Al'adun Hausawa a Da,da Yanzu.

Al'adun Hausawa a Da,da Yanzu.

Share

AN BUDE WANNAN SHAFI NE,SABODA TUNATAR DA KAWUKAN MU
BISA KYAWAWAN AL'ADUMMU NA HAUSA,

WADAN DA AYA Mungode

Dan Bunkasa Harshen Hausa da Al'adunsa,
Muna Maraba da shawarwarinku Domin wannan shafi naku ne.

12/06/2026

Idan baka yarda ba ka gwada.

12/06/2026

MACE MUTUM CE!(4)

Ci gaba kuma na karshe...

."Ba zai yiwu ba ka samu mutum da idanunsa biyu yana gani,ka ce masa...Kai..yanzu kai makaho ne,kuma kace dole sai ya yarda,kuma duk abinda zai fada ba abin kamawa bane,kawai dole ya hakura shi tunda ance baya gani to ya yarda kawai baya gani,...wannan ganin kuma ya sawa ransa cewa,sunansa makanta,..anya haka zai yiwu?

Kamar haka Al'umma su ka dauki mace,da iyawarta da kwarewarta da tunaninta da duk wata baiwa da Allah ya yi mata banza ne kawai, hujja ita mace ce.Wannan ba karamin zalunci bane.

BAMBANCIN KWAKWALWAR MACE DA TA NAMIJI TUN A YARINTA.

Idan ka tambayi mutane game da yayansu da su ke haifowa,ka tambaye su idan aka samu mace mai lafiyayyen tunani da namiji mai lafiyayyen tunani,za ka ga idan suna yara macen ta fi basira da gane abubuwa...amma tambaya..me ya sa namijin yake zama shine mai basira fiye da macen idan tafiya ta yi tafiya?

Dalili shine....su kansu iyaye suna sawwala idan su ka haifo mace ba komai bace namijin nan dai shine wata tsiya,haka za a rika gwasale mace duk abinda zata yi ana gaya mata ita macece,ba za ta iya ba sai maza,

Shi kuma namijin ana karfafarsa ana ce masa shi namiji ne zai iya yin kaza da kaza,wato tun a farko uwa da uba su ke kashe zuciyar yarsu mace..a duniyar hausawa kuwa tun tana zanin goyo ake fara gaya mata,amfaninta kawai a wannan duniyar shine..ta yi girki a ci,ta haifi yaya shikenan bata da wani cigaba da zata samarwa a al'umma,kuma ba'a da wani fata akanta wanda ya wuce ta girma ta yi aure.

Al'umar da ta ci gaba tana sanya mace a matsayi na gaba wajen gina Al'umma,shi yasa duk wasu abubuwa masu alaka da kwakwalwa ana barwa mata ne su, su ka san yadda ake gina dan'adam,...Misali...makarantu da yawa mata ne ke koyarwa,idan ma akwai maza zaka samu kadan ne a duniyar da aka ci gaba.

Anan suna nufin gina al'umma sai mata,tunda aka dauki abinda ya shafi ilimi aka mikawa mata shi,sannan da yawan mutanen da s**a zama wasu a kwakwalwa za ka samu iyayensu mata ne s**a basu gudunmawa 100%.

KISSAR IMAM ALI AS DA MU'AWIYA.

Ya zo a sira ta Imam Ali as cewa...
Mu'awiya ya taba aikawa Imam Ali as cewa,..dole Imam Ali aa ya zo ya yi masa bai'a,idan kuma ya ki zuwa,shi Mu'awiya zai turo masa mazaje masu zuciyar zakuna.

Sai Imam Ali as ya ce..ba zai masa bai'aba..kuma yana jiran zuwan wadannan mazajen masu zuciyar zakuna..zai hadasu da mazaje masu zuciyar mata.

Wannan Maganar ta shugaban balaga da hikma ta sa duniya ta shiga tunani,shin zuciyar mace yaya ta ke?

INA MATSALAR TA KE?

Dole mu yi nazari muga a ina muka samu wannan matsalar mai dogon tarihi,domin warwareta da abubuwan da su ke na zahiri.

Tabbas mata suna da rauni musamman rauni kala biyu,..

Akwai na halitta wanda Allah ne ya halicce su a haka,idan mu ka ce sai mun sauya su daga wannan dabi'ar zuwa tamu abu ne da ba zai yiwu ba...Misali,..sauya halittarsu ta rashin kuzari zuwa kuzari..tausayi zuwa rashin tausayi,..salo na jiki da ya ke banbance mace da namiji...

Tabbas duka wannan ba muna cewa ba zai yiwu bane gaba daya,ana iya yi amma natijar da za a samu za'aga ta yi muni sosai.

Akwai Dabi'ar da dora msu ita aka yi,wadda ita ce mu ke so a yaka,a sauyata...Misali...

Dakusar da tunanun mace,da nuna mata ita kamar Robot ta ke bama a so ta rika tunani,illa iyaka duk abinda aka gaya mata kawai ta bi.

Nuna mata ita bata da wani amfani da ya wuce haihuwa da tsaron gida da duk wasu ayyuka da su ka shafi cikin gida.

