Egypt Plugs

Egypt Plugs

Share

Connecting Nigerian customers to Egyptian Luxury market The № 1 Portal for Africans to learn Digital Skills.

We provide trainings on the following Skillsets:

✍️ Cryptocurrency trading
✍️ Programming
✍️ Digital Marketing
✍️ Ethical Hacking
✍️ Graphics & UI/UX Design
✍️ Community Management
... And lots more

05/10/2024

Assalamu alaikum Wa Rahmatullah.

Al'ummar Birnin Kebbi da kuma Mutanen Gusau a Zamfara State in sha Allah Shardeum na nan zuwa kawo muku ziyara rana irin ta yau a cikin state University Jega, Kebbi State, sai kuma Ranar Litinin ta Sama in sha Allah zamu hadu cikin garin Gusau.

Da fatan zaku samu damar halarta.

Zamu sanar da exact venues din zuwa monday in sha Allah, ku fara tattara mana abokanku da sauran abokan arziki.

In sha Allah duka yan baiwan Arewa sai sun samu Airdrop na Shardeum.

Zuwa yanzu mun sallami Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, Taraba, Bauchi, da Sokoto sauran next week zamu kawo muku ziyara ya ku zamfarawa da Kebawa

Photos from Egypt Plugs's post 03/09/2024

Sakon godiya ga jama'ar Sokoto

Assalamu alaikum wa rahmatullah

A ranar Asabar 31 ga watan Satumba, mukayi organizing na event karkashin daukar nauyi na Shardeum Blockchain a cikin garin Sokoto birnin Shehu.

Hakika Sakkwatawa sun nuna mini halacci ta solidarity wanda sama da mutane 80 s**a halarci wannan taro.

A wannan taro mun tattauna abubuwa da yawa tun daga kan abinda ya shafi Internet har zuwa web3 da kuna damarmaki da muke dasu a web3 da yanda mutum zai iya amfana da wannan damarmarki.

A karshe mun bada shawarwari ga yan baiwa akan lallai su nemi ilimi. A karkashin wannan muka yi alkawarin bude Academy a cikin Garin Sokoto.

A halin yanzu har mun mallaki office a Argungu Plaza, mun biya an bamu mukullin wurin, in sha Allah zamu kammala duk wani tsare-tsare da ya kamata a fara karatu nan da karshen wannan wata a office dinmu na Sokoto.

A yanzu DCTv Africa Africa ta mallaki offices guda uku kenan, Kano, Gumel da kuma Sokoto.

A karshe ina mika godiya ta musamman ga dukkan wanda s**a halarta, da wanda s**a taimaka mini wurin tabbatar da nasarar wannan taro, Zubair Bello, Umar Dan Anini da sauran dalibaina na DCTv Africa online class, DCTV Africa Dev club da sauransu, ina fatan kowa ya koma gida lafiya.

31/08/2024

Da safiyar nan nayi rubutu a (Twitter/X) akan neman exchanges da muke dasu suyi kokarin shigo da yaren Hausa cikin customer support nasu, duba da yawan al'ummar da muke dasu da suke mu'amala da crypto amma suna da matsala da turanci, musamman bangaren p2p.

Ina rokon yan uwa suyi engaging na wannan post din domin mu tabbatarwa da exchanges din cewa muna da yawan da ya kamata a sauraremu.

Wannan abun idan Allah yasa mukayi nasara zai kawo cigaba da yawa a harkar crypto a Arewa kuma za'a samu wasu daga cikin yan arewa su samu aiki a exchanges din a matsayin customer support agents.

Please aje ayi ta comment da reposting har sakon ya kai ga wannan exchanges din.

Ina rokon yan uwan influencers zasu karawa abun armashi ta hanyar yin posting irin wannan ko kuma suyi engaging nawa post din.

Ga link na post dina comment domin ayi engaging nashi.

