10/09/2025
ZADUZ-ZAUJAINI - 097
,عن عائشة رضي الله عنها قالت كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يخرج رأسه إلي، وهو معتكف، فأغسله، وأنا حائض
★ FASSARA
Daga Nana A'isha RA Tace;
"Manzon Allah SAW ya kasance yana fito mini da kansa (ta window) a gareni, Alhalin yana cikin i'itikafi, se na wanke masa shi, kuma ina cikin al'ada (Haila)."
🕋 Bukhari
🕋 Muslim
★ TRANSLATION
Narrated by Aisha RA;
During I‘tikaf, the Prophet ﷺ would extend his blessed head towards me (from the mosque), and while I was in the state of menstruation, I would wash his head.
🕋 Bukhari
🕋 Muslim
★ BAYANI
Annabi SAW Yana mikawa Nana A'isha RA kansa ta window na masallaci dake jikin dakinta sauran jikinsa kuma na cikin masallaci, kuma Annabi SAW yasan da tana cikin haila, se ta wanke masa shi kuma ta take masa shi da mataji, ta masa hidima kuma ta taɓa jinkinsa kuma yan i'itikafi.
★ FA'IDA
• Ya halatta me jinin haila ta taɓa mijinta
• idan wani sashi na jinki mutum ya fita daga Masallaci i'itikafin sa be lalace ba
• Koda ma se fita daga Masallaci indai don biyan bukata ce ta dan adam to babu laifi ya dawo yaci gaba da i'itikafin nashi kamar yadda wani hadisi ya nuna
• Masu haila jansu ajiki ake ba kyamatarsu ba kamar yadda yahudawa suke kyamar mace idan tana haila
• Mun fahimci Yadda mace Yakamata tana hidimtawa me gidanta ta hanyar wanke masa gashin kansa ko tajewa ko wani ko guga ko dafa masa abinci
• Mace me Haila ba najasa nace
Allah ne Mafi Sani