02/01/2023
Fatan Alkhairi a Gare ku Mabiyanmu.
Bronu diaiz fixed Domin Samun Sahihan Labarai Na Gida Dana Kasashen Ketare.
02/01/2023
Fatan Alkhairi a Gare ku Mabiyanmu.
Gaskiya Fedaral Gamman ba ta kyauta ba da ta biya ƴan ASUU rabin albashin watan Oktoba maimakon ta biya su duka. Duk da cewa sai ranar 14 ga watan s**a janye aiki, k**ata yayi kawai a biya su watan gaba ɗaya, musamman ma tunda buƙatun da s**a sa aka yi yajin aikin ma basu biya ba. Sam ba dace a haɗa mari da tsinka jaka ba.
Amma na ji ance ASUU za ta yi taro ranar Litinin domin duba yiwuwar komawa yajin aiki. Ina fatan shugabannin ASUU za su kai zuciya nesa, su kuma yi aiki da hankali. Su lura cewa yajin aikin watanni takwas baya din da s**a yi ma bai amfane su da komai. Saboda haka, idan s**a koma yajin aiki, gidan jiya kawai za a koma.
Sabon yajin aiki kawai zai ƙara kawo tsaiko ne ga karatun ƙannenmu kuma ya ƙara jefa mambobin ASUU cikin ƙangi wahala. Kamar yadda hirarsa ta kwanan nan ta ƙara fito da abin fili, Buhari fa ba shi da tausayi, bai san ya k**ata ba kuma matsalar talaka ba ta dame shi ba. Don haka, idan ma ASUU ta koma yajin aiki, wallahi ko a kwalar Buhari.
Maimakon tsunduma cikin wani yajin aikin, gara ASUU ta ci gaba da tattaunawa da Gwamnati kuma su ci gaba da matsa mata ta kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta tun da ba za su iya zanga-zanga ba. Idan s**a ɗau wannan hanya, duka za mu fito mu taya su wannan yaƙin.
Daga ƙarshe, ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta biyan ƴan ASUU sauran albashin watan Oktoba.
12/09/2022
Mu wannan ba shine matsalar mu ba, Nigeria Sai Buhari kawai.
Ko kun san cewa Sarki Charles III ba ya bukatar fasfo domin ya ziyarci duk kasar da ya ke so?
Idan ya isa kasar da yake so, sai kawai ya bayyana sunansa da sauran bayanai k**ar adireshinsa da shekarunsa na haihuwa ga jami'an shige da fice na kasar da ya ziyarta.
Tammat...
12/09/2022
BBC ku tabbata kun bita kabari don mu samu complete labarai 🙄🙄🙄🙄
Duka 'ya'yan Sarauniya sun isa wurin da aka ajiye akwatin gawarta
Karin bayani - https://bbc.in/3d5qIqy
10/09/2022
Nikam Yanzu Bani Koma Cewa Komai Sai BBC Hausa Sundawo Dai-Dai
Jawabin Sarki Charles III: 'Ubangiji Ya sa sahun mala'iku su yi mata rakiya kushewarta cikin yabo'
10/09/2022
Fuskokinsu cike da annashuwa zasu nada sabon sarki yayita tsohuwar sarauniya kecan kwance cikin firji Babu Rai, Duniya!!!
Masu naɗin Sarki a Ingila sun taru domin naɗa Charles III
https://bbc.in/3esJsk3
03/09/2022
16/08/2022
BABBAR MAGANA:
Wani Fasto mai suna James Sakara ɗan ɗasar Zambiya, ya nemi a binne shi da rai bisa cewa zai sake dawowa duniya cikin kwanaki uku k**ar dai Yesu Al-masihu, amma abin baƙin ciki haryanzu bai samu ya dawo ba. Yanzu haka ƴan sanda sun k**a waɗanda s**a taimaka masa wajen binne shi.
16/08/2022
Manomi ya yanke marainan sa a barci bayan yi yi mafarkin yana yanka nama
Wani manomi a Ghana yana can kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marenansa (golaye ko kwalatai) a lokacin da yake barci.
Mutumin mai suna Kofi Atta, wanda a gadon asibitin da yake ya gaya wa BBC yadda lamarin ya faru, yana can ana ƙoƙarin duba yadda za a yi masa aiki.
Ya ce a yanzu dai ana sa masa ƙarin ruwa ne tare da wasu allurai da ake ta yi masa, amma dai sai an yi masa tiyata.
Sai dai ya ƙara da cewa a yanzu ba shi da ko kudin da zai biya motar asibitin da za ta dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a kasar ta Ghana inda a can ne za a iya yi masa tiyata.
Mutumin ya ce, yana barci ne na ƙailula wato da rana a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama da ke ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marenan nasa.
Mista Atta ya ce abin ya ba shi mamaki ƙwarai domin har lokacin da wasu maƙwabtansa biyu s**a kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya riƙa jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.
'Na yanke kwalataina ina barci'
Mutumin ya ce, har lokacin da aka kawo masa daukin ba shi tabbacin kan abin da ya faru, ji yake k**ar yana mafarki ne.
Ya ce shi kansa bai san yadda aka yi ya dauko wuƙar ba ma, ''abin ya ɗaure min kai, '' in ji shi.
Manomin mai shekara 47 wanda ke garin Assim Akomfode a yankin tsakiyar kasar (Central Region), har bayan da ya yanke marenan nasa yana cikin barci har ya yi kururuwar neman taimako bai farka ba yana cikin mafarki ne domin shi duk bai san abin da ya faru ba a lokacin.
Ya ce duk da cewa maƙwabtansa sun kawo masa dauki inda ya riƙa jin zafi a gabansa ga kuma jini yana zuba, bai fahimci abin da ya faru ba, sai daga baya a gadon asibiti hankalinsa ya dawo ya san abin da ya faru.