Sunusi Danjuma Ali Engr Musa Adam Adam Muhammad Mukhtar Abdul-Hadee Isah Ibraheem Ramiyu Abdulmalik Muhammad Sheka Mahmoud Muh'd Sardauna Al-ameen S Shuaib Abdulrahim Salisu Engr Muhammad Sagir Muhammad Abubakar Musa Zahra Usman

27/08/2024

Assalamu alaikum

Sokoto people here I come

Kamar yanda na sanar a satin da ya wuce in sha Allah wannan weekend zamuyi taro na musamman a cikin birnin Sokoto.

In sha Allah zan sauka Sokoto ranar Alhamis da rana, idan na samu na huta, Ranar Juma'a Aji na Musamman inda zamuyi karatu tun daga safe har zuwa abinda Allah ya bamu iko.

Sai kuma Ranar Asabar 31st, August 2024 zamuyi taron Shardeum Blockchain wanda muke sa ran in sha Allah duk wanda s**a halarta zasu samu Airdrop mai nauyi a lokacin da s**ayi launching.

Zamu fara taron ranar Asabar da misalin 9:30am na safe domin zan bar Sokoto da misalin 1:00pm a ranar.

Wurin Taron shine: K7 Mall, One Agaie Road, Opposite State CID Office, Sokoto.

Kowa yana bukatar yayi register kafin halartar class din da kuma taron (link a comment)

Wannan sakon gayyata ne ga dukkan yan baiwa na Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Sanann in sha Allah zamu tattauna yanda zamu kawo zaunannen office na dindin reshen DCTv Africa wanda in sha Allah zamu dinga koyarwa da kuma mentorship daga wannan office.

Sauran States da muka ce zamu bude office bamu fasa ba, muna da tsari wurin office gaskiya. Bama son bude temporary makaranta da za'a yi class a rufe ta shikenan a bar students suna watangaririya, NO, muna son mu samar da wuri da ko ka kammala zaka dinga zuwa domin guide da mentorship.

Taraba, Katsina, Jigawa da Sokoto ku sani kullum da ku nake kwanciya nake tashi, in sha Allah wata rana Allah zai bamu yanda zamu kula da ku yanda ya kamata da tsayayyan office.

Muna addu'ar Allah ya taimaka mana.

20/06/2024

Assalamu alaikum wa rahmatullahi.

In sha Allah ranar 1st July, 2024 zamu fara registeration na sababbin dalibai a physical class na DCTv Africa da muke gabatarwa a Kano.

Duba da yanayin yawan roko da bukatuwa zuwa ga class da mutane da yawa daga sassa daban-daban na Nigeria, wanda mutum bazai iya zuwa Kano ba, hakan yasa muka yi shiri na musamman yanda mutum zai iya joining Physical class din amma online.

Zaka dauki darasi online tare da wanda suke physical, zakaga komai sannan kaji komai kamar yanda wanda yake a wurin zai ji. Sannan idan baka gane abu ba, a lokacin zaka iya yin tambaya a maka karin bayani kamar kana cikin ajin.

Mun tanadi kayan aiki domin tabbatar da wannan tsari ya tafi yanda ya kamata, da kuma kokarin yada ilimi zuwa kowane lungu da sako na Nigeria.

Kawai abinda ya banbanta wanda zasuyi joining online da wanda suke physical shine ba matsalar network ko rashin wuta ko dsiturbance.

Wannan dama ce ga duk wanda yake son koyon crypto da gaske.

Zamuyi kokarin saka kudin da bazai gagara ba saboda kowa ya samu yayi affording class din. Registration zai kasance daga - in sha Allah bazai wuce haka ba. Sai mutum ya fara tanadi tun yanzu.

Koyi karatu tatacce a ko'ina kake a duniya daga DCTv Africa kamar kana cikin garin Kano.

Da fatan zakuyi patronizing namu sannan ku taya mu yada wannan manufa ta ilimantar da al'umma.