A bangaren hausawa,an sanya musu wani tsoro da aka kirkiro shi,daga mace ta fara ganin alamomin girma a tare da ita,hankalinta zai koma zancen gidan miji,an kayyade wasu shekaru da ake ganin idan ta wuce su bata yi aure ba rayuwarta ta shiga hatsari,sabida haka ko karatu take a lokacin tunaninta ya rabu biyu ne,fargabar samun miji sannan shi karatun bata san me ake yi da shi ba,dukda wasu suna dauka ana karatun ne dan sana'a,wanda alokacin ne ya kamata a da mata tunanin cewa,ita wata al'umma ce da duniya ke jira ta karaso wannan wurin domin amfanar mutane,sabida haka sai ya zama tunaninta wane amfani za ta yiwa al'umar da ta ke ciki?.

Sai ya zama wannan shine tunaninta,shi kuma aure ya zama wani abu ne na kamala wanda zai karfafeta zuwa cimma wancan burin,wato ta gane ba iya aure bane kawai amfaninta ga al'umma.

Sanya musu jin cewa,su bayi ne ko a gidan mijinsu,kuma shi gidan mijin tamkar kurkuku ya ke idan ka shiga kawai sai yadda miji ya fasalta maka rayuwa,duk ilimin da mace ta karanta yana aiki ne a waje,idan ta zo gida miji ne zai zabar mata cewa,..wannan shine ilimi wannan ba ilimi bane,wannan shine daidai wannan ba daidai ba..wannan fa ko da kasurgumin jahili ta aura shikenan zai zamar da ita irinsa,ba mu ce kada a yi wa miji biyayya ba,ko shi miji ya saki matarsa a t**i kamar kazar hausa,a'a,...Muna cewa a duba aga wace gudunmawa za su baiwa al'umma sai a karfafe su,idan aka yi hakan za a ga tasirinsa har a yayanda za a haifa.

Anan yana da kyau su maza su sani,sau da yawa suna rusa rayuwarsu ne da kansu ta hanyar daqile tunnin matansu wanda kuma wannan natijar na komawa kan yayansu.

TASIRIN IYAYE MATA A RAYUWAR YAYANSU.

Manazarta sun gano cewa,..Matan da aka fi basu dama da girmamawa tun daga tasowarsu a yarinta har zuwa gidanje aure,sun fi samar da yaya nagartattu masu hazaqa da tarbiyya kuma sun fi gane karatu ko a makaranta,sabanin matan da su ke rayuwa cikin kunci tun suna yarinta ,shi kuma kuncin nan babu kuncin da ya kai da iliminka da tunaninka a mayar da kai baka san komai ba,duk abinda ka ke ji a kwakwalwarka ba'a yarda da shi ba.

..."Za mu kawo cikakken bayani a rubutunmu mai taken..
HANYOYIN DA ZA KU GINA TUNANIN YAYANKU.

Haka nan macen da ta samu kulawa da nutsuwa da girmamawa tsufa baya kamata da wuri.

Sannan gwargwadon yadda ka baiwa mace dama a matsayinta na Mutum ,kai kanka mijinta za ka fi samun kulawar da ya kamata.

Sannan kuma ana samun soyayyar yaya ga iyayensu maza da su ke girmama iyayensu mata,saboda duk wannan yanayin da ka tafiyar da mace akai yana tasiri a kwakwalwar yaran da ta haifa tun daga ciki.

KARKAREWA.

Wannan rubutun yana kira ne ga al'umar da ta dauki mace tamkar ba mutum ba,ta yi mata matsaya cewa,bata da wani amfani daga aikace-aikacen gida sai haihuwar yara cewa,su sauya tunani yanzu duniya ta ci gaba ta gano cewa,MACE MUTUM CE,duk inda ka ke son ci gaba idan ka dora mace a wurin za a kai nasara matukar bai saba da asalinta na yadda Allah ya ajiyeta Mace ba.

Muna fatan Allah ya sa mu amfana da dan abinda muka ambata.

Nagode

Shareef Muhsan Bachirawa
08034318311
25/05/2026

12/06/2026

Fadima as

12/06/2026

ABUBUWA 50 DA YA KAMATA IYAYE SU LURA DA SU,DOMIN HANA YAYANSU FADAWA ZINACE-ZINACE.(5)

Ci gaba...kuma na karshe.

31. SANAR DA YARA HUKUNCE-HUKUNCEN SHARI'A.

Yana da kyau yara su zama tun daga tasowarsu za afara sanar da su Hukunce-Hukuncen shari'a musamman abinda ya shafi mu'amala tsakanin mace da namiji kai da dukkan ibada tun kafin su balaga.

Da yawan 'ya'ya suna jin labarin hukunci ne daga wani waje ba daga wajen iyayensu ba,wani lokaci su kan ji kamar shi hukuncin ra'ayi ne,mutum ne ya ke ji a jikinsa da kansa a cikin zuciyarsa sai kuma ya raya cewa a wajen Allah ma haka lamari yake,Misali:

Akwai da yawan yaya da su ka dauka sanya sutura bashi da hukunci a addini,kawai yadda kaga dama za ka saka kayanka koda akwai tabarruji,ko kuma cudanya tsakanin maza da mata, suna dauka wayewa ne,idan kan mutum ya waye sai ya yi yadda ya ga dama,idan baka waye ba ka barshi,kuma gwargwadon wayewarka gwargwadon yadda za ka sarrafa rayuwarka.

Saboda haka yara su su ke zabarwa kansu yadda za su cudanya da juna kuma duk abinda s**a ga dama su yi.
To amma idan aka sanar da su hukunci zai taimaka wajen rashin ketare iyaka.

