14/12/2022
QURUCIYA DA TSUFA......
Akwai wani lokaci can da muka je wani qauye a irin family house din nan na karkara Muna wani bangare a gidan Muna hira da Matan gidan, sai mu ka ji ana Kira a fito Malama tazo za a fara karatu sai Matan duk s**a fita s**a tafi wurin Malamar daukan karatu
Ina zaune sai yaro ya shigo wurin da nake, nake tambayar Shi WACECE malamar dake karatun
Sai yaron yace wata tsohuwa ce
Sai na tafi wurin masu karatun Don naji irin karatun nasu
Allah ya sani naje ne naji irin karatun nan na tsofaffin qauye da suke wa Mata na shirme
Hasbunallahu wani'imal wakeel wani irin shocking naji a jikina Yayin da naje wurin naga yanayin shekarun malamar da kuma irin karatun da take koya musu
Baiwar Allahn ta TSUFA sosai Don ko tafiya da Sanda take yi,
Sayyidil istigfar take koya musu, wasun Su kuma Addu'ar neman tsari daga shirka take koya musu,
Wallahi karatu ne cikin nutsuwa duk Wanda yayi kuskuren harafi sai ta gyara musu
bayan sun gama ta tafi nake tambayar wata cikin Matan game da malamar,
Take sanar Dani shekarun malamar sun haura a Dari, Amma baiwar Allah n tana cikin nutsuwa baza ka taba jingina Mata rikitar TSUFA ba
Mashaa Allahu da gani kasan akwai kyakkyawan zaton baiwar Allah n tayi kyakkyawar quruciya, Shi yasa tsufan ta ma yayi kyau
Haka na karanta cikin wani littafi mai suna MESSAGE TO EVERY YOUTH nasihohi masu ratsa zuciya GA Matasa Wanda har sai da na zubda hawaye, Mai littafin ya hakaito wani Labari acikin littafin yace wani matashi ya bashi labarin mahaifin sa ya Kai shekaru 120 a duniya, Amma yace sallar jam'i bata kubce masa, haka nan haqoran sa Ko guda daya bai fadi ba, haka idanuwan sa tas yake gani, haka kunnuwan lafiya lau yake ji, yace Amma game da quruciyar sa mutumin qwarai ne yana da kyakkyawar mu'amala Kuma yana damuwa da al'amuran addini sosai
Nasan kowanne matashi zai yi burin Idan Allah ya qaddaro masa shekaru masu yawa a rayuwar sa to ya samu kyakkyawan tsufa,
Shi kuma kyakkyawan tsufa yana biyo bayan kyakkyawar quruciya ne