JK MEDIA

JK MEDIA

Share

LABARAI DA RAHOTANNI GAMI DA NISHADANTARWA

29/04/2026

AURAN GATA
ANGO DA AMARYA (3000)

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf za ta gudanar da wani shiri na musamman na aurar da zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wato maza 1,500 da mata 1,500.

Wannan shiri ya fi karkata ne ga marayu da kuma ’ya’yan talakawa domin tallafa musu su samu rayuwa mai inganci ta hanyar aure.

Abubuwan da aka tanada ga ma’auratan sun haɗa da:
1. Kayan ɗaki: gado, sif, madubi, katifa, filo da zanin gado.
2. Kayan abinci: shinkafa, taliya, da man girki.
3. Kayan sawa ga mata: atamfa da hijabi.
4. Kayan sawa ga maza: shadda da hula.
5. Sadaki: Naira dubu ɗari (₦100,000).
6. Jari ga mata: Naira dubu ɗari (₦100,000) domin fara sana’a.

Haka kuma, za a gudanar da gwajin lafiya tare da cike takardun (forms) guda uku domin tabbatar da cewa duk wanda zai shiga shirin ya cika dukkan sharudda.

Ƙarin bayani
(Duk wanda zai shiga wannan shiri sai yana da sanaa.)

Allah ya saka wa gwamna da alkhairi, ya sanya wannan aiki ya zama alheri mai ɗorewa ga al’umma, ya kuma sa ya zama sanadin rage talauci da inganta zaman lafiya a jihar Kano.

29/04/2026

A ranar Laraba, wasu matasa da ke da alaka da Isa Ali Ibrahim Pantami sun yi wani gagarumin yunkuri na nuna godiya ga irin taimakon da ya taba yi musu a rayuwa. Wadannan matasa sun hada kai ba tare da wani ya tilasta musu ba, inda s**a kafa wani kwamiti na gaggawa domin tara kudin siyan fom din tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe a madadinsa.

Abin mamaki, cikin kwanaki biyu kacal, matasan sun samu nasarar tara sama da naira miliyan sittin (N60,000,000), kudin da ya isa har ma ya zarce farashin fom din da ake bukata. Kowane daga cikin masu bada gudummawar ya bayar ne da radin kansa, alamar kauna da girmamawa ga malamin.

Wannan mataki da matasan s**a dauka ya nuna irin tasirin da Pantami ya yi a rayuwarsu, musamman wajen taimaka musu da samar da hanyoyin inganta rayuwa. A ranar Laraba din ne wasu daga cikin wakilan matasan s**a je wajen sayar da fom din, inda s**a cika burinsu na siyan fom din kamar yadda s**a kudiri aniya.

Hakan ya kara jaddada yadda dangantaka tsakanin jagora da mabiyansa ke haifar da hadin kai da godiya a aikace.

28/02/2026

KASAR OMAN TAYI MUBAYA'A GA lRAN

Ministan harkokin wajen ƙasar Oman, wanda ke shiga tsakani a tattaunawar tsakanin Amurka da Iran, ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki.

Ya ce yana kira ga Amurka da kada ta ƙara shiga wannan rikici, yana mai jaddada cewa: “Wannan ba yaƙinku ba ne.”

Global eye

02/02/2026

RASUWAR SHEIKH USMAN KUSFA ZARIA

Allah ya yi wa fitaccen malamin addini Sheikh Usman Kusfa Zaria (Rigi-rigi) rasuwa.

Rasuwar ta tabbata daga iyalansa da makusantansa, bayan jinya da ya sha fama da ita.

Sheikh Usman Kusfa ya shahara wajen wa’azi da koyar da addini, inda ya ba da gudummawa sosai wajen wayar da kan al’umma.

Muna roƙon Allah ya gafarta masa, ya sanya Aljanna Firdausi ce makomarsa. 🤲
JK Media

21/01/2026

Gwamna Abba Ya Yi Ta’aziyyar Iyalin da Aka Kashe su 7

21/01/2026

Gwamna Abba Ya Yi Ta’aziyyar Iyalin da Aka Kashe su 7

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ziyarci iyalin da aka yi wa kisan gilla su bakwai, inda ya bukaci a gaggauta gurfanar da wadanda ake zargi.

Ya kuma bai wa mahaifinsu kujerar Hajji, tare da alkawarin gina masallaci da kuma ba shi gida.

JK Media

21/01/2026

‘Yan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 1.54 Kan Giya

Rahoto ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun kashe sama da Naira Tiriliyan 1.54 kan giya da sauran abubuwan sha a cikin watanni 9 na shekarar 2025.

Bayanan sun fito ne daga rahotannin kuɗaɗen shiga na:
Nigerian Breweries Plc, International Breweries Plc, da Champion Breweries Plc.

Duk da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki, kasuwar giya na ci gaba da bunƙasa.

Nigerian Breweries Plc ce ta fi kowa samun riba, inda ta tara sama da Naira Tiriliyan 1 ita kaɗai.

JK Media

16/01/2026

Kotu a Kano Ta Wanke Amaryar da Ake Zarginta da aikata kisa.

Kotu a Kano ta sallami Fatima Dahiru, amaryar da ake zargi da kashe uwargida a unguwar Farawa, bayan rashin isassun hujjoji daga ɓangaren masu gabatar da ƙara.

Shari’ar wadda ta shafe shekaru tana gudana ta ƙare ne da wankewa da sallamar wadda ake tuhuma.

14/01/2026

Sanarwa: Rasuwar Wani Bawan Allah a Hatsarin Mota

Inna lillahi wa inna ilayhi rajiʿun.
Wani bawan Allah ya rasu sakamakon hatsarin mota da ya same shi a Kwanar Dangora. A lokacin da lamarin ya faru, ba a samu wata waya a tare da shi ba.

A halin yanzu, gawar marigayin tana Cottage Hospital Kwanar Dangora, kusa da Police Station, yayin da ake neman ‘yan uwansa domin su zo su karɓi gawar a yi masa jana’iza.

Duk wanda ya san marigayin ko ‘yan uwansa, ana roƙon sa ya sanar da su.
Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.

13/01/2026

GWAMNATIN KANO TA DAKATAR DA MA’AIKATA UKU KAN MUTUWAR MARA LAFIYA.

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da ma’aikata uku a Asibitin Abubakar Imam Urology Center, biyo bayan mutuwar Aisha Umar, sakamakon zargin sakaci yayin yi mata aiki inda aka ce an manta almakashi a cikinta.

Sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Kula da Asibitoci, Samira Suleiman, ta fitar a ranar Talata 13 ga Janairu, 2026, ta tabbatar da cewa Shugaban Hukumar, Mansur Mudi Nagoda, ya bayar da umarnin dakatarwar tare da miƙa lamarin ga Kwamitin Ɗa’ar Aikin Lafiya domin ƙarin bincike.

13/01/2026
Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Kano