32/33 HALASTAWA JUNA SHIGA GIDAJEN JUNA,'YAYA DA IYAYE.

a. Zaka samu abokai sun taso su da kansu sun halastawa kansu shiga gidajen juna,suna ganin kamar wata wayewa ce.
Aboki zai keta kofar gidan abokinsa kai tsaye kuma ya zarce ya daga labulen daki,a wasu lokuta suna tarar da matan abokansu a tsakar gida cikin kowane irin yanayi kuma ba su damu ba.wani har cikin daki zai daga labule yana yiwa matar abokinsa magana ba tare da tunanin a wane hali take ba.kuma ko akwance take ko a zaune zai ci gaba da magana da ita tana mayar masa.
Akwai abubuwa da yawa akarkashin wannan kuma babu bukatar ambata su saboda gudun tsawaitawa saidai mu ce Allah ya kiyashemu.

b. Wasanni tsakanin aboki da matan aboki,..

Wa su suna dauka wayewa ce idan kai abokina ne to matarka ma kawata ce,koda kuwa baya shiga gidan,za ka samu ana wasanni na yasar da magana da barkwanci harda ba'a.

Ka ji abokin miji yana yiwa matar abokinsa ba'a yana ambata siffofinta,....Ta yi kiba ko ta rame itama cikin jin dadi tana mayar masa da magana,shima wannan a karkashinsa akwai bayanai sai dai a yi shiru kawai.

34. HALARTAWA YARAN DA BA NAKA BA SHIGA GIDANKA.

Daga cikin irin wadannan hukuncin shine,..

Za ka samu mutum a unguwa saboda an haifi yara a gabansa sun taso a gabansa saboda haka ya halasta musu shiga gidansa bayan sun balaga,alokaci guda ga yayansa mata watakil ma shi kansa yana da amarya yarinya,sai ya dauka duka yayansa ne kuma ita uwarsu ce ba anan muna nufin shekarun mce bane ya ke sa a hana samarin da ba muharramai ba shiga cikin gida,..aa indai sun kai baligai tunda ba su s**a haifi yayanba,to bai halasta su rika gani a kowane irin yanayi ba,..ko kuma a raina shekarunsu,suna shiga har cikin daki su bata lokaci.

Haka duk macen da tazo hidan koda sa'arsu ce aka auro, za ka samu yadda aka dama haka take sha,ta mayar da su ba samari ba,ta rufe idonta dukda wata banbancin shekarunsu da nata kadan ne,amma sai ta kiyasta a zuciyarta ita uwa ce, haka zaka ga basa kunyar zama da kowace irin shiga ko cudanya,saboda tana rayawa azuciyarta yara ne alhalin sun baiwa shekaru 15 baya,..idan ke bakya jin wani abu zai yiwu shi ya ji,b***e kuma dukkanku halittane ta dan'adam.
Abubuwa da yawa sun sha faruwa sakamakon irin wannan sakacin,su kansu yaran suna ganin daidai ne hakan.

Alokaci guda wanda ya tsaurara tsaro a gidansa ya kiyaye shari'a yaran suna kallonshi dan kauye,su sa masa suna ta zagi da habaici,suma iyaye mata suna ganin mai gidan ya cika tsaurarawa,baya kallon tare aka tashi ko kuma abokan yayansa ne.

Illolin da ke cikin barin irin wannan barnar na faruwa suna da yawa,daga ciki ana samu, su kansu iyayen mata wadanda su ka kasa fin karfin zuciyarsu,wasu kuma yayan makota da makota anan ake samun matsalar,domin yayanka mata ba muharraman yayan abokinka maza bane,Allah bai sanya su Muharramai ba saboda abota.

Anan za mu ce yana da kyau iyaye su karanta hukunce-hukuncen shari'a na muharramai da wadanda ba muharramai ba.

35. 'YAYAN RUKO

Da yawa suna daukar yayan ruko na dangi a matsayin 'ya'ya wai dan sun tashi a gidansu,sai kaga garjejen kato yana ratsa yanmata a cikin gida saboda a gidan ya tashi ana ganinsa tamakar dan gida.

Ko kuma akwai yarinyar da ake ruko,su kuma samarin gidan na mu'amala da ita tamkara muharramarsu,saboda suna kaddara agidan ta tashi,suma iyaye sun kawar da kai ta ya ya 'ya'ya za su san hukunci?.

Ko kuma yaro ne agola ko mace ce agola,sai ya zama ana mu'amalantar juna kamar wadanda aka fito ciki daya.

Da farko dole Uba ya sani cewa,
Dan ya auro mace da 'yarta agola,idan ta kai munzalin shari'a haramun ne yayansa na cikinsa su ganta ba hijabi,haka shima idan ďa ne agola ya girma agidanka,bai halasta ba ya rika keta matanka da yayanka ba tare da suna sanye da hijabi ba.

Wannan yana cikin abubuwa masu tsauri da ake kawar da kai ana ganin kamar Allah ma ya kawar da kai.

36. GINA RAYUWAR YARA DA IBADA

Wannan shine al'amari mai muhimmanci gina yaranka bisa ibada tun suna kananu.

Wannan yana taimakawa su tashi masu tsoron Allah ko baka kusa sunsan kana da wakili shine Allah,sun san yana ganinsu a kan duk abinda ka koyar da su.

a. Koya musu sallolin dare.
b. Azumin nafila tun suna yara kuma anuna musu akwai lada mai yawa da ake samu da kuma kusanci da ubangiji.