Sabiu Muhammad Danpullo
CEO DCTv Africa

27/05/2024

Assalamu alaikum wa rahmatullah

In sha Allah yau da Misalin karfe 4:05pm na yamma zamu yi hira ta musamman a Gidan radiyon Premier Radio 102.7 FM inda ni da oga Sunusi Danjuma Ali zamu fadi albarkacin bakinmu akan abinda ya shafi mining da kuma cryptocurrrency in sha Allah

Zaku iya bibiyar shirin akan shafinsu na facebook ko kai tsaye ku kamo tashar akan 102.7 fm domin saurare.

Za'a bada damar yin tambaya da contribution in sha Allah

Allah ya bamu nasara

25/05/2024

Assalamu alaikum wa rahmatullah

Yanzu na shiga youtube na ci karo da wani video na Prof. Umar Sani Fagge, in da yayi tsokaci akan cryptocurrency.

Hakika Malam yayi maganganu masu taba zuciya kuma masu ma'ana. A cikin maganar da yayi ya bada ka'idoji guda uku da kasuwanci ke iya halatta, ma'ana idan ka cika wannan ka'idojin uku to abinda ka samu daga wannan kasuwancin Halal ne, indai ba akwai wani nassi karara da ya haramta abinda kake kasuwanci ba.

Na farko Malam yace kana bukatar hannun jari, ma'ana capital da zaka zuba domin juyawa da niyyar idan haja ta kara daraja ka sayar ka samu riba.

Na biyu Malam yace kana bukatar ilimin gudanar da kasuwanci, wanda idan muka dauko wannan maganar zuwa crypto zamu iya kiran wannan da ilimin Analysis (Both Technical, Fundamental, On-chain and other related skills) a trading.

Na uku malam yace idan ka hada wadancan abubuwa biyu, sai kuma ka jira masu saya.

Malam yayi wannan maganar cikin minti dayan farko na Video din, wanda kuma hakan ya fito da masu trading cryptocurrency na spot trading bisa ilimi cewa lallai Halal suke ci, domin mun cika duka ka'idojin; muna saka kudinmu a matsayin jari, sannnan mun bata lokaci shekara da shekaru muna neman ilimi har Allah ya mana muwafaka muka iya analysing kasuwa, mu gane me ya kamata mu saya, a ina ya kamata mu saya sannan a ina ya kamata mu sayar, sannan idan mukayi analysis sai mu sayi coins da muke ganin za'a samu riba dasu, mu rikesu mu jira har lokacin da farashinsu zai tashi kuma a samu masu saya mu sayar musu a exchange (DEX ko CEX).

Bayan Malam ya gama wannan bayanin sai ya tambayi almajiransa shin akwai wannan abubuwan guda uku? sai wasu s**a ce babu, wanda hakan ya tabbatar da cewa lallai basu fahimci menene crypto trading ba da yanda yake gudana. Wannan amsa da aka baiwa malam sai ya dora akanta, cewa toh indai babu wancan abubuwa 3 toh lallai haram ne kuma bai halatta ba, har ya kawo misalai wanda suke nuna Malam ya danganta crypto da ponzi schemes da sauran dampara da akeyi da kuma get rich quick schemes.

Amma da na tsaya na fahimci su almajiran, sai na gane suna kokarin danganta lamarin da mining ne; wanda shi kuma mining ba trading bane, wani aiki kake yi ake biyanka, wanda na tabbatar idan aka yiwa Malam bayaninsa shima, da yanda yake aiki tabbas malam bazai haramtashi ba.

In sha Allah a wannan satin (Ranar Litinin mai zuwa) zan yi hira a Premier Radio 102.7 FM dake Kano da misalin 7:05pm na yamma (Magariba zuwa Isha) domin yin bayani akan menene mining da kuma bambamcinsa da crypto da trading domin abubuwa su kara fita fili.

