Jibwis Tarauni

Jibwis Tarauni

Share

Wannan shafin Mallakin Ƙungiyar Jamaatu Izalatil Bidah Wa iqamatis Sunnah be rashe ƙaramar Hukumar Tarauni.

An samar da shafin ne don yaɗa karattukan malamai na cikin ƙaramar Hukumar da wajenta.

21/01/2026

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir,

Shugaban Kungiyar Jama'tu Izalatil Bid'ah Wa iqamatis Sunnah na karamar Hukumar Tarauni Mal. Yunusa M. Gidado da Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Dr. Muhammad sani Umar (ARQAM) da Shugaban Majalisar Agaji Mal. Zaharaddeen Isah, na mika saqon Ta'aziya ga Shugaban Kungiya na Kasa Sheikh Abdullahi Balalau da Shugaban Kungiya na Jihar Kano Sheikh Prof. Abdullahi Saleh Pakistan da sauran mambobin kungiya da Al'umman Musulmi baki daya, bisa babban rashin Shehin Malami Sheikh Habibu Yahaya Kaura.

Muna Addu'a Allah ya jikan Mallam ya Gafarta masa kurakuransa, Allah ya haskaka makwancinsa Ya kuma sanya Aljannah makoma gareshi.

Iyalai da 'yan Uwa Allah ya bamu hakurin jure rashin

إن لله ما اخذ وله ما أعطى وكل شي عنده بأجل مسمى فلتصبر و لتحتسب

✍️ Jibwis Tarauni

21/01/2026

Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji‘ūn

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Ƙasa, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau,
yana sanar da dukkan ‘yan uwa Musulmi da mambobin Kungiyar JIBWIS rasuwar:

Sheikh Habibu Yahaya Kaura
Shugaban Working Committee na Kungiyar JIBWIS ta Ƙasa, wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya karɓi rayuwarshi bayan jinya da yayi fama da ita.

Za a gabatar da Sallar Jana’iza da misalin karfe 4:30 na yamma, a Hedikwatar Kungiyar JIBWIS,
Utako Bega Junction, Abuja.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, kuma Ya ba iyalansa, ‘yan uwa da al’ummar Musulmi haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

JIBWIS Nigeria.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Hausawa 'Yan Dillalai Street
Kano