.."Mu lura da wani abu..
Yara sun fi manya tsoron Allah gwargwadon yadda aka rene su,shi babba idan ya girma ya yi wayo yana sanin wasu hukunce hukunce da za su sa ya iya taka doka sabanin yaro.

To idan yaro ya saba da kiyaye dokokin Allah,to mai sauki ne idan iyaye su ka gina tarbiyya yaro ya zama ya kiyaye ta.

c. Shagaltar da yara da karatun Alqur'ani da adduoi.
Ko kalle-kalle za su yi a sabarwa da zuciyarsu son kallon abu mai alaka da addini.

Gina ziciyar yaro da bin Allah tun yana karami tafi sauki akan ya zama matashi.
Ku daina cewa ba za ku koyawa yayanku kiyaye shari'aba sai sun zama baligai lallai kuskure ne.

Ya halasta yaro karami a rika tashinsa ana sallolin dare tare da shi..za mu kawo yadda ake saka yara barci idan ana so su yi barci,da yadda ake tashinsu cikin hikma a rubutun da muke yi mai taken ...HANYOYIN DA ZA KU GINA TUNANIN YAYANKU.

Anan wurin za mu dakata haka..
Sauran hanyoyin na 37.....zuwa 50 za ku same su a cikin littafi kammalalle wanda ake yunkirin mayar da wannan shawarwarin littafi dan karami da kowa zai iya mallaka kuma ya amfane shi da yayansa kamar yadda mutane su ke ta bayar da shawara.

Insha'Allah yana nan fitowa tare da adduoinku masu Albarka.

Wasslam

Shareef Muhsan Bachirawa
08034318311
12/jun/2026

24/05/2026

MACE MUTUM CE!(3)

Ci gaba...

Kamar yadda muka kawo cewa,..

Kallon mace a ba wata tsiya ba kuma bata da wata kima dadadden lamari ne da ya shahara tun kafin zuwan musulunci,akwai al'umar da su ke rayuwa suna sanya mata acikin kayan gado,misali mutum zai iya gadar matan babansa ciki harda mahaifiyarsa idan ya mutu.

Akwai Al'umar da su ka rayu,Idan mazajensu sun mutu saidai a hada su da matansu a bizne su,kuma wannan mace bata da zabi,tana ji tana kallo tana kuka haka za ta kwanta kusa da mataccen mijinta a bizne su,kuma har yanzu akwai irin wannan al'umar suna rayuwa a haka,amma idan ita ce ta mutu shi zai iya sake auren wata.

Bari na dan hakaito mana wata kissa da ta faru wadda Allah Subhanhu wa ta'ala ya kawo ta acikin Alqur'ani.

Ya zo a sira cewa,..Ita Mahaifiyar Sayyada Maryam as ta yi bakance ga Allah cewa..ta na so ya ba ta da namiji da za ta sanya shi mai yin hidma a baitul muqddas,watakil share-share da gyarawa masu ibada takalma idan sun ajiye wanda ta ke kallon wannan a wata sadaukarwa ga ubangiji.

Bayan ta haifi sayyada Maryam sai ta ji a zuciyarta cewa bata samu abinda ta ke bukata ba,domin Mace ta haifa.

Sai ta ke gayawa Allah cewa...Ya Ubangiji ka ga alkawarin da na yi maka da irin burina na samar da wani Da namiji da zai zama mai hidma ga masu ibada,har ka ce ka amsa min,amma yanzu na haihu sai na ga na haifo mace,me hakan ya ke nufi?.

Sai Allah ya ce mata kada ki damu Namiji bai kai mace ba..kamar muce Allah ya raba rigimar tun anan idan ana da tunani,Allah da kansa yace Namiji bai kai mace ba,amma Allah bai bar abin haka ba saida ya nuna wata aya da har zuwa yau din nan ba wani namiji da ya samu wannan matsayin,ayar kuwa ita ce.

Lokacin da sayyada Maryam as ta kai kololuwa wajen ibada,sai Allah ya ce da ita,...Ya ke Maryam..yanzu za ki iya shiga masallaci ki hada sahu da maza a yi ibada tare da ke ki yi sujuda atsakiyarsu ma'ana ki yi sujuda ki yi ruku'u duk tare da su..Tambaya....shin akwai wani Namiji da Allah ya taba cewa..yanzu ka shiga tsakiyar mata ka yi ibada tare da su ana gogayyar jikin juna?

Wannan yana nuna mana irin karfin ruhin da 'Ya mace ke da shi wanda ya ke kaita ga musharaka da maza ba tare da taraddudin za'a samu matsala a Imaninsu ba.

Wannan yana nuna mana yadda kowace Al'umma take da ilimin cewa,ko Malami ne ake so ya lalace to a hada shi da mace saboda su maza ba su da irin wannan tsarkin ruhin..shi yasa Azzaluman mahukunta da su ka rayu da Imamai as su ma su sun yi kokarin gwada Imamai as ta hanyar hada su waje daya da mace a kurkuku dan aga yadda zata kaya,wanda Allah da ikonsa babu wani Imami da aka yi galaba akansa saboda tsarkinsa,..dalilin kawo wannan shine....ku san kowace Al'umma sun yanke hukuncin ba wani Namiji da zai iya tsallake cudanya da mace ba tare da ya halaka ba,alokaci guda kuma ga macen da Allah ya bata wannan girman.

