Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya

Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya, Education, Kano.

Photos from Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya's post 23/04/2026

Shekara 10 da Bude Makarantar mu "Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya" Wacce Ambassador Doctor Hajiya Umaimatu Umar Muhammad Tagina Ƙarƙashin Rukunin Makarantun Sheikh Muhammadu Dan Almajiri. Ambassador Hafizu Aminu Daiba Yake Jagorantar ta.

AN BUDE MAKARANTAR RANAR 24/4/2013.

Da Izinin Maulana Sheikh Fadalu Dan Almajiri Wanda Na'ibin Masallacin Daiba Sheikh Barhama Dan Almajiri ya Jagoranta.

Mun Tsara Makarantar ta Yara Ƙanana, Shekara 5 zuwa 10 Muke Dauka Su Girma a Hannunmu, Muna Karatu Daga Asabar Zuwa Laraba, 7:300 Zuwa 6:00 na Yamma.

MANUFAR MAKARANTAR.

Har datar da 'Ya'yan Musulmi Alqur'ani mai girma Tun daga Ƙuruciya, Samar Musu da Ilimin Litattafai na Addini Dana Zamani, Samar da In gantacciyar Tarbiyya.

WASU DAGA NASARORIN DA MUKA SAMU.

-Fidda Hafizan Alqur'ani mai girma tare da Tilawa.
-Samar da Ƙarin Ajujuwa daga Uwar Marayu da Kuma Gwani Mal. Abbas Musa.
-Samar da Rijiyar Burtsate.
-Samar da Solar da Fankoki daga Uwar Marayu.
-Ziyarar Annabi S.A.W da Shugaban Makaranta Yaje Daga Uwar Marayu.
-Kyautar Filaye ga Malaman da S**a Fidda Hafizan Alqur'ani a Makarantar.
-Daukar Nauyin Karatun Marayu da Cigaba da Karatun su a Makarantun gaba.
-Yimata Rijista da Ma'aikatar Ilimi, da CAC, da Sauran Ƙungoyoyi da S**a Shafi Har Kar Ilimi Halastattu.

WASU DAGA MATSALOLIN MAKARANTA

-Dorawa Makaranta Bene Domin Fadadawa.
-Gyaran Solar da Ƙara Girmanta da Ƙarin Fankoki Sabo da Zafin Rana ga Dalubai.
-Gyaran Rijiyar Burtsatse.
-Samar da Ƙarin Bandakuna da Gyara na Yanzu.
-Samar da Shinfidu Waato Tabarmi ga Dalubai.
-

WASU DAGA BURIKAN MAKARANTA

-Cigaba da Fidda Hafizan Alqur'ani Masu In ganci.
-Samar da Yanayi mai kyau ga Malamai domin in ganta koyo da koyarwa.
-Fadada Fannin Boko
-Samar da Gidajen Malamai a Kusa da Makaranta.
-Bude Makarantar Matan Aure Alhamis da Juma'a.
-Bude Makarantar Manya Bayan Magariba.
-Bude Ɓangaren Bodon Tsarin Kwana na Dalibai.
-Samarwa Malaman Makaranta Muhalli na Din dinnan.
-Koyawa Dalubai Sana'a.
-Daliban Makaranta Suzama Wayayyu Acikin Addini da Rayiwarsu ta Ƙuruciya Har Girmansu.

Duka wanan Faralace Daga Allah Madaukakin Sarki Alhamdulillahi.
Domin Gani da Ido Yanda Makaranta Take tafiya zaku iya kai ziyara Shafinmu na Facebook Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya ko kuma kawo ziyara kai tsaye Makaranta ko ta hanyar WhatsApp ko kira 08038651846

Allah ya ƙara Daukaka Makarantun Alqur'ani da Ma'abo Alqur'ani da Masu yiwa Alqur'ani hidima da Masoya Alqur'ani

Photos from Nurul Islam Fi Rihabil Qur'an Hajara Islamiyya's post 23/04/2026

Cikin Godiya ga Allah Shekarar su 3 da Hardace Alqur'ani a Wanan Makaranta

11/04/2026
01/03/2026

Daya Daga Hafizan Alqur'ani mai girma na wanan Makaranta 2026 lokacin da suke gabatar da Musaffa.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Kano
700252