Darul Qadiriyya riyadul jannah

Darul Qadiriyya riyadul jannah Dan Neman Karin bayani KO bada shawara
(1)

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN!!!.A madadin Maulanah Amirul wa'iziyna Sheikh Abduljabbar Kabara da yan uwa da masoya...
19/07/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN!!!.

A madadin Maulanah Amirul wa'iziyna Sheikh Abduljabbar Kabara da yan uwa da masoya wannan makaranta ta Mujamma'u Ashabil Kahfi Warraƙim, muna miƙa saƙon ta'aziyya bisa babban rashi na ɗan uwa kuma masoyi, wato Nasir Jilani Mahiru Sharif Bala (Sinhaji) wanda Allah ya karbi rayuwarsa sakamakon hatsarin jirgin ruwa tsakanin iyakar Kamaru da jihar Adamawa, a jiya Asabar 18/07/2026.

Muna roƙon Allah ya jiƙansa ya bashi shahada, tare da dukkan mamatanmu baki ɗaya.

©MASAK ✍️
19/07/2026.

10/07/2026MUHIMMIYAR SANARWA.~Maulana Ameerul Wa'izeena (H)
11/07/2026

10/07/2026

MUHIMMIYAR SANARWA.

~Maulana Ameerul Wa'izeena (H)

بسم الله.والصلاة والسلام على رسول الله وآله.جزء من القصيدة.....أحسنتمو  يا  شيخنا أحسنتموولدى الصباح سَيَحْمَدُ القومُ ا...
02/07/2026

بسم الله.
والصلاة والسلام على رسول الله وآله.

جزء من القصيدة...
..أحسنتمو يا شيخنا أحسنتمو
ولدى الصباح سَيَحْمَدُ القومُ السرى.

تحقيقكم في البحث أضحى ناتجًا
وسواكمو في البحث أضحى أبترا.

والباحثون نشيم من تحقيقكم
وَهْجاً غدا من ضوء شمس أنورا.

ونشم من رَيَّاكمو عرفاً شذى
نسرينه طِيباً يفوقُ العنبرا.

عَطَّرتمو ما كان قِدْماً نَتَّنوا
ما المسك ريحاً كان هذا أعطرا.

فجزاكمو الرحمنُ خيرَ جزائِه
وسقاكمو من كَفِّ طه الكوثرا.

أودعتمو في الجوف علماً باهرًا
طُولاً وعَرْضاً غَوْرُه لن ينكرا.

من رام تحقيقا يَغُصْ في جوفِه
عُمقاً فإن الصيدَ في جوفِ الفرا...

Allah ya karawa Maulana Ameerul Wa'izeena lafiya da nisan kwana, Ubangiji ya yanke mana wannan jarabawa, ya faranta mana da futowarsa a kusa, alfarmar Shugaba SAWW da Alayensa AS.

@محمد النفس الزكية كبر

29/06/2026

Litattafai 227 da sarki yola ya kwace yau alkalan kotun daukaka kara sunyi umarnin a dawo dasu gabanta.

22/06/2026

Game da rahoton zaman kotu kan shari'ar Maulanah Amirul wa'iziyna Hafizahullah na yau Litinin 22/6/2026, a saurari gidajen jaridu sunyi hira da babban lauya wanda shi ne yake wakiltar Malam a shari'ar, don haka duk wanda yake so yaji abinda ya faru ya saurari rahoton zuwa anjima.

Muna fatan Allah ya ƙarawa Malam lafiya, ya bamu nasara ya fito mana da shi lafiya.

Dangane da Shari’ar Maulanah Amirul Wa’iziyna (H) ga lazumi da kowane ɗan makaranta ake so yayi a daren yau.Zaka karanta...
21/06/2026

Dangane da Shari’ar Maulanah Amirul Wa’iziyna (H) ga lazumi da kowane ɗan makaranta ake so yayi a daren yau.

Zaka karanta ayar ​مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ kafa 17 sai ka roki Allah bukatar(samun rinjaye da tabbatar adalci akan Shari’ar) sai ka kara karantawa ita wannan ayar ​مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ kafa 107 sai ka kara tsayawa ka roki Allah bukatar sai ka kuma kara karantawa kafa 1007 sai ka kara rokon Allah bukatar a rufe da yiwa Annabi S.A.W salati da ya'yan ɗakin sa.