Ya zo a tarihi kafin zuwan musulunci har zuwan musulunci larabawa idan aka haifa musu mace suna bizneta ko su tafi da ita bayan gari su kasheta su jefar,..idan aka gayawa mutum an haifar masa mace sai ya qwansare fuska fuskarsa ta yi ja saboda an haifo masa tashin hankali....

Wannan fa duk muna so mu nuna yadda maza su ka taso ne tun asali da jin cewa mace ba komai bace,su maza sune halitta mai girma da dara.

YADDA MANZON ALLAH SAWW YA SAUYA TUNANIN AL'UMMA AKAN MACE.

Yana daga cikin abinda ya sauya tunanin al'umma irin yadda manzon Allah saww ya sauya fasalin yadda ake kallon mace.

Kada mu dauka akan Sayyada Fatima as manzon Allah ya fara sauya wa duniya tunani,lallai ya aikata hakan har a abokansa na kiwo yadda ya ke girmama su suna yara,har zuwa sayyada Khadiji da ta zama matarsa,ta yadda ya ke mikewa tsaye idan ya ganta kuma ya ke mata magana da gurmamawa kai wannan falalar saida ta shafi kawayen sayyada Khadija wanda ba tarihin muke so mu kawo gaba daya ba,muna tunawa kawukanmu ne cewa,tuni manzon Allah saww ya yaki wannan tunanin.

Manzon Allah saww ya buga samfur da sayyada Fatima as yadda itama ya ke girmamata,..Ance wani sahabi ya ga manzon Allah saww ya sumbaci wiyan sayyada Fatima as sai ya ke cewa manzon Allah ...Macen ka ke yiwa haka?...Sai mazon Allah saww ya ce masa..shin kai baka aikata haka akan yarka?..sai ya ce Eh..a take manzon Allah ya sauya fuska kuma ya umarce shi da ya rika aikatawa yayansa mata hakan.

WATAKIL YADDA NAMIJI KE KALLON MACE A BA KOMAI BA SHINE YA HADDASA MATSALOLI DA YAWA NA ZAMANRAKEWAR AURE.

Wato idan za mu kawo tarihin Al'umma ne game da yadda su ke kallon mace lallai za ku gazgata cewa,wannan kallon zai iya yiwuwa shine ya sabbaba matsaloli da yawa na zamantakewa.

Za mu ci gaba Insha'Allah
Shareef Muhsan Bachirawa
08034318311
24/05/2026

12/05/2026

HEADMASTER NA FARKO A AREWACIN NAJERIYA...

Shin kunsan wanene Magajin Gari Muhammadu Sambo ?

Marigayi Magajin Gari Sambo: Shine wanda ya kirkiri Kaduna ta Zamani, Malamin Farko ɗan Asalin Arewa, kuma Jagoran Ƙungiyar Turawan Birtaniya da ta Gudanar da Ƙirga Mutane (Ƙdaya) ta Farko a Arewacin Najeriya a 1923.

Labarin Muhammadu Aminu Sambo labari ne na jajircewa, sadaukarwa, Nagarta adalci da jagoranci. An haife shi a shekara ta 1888 a Zariya, daga babban gida mai daraja, zuriyarsa tana komawa Gidan Mal Tajo, ɗan Malam Musa Bamalli, wanda shi ne mai ɗaukar tutar Shehu Usman Ɗan Fodio, kuma wanda ya kafa gidan sarautar na Mallawa a masarautar Zazzau.

Tunaninsa ga ilimi ya bayyana tun yana ƙarami. Bayan ya kware a karatun Alƙur’ani, sai ya zama ɗaya daga cikin ‘yan Arewa na farko da s**a rungumi ilimin Turawa (ilimin boko) wani mataki mai ƙarfin da ya sauya rayuwarsa da ta al’ummarsa baki ɗaya.

Hanyarsa ta ilimi ta fara ne a shekara ta 1903 a Makarantar Kano Provincial School, inda yake ɗalibi na takwas da aka rubuta a rajista. Daga 1903 zuwa 1908, ya shimfiɗa tubalin sadaukar da rayuwarsa ga neman ilimi da wayewa.

A 1910, ya zama Malami mai kula (Headmaster) ɗan asalin ƙasa na farko a Makarantar Zariya Provincial School (wanda yanzu ake kira Alhudahuda College). Wannan nasara ta nuna irin jajircewarsa wajen ci gaban ilimi. A 1912, aka naɗa shi Headmaster na farko a Makarantar Bauchi Middle School (wacce daga baya aka sani da Sambo College of Education). A nan ne ya koyar da ilimi tare da karfafa tunani mai zurfi da neman ilimi.

A 1916, aikinsa ya ɗauki sabon salo lokacin da Sarkin Zazzau Aliyu Ɗan Sidi ya naɗa shi Wamban Zazzau kuma Hakimin Jaji. A wannan Lokacin ya fara gina wani gidan baki (guest house) wanda daga baya ya zama Command and Staff College Jaji, babbar cibiyar soja a Najeriya.

Sai dai a 1920, Sarkin Zazzau Dalhatu ya kwace masa sarauta, amma bai fid da rai ba. A 1923, a sake karramashi a lokacin da aka zaɓe shi ya jagoranci ƙungiyar Turawan Birtaniya da s**a gudanar da ƙirga mutane ta farko (Ƙidaya) a Arewacin Najeriya. Sakamakon haka, Sarkin Ingila, Sarki George, ya ba shi takardar yabo (Certificate of Honor) a 1924.

