17/10/2025
1. Ikhlasi (Niyya) – Ka tabbata haddanka don neman yardar Allah ne, ba don a yaba maka ba.
2. Tsari da lokaci – Samu jadawalin karatu na kullum; kada ka bar rana ta wuce ba tare da ka karanta ba.
3. Maimaici (Repetition) – Maimaitawa tana ƙarfafa kwakwalwa, tana sa kalmomin Qur’ani su zauna a zuciya.
4. Aiki da abin da kake haddacewa – Yin aiki da Qur’ani yana taimaka maka ka fahimta kuma ka tsare shi da zuciya.
5. Neman taimako daga Allah – Yawaita addu'a, musamman da wannan:
“Rabbi yassir li hifz al-Qur’an, waj‘alhu nuran li qalbi.”
(Ya Allah, ka sauƙaƙa min haddar Qur’ani, ka sanya shi haske a zuciyata.)
📌 Ka sani: Haddar Qur’ani ba gasa ba ce — tafiya ce tsakanin kai da Allah. Sannu a hankali, da gaskiya da dagewa, za ka kai.