02/01/2026
WAYE NE Professor Isa Ali Pantami ?
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami mashahurin malami, masani a harkar fasahar sadarwa (ICT), masani a tsaron intanet (Cybersecurity), malamin addinin Musulunci, kuma tsohon Ministan Gwamnatin Tarayya ne a Najeriya.
๐ Haihuwa da Karatu
An haife shi a ranar 20 ga Oktoba, 1972 a Pantami, Jihar Gombe.
Ya yi karatun Computer Science a Jamiโar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), inda ya samu Digiri (B.Tech) da Digiri na biyu (MSc).
Ya kuma samu MBA a Technology Management.
Ya kammala Digirin Digirgir (PhD) a Computer Information Systems a Robert Gordon University, Scotland.
Ya halarci manyan kwasa-kwasai da horo a jamiโoโi irin su Harvard, MIT, Oxford da Cambridge.
๐ Aiki a Ilimi
Ya kasance Malami (Lecturer) a Jamiโar ATBU.
Ya yi aiki a Islamic University of Madinah.
A shekarar 2021, aka nada shi Farfesa a fannin Cybersecurity a Jamiโar Fasaha ta Tarayya, Owerri (FUTO).
๐ผ Aikin Gwamnati
A shekarar 2016, aka naษa shi Babban Darakta (DG/CEO) na NITDA, inda ya ฦarfafa dokoki da tsare-tsaren ICT a Najeriya.
Daga 2019 zuwa 2023, ya zama Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital.
A lokacin mulkinsa, ya jagoranci shirye-shiryen:
National Digital Economy Policy and Strategy (2020โ2030)
National Broadband Plan (2020โ2025)
Wadannan sun taimaka sosai wajen bunฦasa intanet da tattalin arzikin dijital a ฦasar.
๐ Matsayi a Duniya
Ya shugabanci World Summit on the Information Society (WSIS) a ฦarฦashin ITU a 2022.
Kungiyar African Union ta naษa shi Co-Chair na African Scientific Research and Innovation Council (AU-ASRIC).
Yana da fellowship a ฦungiyoyi masu daraja k**ar British Computer Society da Nigeria Computer Society.
๐ Addini da Alโumma
Farfesa Pantami shahararren malamin Musulunci ne kuma Babban Limamin Jumaโa, yana haษa ilimin zamani da koyarwar addini wajen wayar da kan alโumma.
โ ๏ธ Muhawara
A wasu lokuta, kalamansa na sun jawo muhawara a kafafen yaษa labarai.
Daga Alkalamin โ๏ธ
Asmau