A 1925, aka dawo da shi sarautar Hakimci tare da bashi kuma ba shi Hakimi mai kula da Sabon Gari Zariya. Ya taka muhimmiyar rawa wajen gina Sabon Gari, Zariya, inda ya kafa makarantar firamare, da kuma haifar da sabbin unguwanni irin su Muchia da Dogon Bauchi daga 1927 zuwa 1930.

A 1937, tasirinsa ya bazu zuwa Kaduna, inda aka ba shi sarautar Magajin Garin Zazzau a lokacin Sarkin Zazzau Ja’afaru Ɗan Isiyaku.

A zamaninsa, Kaduna ta samu ci gaba sosai — an raya Tudun Wada, Unguwan Shanu, da wasu unguwanni. A 1943, ya fara shirin dasa itatuwa wanda ya kyautata kyawun gari, sannan ya ƙirƙiri lambar gidaje ta haruffa da lambobi (alpha-numeric house numbering), wanda ya taimaka wajen tsara gari da gyara harkokin gine-gine.

A 1956, ya kafa tarihi na zama mutumin farko daga Arewa da ya zama Administrator (Shugaba) na Gwamnatin Ƙaramar Hukumar Kaduna. A wannan shekarar kuma, Sarauniya Elizabeth II ta ba shi lambar yabo ta Member of the British Empire (O.B.E.) saboda gudunmawarsa ga al’ummarsa.

Ayyukan Muhammadu Aminu Sambo sun wuce zamaninsa. Gudunmawarsa a ilimi, ci gaban birane, da gudanarwa sun bar gagarumin tasiri a Arewacin Najeriya. Makarantun da ya kafa sun zama cibiyoyin ilimi, kuma hangen nesansa wajen tsara gari da kula da muhalli ya zama abin koyi ga shugabanni na gaba.

Ya rasu a shekara ta 1961, ya bar tarihin gaskiya, jagoranci, da ci gaba. A yau, sunansa yana nuni da ƙarfin ilimi, shugabanci mai hangen nesa, da ƙoƙarin cigaban al’umma.
Allah ya gafarta masa da dukkan magabatanmu.

Daga Dandalin Tarihin Magabata

11/05/2026

ABUBUWA 50 DA YA KAMATA IYAYE SU LURA DA SU,DOMIN HANA YAYANSU FADAWA ZINACE-ZINACE.(3)

12. HANA YAYA MATA DA S**A BALAGA WASAN KOKAWA KO RUNGUME-RUNGUME.

Akwai wata sabuwar dabi'a da ta bayyana wadda mutane suna ganinta ba komai ba,ita ce yawan mannewa juna mace da yar'uwarta mace musamman kawaye,wanda suna kaiwa su saba da juna suna iya bayyanar da kirjinsu ga junansu basu damu ba da sauran abubuwa da yawa har suna iya shiga bandaki daya su yi wanka.

Yana da kyau su sani kasancewarsu mata ba yana nufin ya halastawa kowacce kallon jikin yar'uwarta ba,ta janubinmu mu masu fadakarwa a kiyaye saboda gudun fadawa halaka,ta bangaren halasci ko haramci a nemi malamai su yi bayani.

13. NAZARIN 'YA'YA DOMIN TANTANCE KARFIN SHA'AWARSU.

Yana da kyau ya zama muna iya banbance karfun sha'awar yaranmu lokacin da su ka balaga,hakan zai sa mu lura da wurren da su ke iya shiga su kadai ba tare da Security ba..

14. ABINCI

Duk lokacin da yayanmu su ka kai marhalar balaga,dole mu lura da irin abincin da muke basu,kada a rika basu abubuwan da su ke tara sha'awa.

15. TUFAFI.
A bangaren yaya mata,dole ne mu kiyaye sosai wajen hana su sanya kaya masu bayyana tsiraici koda a cikin gida ne b***e waje,domin hakan ke kai idanuwan lalatattu zuwa kan yaya mata,haka ma samarin da su ke makota da su.

Haka suma Mazan a hana su saka kayan da ba su dace ba,suna yawo a tsakiyar kananan yan mata.
1. Gajeren wando zallah,wanda wani yana tafiya ana ganin motsin gabansa.
2. Singlet
3. Ko yawo ba riga yana bayyana cibiyarsa a tsakiyar yaran gida wasu ana iya ganin gashin cibiyarsu basu damu ba,kuma iyaye basu tsawatar ba.

Wannan duka ana maganar yayanmu da ke rayuwa waje daya ne kanne da yayye,na dangi da na makota.

16. KWANCIYA
Yana da kyau idan yayanmu suna kwance mu rika lura da irin wanciyar da su ke yi.Kwanciya tana daga cikin abubuwan da su ke da tasiri wajen tunzura sha'awa.Yana da kyau a yi kokarin hana yara kwanciyar rub da ciki,ko rungume filo da sauransu.

A muhimmantar musu da kwanciya a barin hannun dama yana da muhimmanci sosai.

17. DAUKEWA YAYANMU MATA BUKATUN YAN DA KULLUM.

A nan za mu ja hankalin iyaye maza wanda zan ce 90% daga cikinsu basa lura da matsalolin yayansu mata.