Ga link na video din a comment domin kuma ku kara zama alkalai, idan kuma akwai kuskure a cikin rubutuna sai ku min gyara.

Nagode

Sabiu Muhammad Danpullo

23/05/2024

Over Protocol sun zo da wata Exchanger mai suna FlipSter, wanda sai kayi register da ita kayi KYC sannan kayi linking da account dinka sannan kake da possibility na samun Airdrop nasu.

Wannan matakine da s**a dauka domin tace mutanen da suke da accounts sama da daya.

A yanzu haka register da Exchange din ya tsaya saboda yawa da yan baiwa s**a masa. BUt I am sure zasu gyara kuma a cigaba da yin register as usual

Allah ya bamu nasara

22/05/2024

Assalamu alaikum wa rahmatullah!!!

Dan Allah inason yin amfani da wannan damar nayi kira da hukuma da Malamai da kuma sauran abokai da muke harkar cryptocurrency cewa a gaskiya wannan yanayin na cecekuce da ke faruwa bazai haifar mana da da mai ido a arewa ba.

Na farko wasu malamai sun saka baki a harkar cryptocurrency suna bada fatawa wanda su matasa masu harkar crypto suke ganin kamar da kuskure a ciki, Malaman basu fahimci menene cryptocurrency da yanda yake aiki ba.

Su kuma a bangaren malamai suna ganin sun san abinda suke magana akai, kawai son zuciya yasa matasa suke kin karbar gaskiyar da suke fada musu akan crypto.

Wannan zai sa mutane da yawa su raina Malamai da addini, suna yiwa addinin da malaman kallon gidadanci, su kuma malamai suna mana kallon maciya haram yan wuta.

Shawarar da zan bayar anan shine; dan Allah ko Gomnatin Kano, gari mai albarka, karkashin jagorancin majalisar Malamai, ta hada wani zama na musamman domin tattaunawa tsakanin wanda ake ganin suna da ilimi akan addini da kuma su yan cryptocurrency, ya zama kamar wata daurace ko seminar kamar ta kwana daya ko biyu. Su yan crypto su zo suyi presentation na ilimi akan menene cryptocurrency zalla kawai, su kuma malamai su sauraresu da kunnen basira da niyyar fahimtar menene shi blockchain da cryptocurrency din.

Bayan yan crypto sunyi nasu presentation din, sai a baiwa malamai damar su fito da hakkin addini da hukunce-hukuncen addini daga cikin abinda su yan crypto s**ayi presenting.

Hakan zai taimaka a ware menene mai kyau a harkar cryptocurrrency sannan menene marar kyau. Kaga daga nan za'a samu maslaha kowa ya gane dai-dai. Yan jaridu kuma su yada wannan zama domin kaiwa kowane lungu da sako.

Akwai wuraren da za'a iya yin wannan zama kuma ayi shi cikin nasara, Misali Jami'ar Bayero suna da manyan zaurukan taro irin wannnan, shi kanshi gidan gwamnatin Kano akwai hall da zai isa ayi wannan taro da ma sauran wuraren da za'a iya amfani dasu.

Sponsorship na tabbata ba matsala bane, gomnati zata iya yi, kungiyoyi zasu iya yi, mu a tsakaninmu yan crypto zamu iya contributing kudi ayi, kamfanonin blockchains da exchanges da yawa zasu iya yi.

Dan Allah idan akwai wanda yake da damar kai wannan kira ga wanda abin ya shafa ya taimaka mana mu ceto yankinmu na Arewa daga wannan rudanin.

Nagode.

Cc:

Sunusi Danjuma Ali
AUDU BULAMA BUKARTI
Abba Hikima
Nasiru Salisu Zango
Mohammed Bello Kano
Mahmoud Muh'd Sardauna
Abubakar Tanko
Al-ameen S Shuaib
Freedom Radio Nigeria
Arewa Radio 93.1

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Kano