Nafisat Adamu

Nafisat Adamu

Share

DAGA ANNABI GIRMA YA KARE!

14/05/2026

Wata rana haka gidajen mu zasu zama tarihi abin nunawa a hotuna, lokacin bamu a raye muna can muna girbin abinda muka shuka! ya ubangiji kayi mana gafara da rahamar ka...🥺🥺

14/05/2026

tabbas mallam 👌👌

05/05/2026

Wanda ya kwana lapia ....!?👌🏌️

24/04/2026

An labarto cewa wannan mutumin dake wannan hoto sunan shi Ahmad Abdullah, ƙwararre ne a harkan magani dake aiki a wani wajen sayar da magani....

Kowani wata wata Dattijuwa takan zo gareshi domin sayan maganin ta. Zata tarar dashi akan teburin da ake biyan kuɗi, duk lokacin da ta ganshi, sai fuskar ta ta cika da annuri na farin ciki, shekaru kusan uku haka yake faruwa, idan dai tazo shi sai dai ya karɓi fam 200 na kuɗin Egypt ya Bata magani.

Ana nan sai wannan bawan Allah ya mutu, matar sai ta zagayo a ƙarshen wata kamar yadda ta saba, ta nemi maganin ta, taje teburin biyan kuɗin domin ta biya 200 kamar yadda ta saba.... Amma kuma sai bata same shi ba... Kafin ma ta buɗi baki ta tambayi Ina yake, sai sabon wanda ke karɓan kuɗi yace da ita: "Malama meye wannan wai?" Sai tace dashi: "kuɗin magani mana". Sai yace da ita: "Ae kuɗin ta 2000 ne ba 200 ba"

Cikin mamaki sai tace: "Amma sama da shekaru 3 haka nake saya 200 daga wajen wani matashi dake aiki anan kafin kai..... ko yana ina?"..

Sai sabon cashier yace da ita: "Allah ya mishi rasuwa"

Da aka duba cikin record sai aka tarar cewa wannan bawan Allah ya kasance yana cika mata 1800 daga cikin albashin shi a kowane wata

A yayin da mai shagon maganin ya gano hakan, shima sai ya yanke hukuncin kan cewa aci gaba da bata magani a wannan farashin a matsayin sadaqatuj jariya ga wanaan matashin da ya rasu..🥺

Ya Ubangiji Ka bamu zuciyar taimakon bayin ka, ka ƙara mana wadatar zuciya data aljihu albarkacin Muhammadur Rasoulullah sallallahu alaihi wasallam

14/04/2026

Shugaban da bashi da na biyu (s.a.w)

12/04/2026

Barkanmu da safiya....🕊️💕

07/04/2026

Wannan shine gaskiyar magana!👌🕊️

30/03/2026

IRAN FA A SHIRYE TAKE!👌👌

Jiya jiyan nan Amurka da Izra@ila s**a kai mummunan farmaki akan wasu tashoshin samar da lantarki na Iran wanda hakan ya janyo daukewar lantarki a wasu sassa na birnin Tehran da Alborz tare da wasu manyan birane na Iran...

Amma da yake suna da shugabanni masu kishi da azama tun a daren jiya injiniyoyin kasar Iran s**a gyara lantarkin, zuwa safiyar yau duk biranen da s**a rasa lantarki sun dawo samu....

Mu kuwa a Nigeria ba yaki muke ba, amma lantarkin ya gagari kaso maiyawa na al'ummar Nigeria duk da tarin kudaden da ake cewa ana warewa harkar lantarkin...

To Allah ya kyauta...

22/03/2026

Day-03 Eid Mubarak 👌

21/03/2026

Kamar yadda rahoto na MME ya bayyana, Saudi Arabia ta amince da buɗe King Fahad Air Base dake Taif ga ƙasar Amurka domin ci gaba da yaƙi da ƙasar Iran 🇮🇷..

Idan haka ya faru fa, ƙasar Saudi ta nuna goyon bayan ta sosai kenan ga ƙasar Isr@'ila da Amurka.

Babban tashin hankalin ma shine wannan waje da zasu bawa Amurka ɗin kusa yake da makkah, bai wuce 70km ba...!

A wurgo abu kuma wasu s**e wai ana so a yaƙi Saudiyya ko?

Allah yasa mu wanye lafiya kawai...🙏🥺

21/03/2026

Iran ta sanar da cewa Amurka karya takeyi akan man fetur din da tace Iran tana dashi a cikin jiragen ruwa wanda wai yawansa yakai lita miliyan dari da hamsin, wannan babbar karya ce da yaudara inji Iran...

Amurka tayi wannan yaudarar ne da niyyar bawa yan kasuwa kwarin gwiwar da man fetur zai dena tashi...

Iran ba zata siyar da man fetur ga ƙasashen da s**a gujeta a baya akan Amurka, zata siyar ne ga kasashen irinsu China wanda dama dasu take mu'amala tuntuni...

Yan kasuwar man fetur na duniya ku sani Amurka karya take muku ba wani man fetur da zan siyar....

Muna nan akan batun da mukayi na cewa sai gangar ɗanyen man fetur ta haura dolar dari biyu kowacce guda daya....

Want your school to be the top-listed School/college in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kano Nigerian
Abuja