Mutum yana da 'Ya ta balaga amma bai san a ina take samun kudin sayen audugar mata ba,kai bai taba hirar da mahaifiyarta ba,bai ma san ta fara al'adaba ko aa,bai san ina take samun kudin Kyan amfaninta na yau da kullum ba,har kananun sutura irinsu Pant,underwear da brassiere,b***e a yi maganar kayan kwalliya.

Ita mace akan kanta tana so ta ji ta yi kwalliya ta fi samun nutsuwa da sukuni koda kuwa bata da aure.

Maza da yawa sun dauka ita mace tana yin kwalliya ne kawai saboda biki ko miji,lallai ba haka bane.

Mace tana jin dadi da samun farinciki ta yi wanka ta yi kwalliya ta duba mudubi ta kalli kwalliyarta koda kuwa barci zata kwanta,to wane taimako muke yiwa yayanmu da basu da mazaje ?

Akan wannan bukatar mata da yawa sun fada mummunan hannu.

Mata da yawa sun bada kansu sabi kananun bukatun wanda sun gagara fadawa iyayensu saboda kunya.

Yana da kyau a rika basu kyautar kudade masu nauyi dan biyan bukatarsu wadda ba lallai iyaye maza su kai hankulansu kanta ba.

18. KYAN KALLO.
Wajibine ga iyaye su lura da irin tashohin da yayansu ke kallo.

19. LITATTAFAI.
Duk lokacin da ka ga yaro da littafi ka tabbatar ka amsa ka ga maye a cikinsa,haka a rika yawan bincika jakunkunansu ana ganin me su ke ajiyewa ciki.

20. WAYA.
Tana daga cikin abubuwan da su ke lalalata tarbiyyar yayanmu,wajibine ku rika sanin abubuwan da ke cikin wayoyin yayanku.

Tun daga shafukan Social media zuwa fima-fimai da ake turawa.

21. KIRAN WAYA.
Idan so samu ne duk wanda ya kira yarki a waya ya zama kina kusa da ita kina jin me ake tattaunawa,kuma kada a tsawaita,idan so samu ne kada a yarda su mallaki layukansu saidai su yi amfani da wayoyinku,idan suna son waya to idan sun yi aure mazajensu su saya musu.

Za mu ci gaba Insha'Allah
08034318311
11/05/2026

11/05/2026

ABUBUWA 50 DA YA KAMATA IYAYE SU LURA DA SU,DOMIN HANA YAYANSU FADAWA ZINACE-ZINACE.(2)

3. SON JIKI.
A kwai yaran da ake haihuwarsu da son jiki wanda za ka ga ko da yaushe suna makalewa a jikin mutane,wasu ma sai kaga suna shafa mutum,yana da kyau a rika tsawatar musu ana takaita musu yawan bin jikin mutane da su ke.

Daga cikin matsalolin da hakan ke haifarwa:..

Za su iya fadawa hannun mutanen banza,sannan kuma za su iya tashi suna bin jikin mutane ba tare da wata damuwa ba.

Wasu shekaru masu nisa na taba ganin wata yarinya bata fi shekaru 4 ba,amma tana kwantawa a jikin mutane tana cewa dadi ta ke ji,har na tsawatar mata, tare da masu tambayarta me ta ke ji.

4. RABA WAJEN KWANCIYA.
Rabawa yaranku maza da mata wajen kwanciya,sannan da nuna musu haduwar mace da namiji waje daya ba abu ne mai kyau ba tun suna yara,har wasanni idan zai yiwu a raba musu.

Na san lokcin da muna yara idan aka ga Namiji yana wasa da Mata ana ce masa Na Mata Na Mata,idan mace ce,ana ce mata,mai wasa da maza karya,tunda na ganta na rainata....

Lallai wannan ya sa Mace da Namiji suna tashi kowannensu na kyankyamin ya kusanci dan'uwansa ko da uwa daya uba daya su ke,wanda a yanzu wannan zamanin ya rusa mana wannan tsarin,sai ya zama suna tashi tare su balaga a waje daya,shi kuma wannan canjin da ake samu na shekarun balaga ba ruwansa da sabo yan'uwantaka,nasan an sha samun matsaloli na yara uwa daya uba daya.

5. BOYE TSIRAICINSU.
A nuna musu tun tasowa suna da wasu wurare da ba a so kowa ya gani.
Hakan yana taimakawa lokacin da girma ya zo musu su kara tsananta kyamar bayyanar da wasu sassan jikinsu a tsakaninsu.

Wannan za mu iya cewa koda kuwa uwa daya ne uba daya,a tabbatar suna boye wasu sassan jikinsu tsakanin koda mace da mace haka namiji da namiji,b***e kuma mace da namiji.

A wannan wurin zan so mu yi jan hankali ga iyayen da basu damuwa da sauyawar kirjin yayansu mata,wanda ya dace tun kafin lokacin su fara nuna musu muhimmancin rayuwa da hijabi.

Shi wanda ku ke ganin dan'uwanta ne da su ke rayuwa sha'awarsa bata gaya masa haram da halas,addini ne kawai yake fadin wannan.

A shari'a har iyaye akwai wuraren da haram ne yayansu su kalla nasu b***e kuma kanne da yayye.akwai kuma wanda bai kamata ba,..a gaban danki da ya kai shekaru sama da 10 ki rika fito da kirjinki waje a gabansa,wannan ba muna cewa haram bane idan ana son sani a je wajen malami,amma dai kada a saba masa da kallon wadannan wuraren tun a gida,domin zai zama ba sa kyankyamin kallo ha a waje..

