Muhalli TV

Muhalli TV

Share

Duniya da Kewaye || Kimiyyar Muhalli 🌍

18/05/2026

KUNGIYAR HEDA TARE DA NIHSA SUN FARA WAYAR DA KAN JAMA'A GAME DA AMBALIYAR RUWA KAFIN DAMINA TA SHIGO

Kungiyoyin sun ce yin hasashen ambaliyar kaɗai ba ya isa, sai an haɗa da fassara shi ga al'umma yadda za su gane kuma su yi amfani da shi.

Kungiyoyin sun ce manoma ne s**a fi shan wahala daga ambaliya a kowace shekara, saboda haka ana shirya horo na kwanaki biyu (ranar Talata da Laraba) ta wayar tarho. Za a yi magana da Hausa, Yoruba, Igbo, Pidgin da Turanci.

An gayyaci manoma, shugabannin al'umma, 'yan jarida, da hukumomi su halarci domin su koyi yadda za su kare gonakinsu, dukiyoyinsu, da rayukansu kafin ambaliya ta zo.

Muhalli Tv

17/05/2026

WATA GAGARUMAR GIRGIZAR ƘASA MAI ƘARFIN 5.1 TA GIRGIZA TSAKIYAR TAIWAN

Hukumar Kula da Yanayi ta (CWA) a Taiwan ta bayar da rahoton cewa, wani gagarumin girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.1 ya afku a yankin Nantou da ke tsakiyar ƙasar.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:46 na safe (agogon wurin) a ranar Lahadi, 17 ga Mayu, 2026.

Muhimman Bayanai Game da Girgizar Ƙasar:

• Ƙarfi (Magnitude): Maki 5.1
• Wurin Da Ya Fi Shafa (Epicenter): Garin Puli da ke Yankin Nantou. Wannan wuri yana kimanin kilomita 33.5 a arewa maso gabashin babban birnin yankin na Nantou.
• Zurfin Ƙasa: Kilomita 15.5

Tasiri da Tsananin Girgizar Ƙasar:

Rahotanni sun nuna cewa tsananin girgizar kasar ya bambanta dangane da yankuna:

• Yankin Nantou: Anan ne girgizar ƙasar ta fi tsanani, inda ta kai maki 4 a ma’aunin tsananin girgizar ƙasa na Taiwan wanda yake da matakai 7.
• Taichung, Yankin Hualien, da Yankin Miaoli: A waɗannan yankunan, tsananin girgizar ƙasar ya kai maki 3.

Halin Da Ake Ciki Yanzu:

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani bayani na asarar rai, rauni, ko gagarumar barna da girgizar ƙasar ta haddasa.

Masana suna ci gaba da sanya ido kan lamarin don ganin ko za a sami ƙananan girgizar ƙasa (aftershocks) bayan wannan.

✓Ku tuntuɓi MUHALLI TV domin ƙarin labarai.

Muhalli TV - Labaran Yanayi da Muhalli ✓

16/05/2026

ZAFI MAI TSANANI YA NA NEMAN ZAMA RUWAN DARE A INDIA DA PAKISTAN

Wani sabon bincike ya nuna cewa zafi mai tsanani a Indiya da Pakistan ya zama ruwan dare, saboda canjin yanayi da mutane ke jawowa.

Yanayin zafin na kai wa sama da digiri 46 a ma'aunin selshiyos (Celsius), inda ya riga ya kashe mutane da dama. Talakawa, ma’aikatan waje, tsofaffi, da yara sun fi shan wahala.

Masana sun ce duk wani zafi da muke gani yanzu, ya fi na da da kusan 1C, kuma hakan na kawo hadari ga lafiyar miliyoyin mutane.

Muhalli Tv

16/05/2026

Ashe akwai ƙasar da ta ke da gine-ginen Pyramids ɗin da su ka fi na Masar (Egypt) yawa 😲

10/05/2026

Manyan Pyramids ɗin Misra kenan (The Great Pyramids of Giza): Khufu 🔺 (Na Sarki Khufu), da Khafre 🔺 (na ɗan sa Sarki Khafre), da Menkaure 🔺 (na jikan sa Menkaure)!

10/05/2026

Sirrin Ginin Pyramids 🔺 ɗin Giza: Shin Me Ne a Ciki, Kuma Su Nawa Ne? 🤔

゚viralシ

09/05/2026

To ko dai da Gaske ne cewar Aljanu ne su ka Gina Pyramids ɗin Ƙasar Masar (Egypt) 🤔

゚viralシ

27/04/2026

Shin ko kun san gini mafi nisa a duniya? 🤔

゚viralシ

20/04/2026

HUKUMAR NEMA TA SANAR DA BARAZANAR AMBALIYAR RUWA A 2026

A lokacin da Najeriya ke kusantar tsakiyar ruwan sama na 2026, tambaya mai muhimmanci ta sake tasowa: Shin za mu sake tsintar kan mu a tsakanin gargaɗin masana da jinkirin ɗaukar mataki?

Hasashen Ambaliyar Ruwa na Shekara ta 2026 ya zo da gargaɗi mai tsanani: An sanar da cewar fiye da al’umma 30,000 a duk ƙasar suna cikin haɗari. Daga cikinsu, mutane 14,118 a jihohi 33 da FCT suna cikin babban haɗari, mutane 15,597 na a cikin matsakaicin haɗari, yayin da 923 ke cikin ƙaramin haɗari.

Gidaje, hanyoyi da ƙananan masana'antu na iya rugujewa cikin ’yan kwanaki idan ba a dai mataki da wuri ba.

Ambaliyar ruwa a Najeriya ta zama matsala mai maimaituwa saboda sauyin yanayi da sakacin mutane: Daga cikin manyan dalilan akwai ƙarfin ruwan sama, ƙaruwar ruwa a koguna, saurin faɗaɗuwar birane, rashin magudanan ruwa da zubar da shara a ko ina.

Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙoƙarin da take yi wajen inganta ba da tallafin gaggawa. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da ƙoƙarin da su ke wajen haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa.

NEMA ta na taka muhimmiyar rawa. Ta mai da hankali kan saurin ankarar da al'umma a matakin farko, tare da haɗa gwiwa da hukumar NiMet da NIHSA. Ana wayar da kan jama’a game da ficewa daga wuraren da za su fuskantar haɗari, tare da tsaftace magudanan ruwa da kuma hanzarta sanar da hukumomi in an samu ambaliya.

Duk da haka, har yanzu akwai ƙalubale: Gargadi ba ya isa ga al’ummomi masu nisa, wasu kuma suna raina haɗari, ga kuma wasu jihohin ba sa himmatuwa wajen kiyaye dokoki.

Domin a rage illa, dole a:

- Tsaftace magudanar ruwa
- Tabbatar da dokokin tsarin birane
- Hana gina gidaje a filayen ambaliya
- Ƙarfafa shuke-shuke da ababen more rayuwa masu jurewa sauyin yanayi

Dole mu shirya yanzu domin kare rayukan mu da dukiyoyin mu.

Muhalli TV 📡 – Mu kare muhallin mu, mu kare kan mu.

19/04/2026

Shin ko kun san ina ne Fadar Sheɗan? 🤔

16/01/2026

Barka da safiya!
Wa ne kariya ku ke ba wa kan ku a wannan lokaci na sanyin hunturu?

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Kano