Duniya Tana da dadi, Ga mai hankali shagaltuwa a cikinta ba namu bane idan ka tuna kwanciyar kabari da hisabi ga tsayusar dake jiranmu a gaban Allah domin yi mana hisabin irin aiyukan da muka aikata cikin wannan duniya da muke ganin kamar bazata tashi ba.
Duniya ba tabbas bace lahira itace tabbas lahira itace take dauke ta farin cikin da babu digon bakin ciki, ubangiji kasa muna cikin wanda zasu Rabauta a lahira.
Allah kayi mana kayiwa iyayenmu, yan uwanmu da sauran Al'ummar musulmi gafara 🤲🤲🤲
Sani
Jaba
SUNNONI DA LADUBBAN RANAR IDI
1️⃣ YIN WANKA KAFIN FITA SALLAH
Ya inganta a cikin Muwaɗɗa na Imamu Malik, Rahimahullah, 428, cewa: Abdullahi Ɗan Umar, Radhiyallahu anhu, ya kasance yana yin wanka kafin ya fita sallar idi.
2️⃣ CIN ABINCI KAFIN FITA IDI IDAN KARAMAR SALLAH CE DA KUMA CIN ABINCI BAYAN IDI IDAN IDIN LAYYA NE:
Hadisi ya inganta daga Anas Ɗan Malik cewa: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya kasance ba ya fita sallar idi na karamar Sallah har sai ya ci dabino kuma ya kan ci mara ne ( wato 1 ko 3 ko 5 ko 7...). Bukhari ya riwaito 953.
Duk wanda bai samu dabino ba sai ya ci daga abun da ya halasta.
Amma dangane da Idin layya an so wanda zai yi layya kar ya ci komai har sai bayan sallar idi sai ya ce daga dabbar layyan shi.
Wanda kuma bai da dabban da zai yi layya babu laifi idan ya ci abinci kafin sallar idi.
3️⃣ KABBARBARI A RANAR IDI
Ibn Abi Shaibah ya riwaito da isnadi ingantacce daga Al-Zuhriy cewa: Mutane sun kasance suna yin kabbara a ranar idi daga lokacin da s**a fito daga gidajensu har sai sun isa filin sallar idi sannan suna ci gaba da kabbarbari har sai liman ya fito... A duba Irwa'u al-Galil 2/121.
Sai dai lokacin kabbarbarin Idin karamar Sallah yana farawa ne lokacin da idi ya fara (ranar da aka ga wata) har sai liman ya fito sallar idi.
Amma kabbarbarin sallar idin layya yana farawa ne daga daya ga watan dhul-Hijjah zuwa karshen ranakun ayyamut tashreeq.
YAYA AKE KABBARBARIN?
Ya zo a Musannaf na Ibn Abi Shaibah da sanadi ingantacce daga Abdullahi Ɗan Mas'ud, Radhiyallahu anhu: ya kasance yana kabbara a cikin ayyamut tashreeq: ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LAA ILAAHA ILLAAH, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR WA LILLAAHIL HAMD. A wata ruwayar ya ce za a yi kabbara sau 3.
A wata har wayau daga Abdullahi Bn Mas'ud: ALLAHU AKBAR KABEERAN, ALLAHU AKBAR KABEERAN, ALLAHU AKBAR WA AJAL, ALLAHU AKBAR WA LILLAAHIL HAMD. A duba littafin Irwa'u al-Galil 3/126.
4️⃣ YI MA JUNA MURNA (BARKA)
Daga Jubair Bn Nufair, ya ce: Sahabban Manz
17/04/2023
LABARI CIKIN HOTUNA: Ministan bunƙasa fasahar sadarwa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami tare da shugaban Limaman Masallatan Harami dake Makkah da Madinah, Sheikh Abdurraahman SUDAIS.ماشاءاللہ
GOMAN K'ARSHE
Shin wane tanadi kake yi ma wadannan kwanaki??
Daga Ummuna Aisha Allah ya ƙara yarda a gare ta, ta ce: "Manzon Allah SAW ya kasance idan waɗannan goman s**a shigo, ya kan zage damtse, ya raya darensa, kuma ya tayar da iyalensa"
Bukhary da Muslim
11/04/2023
ANSHA RUWA LAFIYA
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Telephone
Website
Address
Jaba
Kano
SAS