6. Cakuduwar yara maza da mata waje daya tsirara koda kuwa lokacin wanka ne.

Akwai matsaloli da su ke yawan faruwa na yara da ake samu suna aikata munanan dabi'u duk da su basu kai lokacin balaga ba.

Na farko kamar yadda muka fada kwakwalar dan'adam na cike da tambayiyi ne kuma tun daga yarinta,to su yara wannan banbamcin idan su ka gani so su ke sai sun tabbtar ya ya ke,to sakaya wurin yana hana tunaninsu yakai wurin.

7. CANZA TSARIN ZAMAN MAKARANTU.
An ci bahaushe da yaki wajen nuna masa mace da namiji abu daya ne musamman a makarantun zamani,tun daga yarinta ake cakudasu waje daya komai ana hada su yi harda kokawa,a nan yara ke tashi basa jin tsoron hada jiki da mata,kuma wannan lokacin shine gini na farko da ake yiwa yara na tarbiyya.

A nan yaro yake tasowa har balaga ba'a taba nuna masa banbancin mace da namiji ba,ana rayuwa babu kyankyami har su balaga a tare,suna shiga makaranta tun suna yara,idan makarantar ta zama mai hade da secondary haka zaka ga sun zama kawayen juna,gasu shekarunsu ya kai na balaga,amma komai tare ake,..kwallo guje-guje zama waje daya cin abinci tare,wannan kam ba bukatar dogon sharhi,kowa zai gane kuma zai halarto da barnar da ke faruwa.

8/9. KWADAYI DA DANGANA.
Hana yara kwadayi ta hanayar koya musu dangana dole,ya zama yaro da kansa ba komai zai gani ya sa ransa ba.
Tun suna yara ya zama ba komai su ka gani iyaye na ci sai an basu ba,wannan abu ne mai wiya amma yana da kyau.Haka kuma ba komai ne in za a basu sai an ci ba,Musali:

Iyaye su zo da abu mai dadi su cinye su hana yayansu,wani lokaci kuma a zo da abu mai dadi a mika musu ba sai iyaye sun ci ba,ko kuma,..ba su san da shi ba su ga an dauko an basu,..Mun san wannan akwai wahala sosai wani ma ba zai gane falsafar da ke ciki ba,amma akwai amfani matuka,horaswa ce sosai,duk ba za a gane ba sai an je da yaro cikin taro ya zama ba ya sa ido a kan abubuwa na ci ko sha za a gane fa'ida,sannan za a gane munin abin idan yaro ya hango wani abu na ci ko sha a wani gida ko a hannun yara ya sakawa abin ido.

Hakan yana nuna musu cewa,ba komai bane idan su ka gani sai sun ci,sannan ba komai bane idan aka basu yana nufin saida aka ci aka rage ba.

Idan yaro ya ko yi wannan,ko da ya hadu da yara masu munanan dabi'u abin hannunsu ba zai sa yakwantar da kai a wajensu ba,haka ma manya masu yaudarar yara da wasu abubuwa dan lalata su.

Sannan wannan ginin na farko na tarbiyyar yara anan ake samun matsala,yaro ya koyi wasu dabi'u da har tsufansa ba zai iya dainawa ba..

10. ROKO.
Wannan musamman yaya mata,iyaye masu yawan roko suna aika yara wurare a roko musu abu,hakan yana sanyawa yara su tashi basa kunyar rokar abu,to babbar illa tana ga 'ya mace.Lokacin da mace ya zama bata da kunyar roko to ba zata iya banbance inda ake yinsa ba,kuma wannan yana kai su ga fadawa mummunan hannu,kuma rokon zai zamar musu jiki basa ganinsa a matsala har girmansu.

11. DOLE NE KULA DA LOKUTAN BALAGA NA YARA.
A nan muna so iyaye su sani kuma su ajiye tsohon lissafin da su ke da shi na da can a kan abinda ya shafi lokacin balagar yara.

Duk wanda ya ke da 'ya mace,daga lokacin da ta kai shekaru 9 idan ya dauka cewa yarinya ce karama ya yi kuskure,masana sun gano mace na fara balaga ne daga shekaru 9 kenan daga 8 za mu fara saka ido a kansu.

Haka namiji daga shekaru 15 ya ke fara balaga,..kenan daga shekara 14 za mu saka musu ido.
Kamar muna so muce,idan yaranmu su ka kai wannan shekarun kada mu dauka basa jin dadin taba juna tsakanin mace da namiji,wanda a yanzu haka ake tafiya,yarinya zata kai shekaru 12/13 amma za ka ga samari na rike mata hannu suna wasa da ita saboda babu alamar girma da ya bayyanar mata,alhalin tana jin dadi,shi ya sa itama ta ke haye musu ko yaushe,musamman masu tallace-takkace,ko kuma rayuwar Family,kuma wasu abubuwan idan su ka faru ai ta mamaki.

A irin wannan lokacin wajibine raba musu wajen kwanciya,ma'ana kada a rika hada su daki daya maza da mata,idan maza ne kowa ya koma gefensa da ban shi kadai,idan mata ne suma kowa da gefensa shi kadai.

Ba'a so mace da mace su rika shafar junansu a lokacin haka ma Namiji,shafar da zata bayar da wata ma'ana.

Za mu ci gaba Insha'Allah

Shareef Muhsan Bachirawa
08034318311
10/05/2026

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Kano