s**a samu nasara. A yakin uhudu kuwa, Sayyida Abubakar. Shine jagora tsirarun Manyan sahabbai, s**a gabata a filin yakin. Tare da manzon allah (S. A. W) yayin da kafurai s**a tarwatsa rundunar musulmai.
Allah Ne Masani.

Duniyar Musulunci Page

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Sharada Phase 1 Kano
Kano
700154