A.Y Dorayi Global Concept

A.Y Dorayi Global Concept

Share

Dirasatul Islamiyya Wattahfizul Qur'an

25/03/2025

Amnesty ta yi Alla-wadai da tsare 'yan jarida biyu a Kano bisa umurnin kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Kano

Mai Yasa Gwamnatin Kano Ta Abba Gida-Gida Dake K**a Karya Tare Da Kokarin Nuna Karfi Tuwo Kan Wasu Abubuwa A Jihar?

25/03/2025

Daga Nan Sarari 24 Muna Allah Wadai Da K**a "Yan Jaridu Guda Biyu Da Gwamnatin Jihar Kano Tai.

Akarshe Muna Kira Da'a Gaggauta Sakinsu Tare Da Basu Kulawa.

25/03/2025

Gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers ya nada sabon SSG, yayin da Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar ya yi murabus daga mukaminsa

Vice Admiral Ibas Ibok-Ete Gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers ya sanar da nadin Prof. Ibibia Worika, a matsayin sabon Sakataren gwamnatin jihar.

Kazalika, Mr Ibas ya sanar da nadin Iyingi Brown babban Sakatare a ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da zai yi rikon kwarya a kujerar shugaban ma'aikata.

DCL Hausa

24/03/2025

Zaman 'Dar-'Dar A Jihar Kano

Tun Bayan Kuratowar watan sallah a jihar kano dake arewacin Najeriya aka shiga zulumi kan dorewar zaman lafiya, hakan yabiyo bayan Sanarwar hawan Sallah da dakataccen sarki da kotu ta tsayar Sunusi Lamido Sunusi Yayi a wani taron shan ruwa daya guda da Gwamnanan Kano. Kwanaki kadan kuma sai wata sanarwar itama ta kara fita daga wanda yai nasara a kotu wato Aminu Ado Bayero lamarin daya saka shakku da gudun barkewar Fitina a lokutan na bukukuwan na sallah.

Har zuwa wannan Lokaci dai babu wata sanarwa ko Karin bayani daga Jami'an Tsaro ko Gwamnatin Kanon.

23/03/2025

Majalisar Dattawan Kasar Bata Samu Adadin Yan Majalisun Da Ake Buƙata Ba, Wajen Amincewa Da Dokar Ta Bacin Da Shugaba Bola Tinubu Yasa A Ribas Ba.

Tsohon Gwamnan Sokoto, Kuma Sanata Ayanzu Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ce
Majalisar Dattawan ƙasar ba ta samu adadin ƴan majalisun da ake buƙata ba, wajen amincewa da dokar ta bacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya a Jihar Rivers.
Tambawal ya shaidawa Jaridar The Sun cewar, adadin ƴan majalisun da s**a halarci zaman ba su kai 73 ba, daga cikin 109 da ake da su. Saboda haka Sanatan ya ce matakin da majalisar ta dauka ya sabawa sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya. Wasu ƴan majalisar da kuma masu sanya ido na ci gaba da korafi akan hanyar da aka bi wajen amincewa da saka dokar musamman hana ƴan majalisun kaɗa kuri'a ɗaya bayan ɗaya. Tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jinjinawa Majalisun ƙasar guda biyu saboda goyan bayan kudirin da ya gabatar musu kan Jihar Ta Ribas.

22/03/2025

Kubayyana Kadarorin Da Kuka Mallaka Cikin Kankanin Lokaci

Gwamnan Kano Engr. Alh. Abba Kabir Yusuf Ya umurci waɗanda ya nada a mukamai da su ayyana yawan kadarorin da s**a mallaka batare da jinkiri ba.

22/03/2025

Duk Kugama Hadakar Ku 2027 Bazaku Iya Kada APC A Kasa Ba: Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Tsohon Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal. Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haɗakar ‘yan siyasa da za ta iya sauke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Matsayar Shekarau na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, s**a soki matsayar Gwamnatin Tarayya game da rikicin siyasa a Jihar Ribas a wani taron manema labarai da s**a gudanar a Abuja.

A wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar a madadin Shekarau, ya jaddada cewa, sabanin abin da wasu ke hasashe, wannan haɗaka kawai wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa, kuma babu wanda daga cikin jagororin wannan haɗaka da ya tuntubi shugabancin jam’iyyarsa.

Sanatan ya bayyana haɗakar a matsayin wata hadin guiwa ta wasu gungun mutane kawai, yana mai cewa, ko da suna da manyan sunaye, hakan ba ya nufin sun haɗe wuri guda domin zama jam’iyya guda ba.

A cewarsa, “Haɗakar wasu manyan jiga-jigai daga jam’iyyun adawa abu ne mai kyau, kamar yadda aka gani kwanan nan a ƙarƙashin abin da suke kira ‘coalition’ na jam’iyyun adawa.

“Babu ɗaya daga cikin manyan jagororin da ke tafe da shugabancin jam’iyyarsa. Kuma wannan taron wasu gungun mutane, duk da suna da manyan sunaye, ba za a kira shi ‘merger’ ba, domin a bisa doka, sai jam’iyyun da aka rijista ne kawai za su iya yin cikakken haɗaka.”hekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haɗakar ‘yan siyasa da za ta iya sauke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Matsayar Shekarau na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, s**a soki matsayar Gwamnatin Tarayya game da rikicin siyasa a Jihar Ribas a wani taron manema labarai da s**a gudanar a Abuja.

A wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar a madadin Shekarau, ya jaddada cewa, sabanin abin da wasu ke hasashe, wannan haɗaka kawai wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa, kuma babu wanda daga cikin jagororin wannan haɗaka da ya tuntubi shugabancin jam’iyyarsa.

Sanatan ya bayyana haɗakar a matsayin wata hadin guiwa ta wasu gungun mutane kawai, yana mai cewa, ko da suna da manyan sunaye, hakan ba ya nufin sun haɗe wuri guda domin zama jam’iyya guda ba.

A cewarsa, “Haɗakar wasu manyan jiga-jigai daga jam’iyyun adawa abu ne mai kyau, kamar yadda aka gani kwanan nan a ƙarƙashin abin da suke kira ‘coalition’ na jam’iyyun adawa a kasar.

19/03/2025

Sam Sam Abu bai dadi ba

Agaggauce: Matasa Sun Kone Rugagen Fulani A Zamfara

Labaran Da Muke Samu Cikin Wannan Dare Daga Jihar Zamfara:
Yanzu cikin daren nan matasa daga unguwar Galadunci dake garin Anka ta jihar Zamfara, sun tsallaka wani yanki inda bukkokin fulani suke nan take s**a cinna musu wuta sun kone inda duka rugagen s**a kone kurmus.

19/03/2025

DA DUMI-DUMI: Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero Zai Gabatar da Hawan Sallah a Birnin Kano.

Wata majiya daga masarautar Kano tace mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya tabbatar da cewa masarautar na shirye-shiryen hawan bukukuwan Sallah karama, kamar yadda al'ada ta tanada

19/03/2025

Babbar Jam'iyyar Hamayya A Najeriya PDP Taki Amincewa Da Matakin Da Shugaba Tinibu Yadauka Akan Jihar Ribas

Inda tace Tinubu ba shi da ikon dakatar da Gwamna a dokar kasa

18/03/2025

Kuma fa haka ne

Abun Kunya Yaqarewa Tinibu- Atiku Abubakar

Tinubu ya aikata abin kunya wajen hukunta mutanen jihar Rivers ta hanyar kakaba musu dokar ta baci domin biyan bukatarsa da wadanda ke juya shi in ji madugun adawar Nijeriya Atiku Abubakar.

Dan siyasar ya zargi Tinubu da gaza daukar matakan da s**a dace don dakile takaddamar da ta kai ga daukar wannan mataki da ya ce da wata boyayyar manufa aka yi shi

Photos from PCM's post 18/03/2025
Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Dorayi Karshe Layin Karshe
Kano