Muna rokon Allah rinjaye da samun galaba akan wadannan azzaluman kada kuma a manta da markar Hasbunallahu wani’imal wakilu.

~ Muhammadu Hafizu Yusuf

28/05/2026
30/04/2026

Clip 1

Alhamdulillah!Malam dai ya hannata case a hannun wannan lauya da Kotu ta bashi shawarar ya hannatawa mutum ne me Amana s...
25/04/2026

Alhamdulillah!

Malam dai ya hannata case a hannun wannan lauya da Kotu ta bashi shawarar ya hannatawa mutum ne me Amana sai yan makaranta a shagala da ruwan Hasbunallahu wani'imal wakilu da cigaba da kaiwa Allah kuka.

25/04/2026

Shari’ar Sheikh Abduljabbar: Kotu Ta Kori Ɗaukaka Ƙara, Ta Mayar Da Maganar Gaban Babban Alƙalin Jihar Kano (Chief Judge...
23/04/2026

Shari’ar Sheikh Abduljabbar: Kotu Ta Kori Ɗaukaka Ƙara, Ta Mayar Da Maganar Gaban Babban Alƙalin Jihar Kano (Chief Judge)

Aliyu Samba

Babbar Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin alƙalai uku, Mai shari’a Mohammed Lawal-Shuaibu, tare da Mai shari’a Abubakar Mu’azu-Lamido da kuma Mai shari’a Ahmad Ramat-Mohammed, ta umarci a mayar da shari’ar Malam Abduljabbar Nasiru Kabara gaban Babban Alƙalin Jihar Kano (Chief Judge) domin sake duba ta bisa ƙa’ida, bayan gano kura-kurai a takardun da aka shigar.

A zaman kotun na ranar Alhamis, an tafka muhawara mai zafi tsakanin malamin, wanda ya bayyana cewa zai kare kansa da kansa, da kuma lauyoyin gwamnati.

Sheikh Malam Abduljabbar ya roƙi kotun da kada a mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, inda ya yi zargin cewa rayuwarsa tana cikin haɗari a can. Haka kuma, malamin ya nuna shakku kan takardun da aka kai masa gidan yari, inda ya zargi cewa lauya ne ya kai masa maimakon ɗan aiken kotu.

Sai dai kotun ta tabbatar masa da cewa wanda ya kai takardar ɗan aikenta ne na halal, ba lauya ba.

Lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano, Barista Bashir Sale da Barista I.A. Garba, sun buƙaci kotun da ta kori ɗaukaka ƙarar malamin baki ɗaya. Sun hujjatar da cewa an shigar da ƙarar ne ba tare da bin ƙa’idojin shari’a ba, don haka babu dalilin ci gaba da sauraron ta.

Ita ma kotun, bayan bincike, ta amince cewa takardun da duka ɓangarorin biyu s**a shigar ba su tafi daidai da tanadin doka ba.

Kotun ta tunatar da Malam Abduljabbar cewa wannan kotu ce ta ɗaukaka ƙara, ba kotun da aka yi masa shari’a a baya ba. Alƙalan sun bayyana cewa Har yanzu akwai sauran shari’a a gaban kotun ƙasa wadda ba a sanya ranar ci gaba da ita ba. Sannan Akwai bayanan cewa wani lauya, Barista Adamu Abubakar, ya riga ya shigar da ƙara a madadin malamin a kotun ƙasa.

Kotun ta nanata wa malamin cewa doka ta ba shi damar neman lauya, kuma idan ba shi da hali, gwamnati tana da nauyin samar masa da lauyan da zai kare shi saboda nauyin shari'ar.

Bayan duka ɓangarorin biyu sun amince cewa a koma kotun ƙasa domin yin gyara, kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke shawarar mayar da maganar gaban Babban Alƙalin Jihar Kano. Kotun ta bayyana cewa tun da babu wani takamaiman hukunci da aka riga aka yanke a yanzu, kuma takardun kowa na ɗauke da kuskure, gara a bi hanyar da doka ta tanada domin yi wa kowa adalci.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen zaman na yau, yayin da ake jiran mataki na gaba daga ofishin Babban Alƙalin Jihar.

Address

Kano

Telephone

+2348034907705

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darul Qadiriyya riyadul jannah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Darul Qadiriyya riyadul jannah:

Shortcuts

Share