20/04/2026
HUKUMAR NEMA TA SANAR DA BARAZANAR AMBALIYAR RUWA A 2026
A lokacin da Najeriya ke kusantar tsakiyar ruwan sama na 2026, tambaya mai muhimmanci ta sake tasowa: Shin za mu sake tsintar kan mu a tsakanin gargaɗin masana da jinkirin ɗaukar mataki?
Hasashen Ambaliyar Ruwa na Shekara ta 2026 ya zo da gargaɗi mai tsanani: An sanar da cewar fiye da al’umma 30,000 a duk ƙasar suna cikin haɗari. Daga cikinsu, mutane 14,118 a jihohi 33 da FCT suna cikin babban haɗari, mutane 15,597 na a cikin matsakaicin haɗari, yayin da 923 ke cikin ƙaramin haɗari.
Gidaje, hanyoyi da ƙananan masana'antu na iya rugujewa cikin ’yan kwanaki idan ba a dai mataki da wuri ba.
Ambaliyar ruwa a Najeriya ta zama matsala mai maimaituwa saboda sauyin yanayi da sakacin mutane: Daga cikin manyan dalilan akwai ƙarfin ruwan sama, ƙaruwar ruwa a koguna, saurin faɗaɗuwar birane, rashin magudanan ruwa da zubar da shara a ko ina.
Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙoƙarin da take yi wajen inganta ba da tallafin gaggawa. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da ƙoƙarin da su ke wajen haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa.
NEMA ta na taka muhimmiyar rawa. Ta mai da hankali kan saurin ankarar da al'umma a matakin farko, tare da haɗa gwiwa da hukumar NiMet da NIHSA. Ana wayar da kan jama’a game da ficewa daga wuraren da za su fuskantar haɗari, tare da tsaftace magudanan ruwa da kuma hanzarta sanar da hukumomi in an samu ambaliya.
Duk da haka, har yanzu akwai ƙalubale: Gargadi ba ya isa ga al’ummomi masu nisa, wasu kuma suna raina haɗari, ga kuma wasu jihohin ba sa himmatuwa wajen kiyaye dokoki.
Domin a rage illa, dole a:
- Tsaftace magudanar ruwa
- Tabbatar da dokokin tsarin birane
- Hana gina gidaje a filayen ambaliya
- Ƙarfafa shuke-shuke da ababen more rayuwa masu jurewa sauyin yanayi
Dole mu shirya yanzu domin kare rayukan mu da dukiyoyin mu.
Muhalli TV 📡 – Mu kare muhallin mu, mu kare kan mu.