05/01/2026
Nanne majalisar dinkin duniya
This page created for only English .
05/01/2026
Nanne majalisar dinkin duniya
Forgive others not because they asked for it, but because your heart deserves to be free, and your scale needs the weight of mercy.
PI NETWORK YAUSHE NE ZA TA FASHE?
KASHI NA 3
MAI JIRAN GAWON SHANU
Pi Network ya zo da mataki huɗu na membobi. Duk wanda ya shiga a karon farko sunansa Pioneer. Idan ya girma zai zama Contributor. Daga nan zai koma Ambassador. Mataki na ƙarshe shi ne Node. Duk wanda ka ji yana kiransa kansa Pioneer, to ya ɗauka shi ya-ku-bayi ne, ba shi cas ba shi da as. Node kuwa, har zuwa yau ba su wuce su dubu 120 ba a cikin mutane miliyan 35 da ɗoriya.
Irin wannan matakai fa, irinsu ne a tsarin kasuwancin nan da aka laƙabawa suna MLM watau tsoma ɗari ka zare biyar, sauran kuma ka bar su cikin ruwa.
Cem ya ƙara da cewa, "kullum zancensu shi ne sai an kai adadi kaza amma har yau s**an ba da wani uzuri da ya hana su motsawa. Suna sane sarai, duk ranar da s**a bada umarnin a yi cinikayya da tsabobin Pi, to daga ranar komai zai dagule."
Kenan a yanzu komai na tafiya daidai bai dagule ba. Haka yake. Domin kuwa wani ɗan Kirifto da ya kira kansa DanseMap na ganin cewar su Nikolas na cin duniyar su da tsinke daga albarkacin manhajarsu ta Pi wadda a kullum ake samun miliyoyin mutane suna kai mata ziyara. Wanda hakan ke ba su damar samu daga tallace - tallacen google.
Wani abu kuma da ke nuna cewar har yanzu jiran gawon shanu muke yi, masana Kirifto na ganin cewar shi harkar Kirifto ba wai adadin mutane ne ke nuna ƙarfinsa ba, illa dai ƙarfin fasahar da aka yi amfani da ita da kuma na'urorin da ke sarrafa shi. Idan ka ɗauki limamin kirifto karansi watau Bitcoin, akwai na'urorin node aƙalla dubu 100 da a kullum suke tasarrrafin lissafin da ya kai zambar dubu sau dubu sau dubu sau dubu ɗari!
Kai ɗan adam Pioneer, ina za ka iya wannan lissafi haka?
Mafi yawan waɗanda s**a yi imani da fashewar Pi na cewar imma dai mutum ba shi da ilmin kirifto ko kuma hassada ke damunsa.
Akan hakan Mista Cem ya bayyana cewa, "... kamar ni, tun 2017 nake aiki da kuma bincike akan kirifto." An nuna cewar Cem ya yi rubutu kusan guda 635 akan kimiyya da fasahar zamani ciki har da kirifto karansi.
Hakan
PI NETWORK: YAUSHE NE ZA TA FASHE?
Abu biyu ya sa ake kauda kai dangane da ikirarin fasahar Pi Network wadda wasu Hausawa 'yan kirifto ke ta hankoron 'ZA TA FASHE'.
Dalili na farko, waɗanda s**a ƙirƙiro fasahar malaman jami'a ne masu bincike da ƙoƙarin sarrafa labari zuwa zahiri. Jami'a ita ce cibiyar bincike da nazari da ƙirƙiro fasaha da tabbatar da ilimi. Kusan duk wani cigaban intanet da aka samu zuwa yanzu, ya samo asali daga malaman jami'a. Don haka tun a 2019 da malaman da s**a haɗa da Dr Nicolas Kokkalis da Dr. Vincent McPhillip da kuma Dr. Dr Chengdiao Fan s**a soma wannan aiki, nan da nan jama'a s**a yi amanna. Sai dai wani malaminsu Farfesa Crispus Nyaga yana cewa, shirin nasu 'Ta gina bata shiga ba ne.'
Dalili na biyu kuma shi ne, ba a nemi ko kwabo daga hannun jama'a ba, duk wanda zai shiga tsarin kyauta zai shiga, aikinsa kurum yayi ta latsa wani abu duk bayan awa 24 domin ya cigaba da zabari.
Shi dai Pi Network, ya samu ne a ƙarƙashin cibiyar bincike ta StartX wadda manyan kamfanonin duniya ke tallafawa. Shirin na ɗaya daga cikin shirye-shirye sama da 700 da cibiyar ta samar. Ya zuwa yanzu an ce akwai mutane kimanin miliyan 35 da ke ta zabari tare da tsammanin wa rabbuka. Nima ina ɗaya daga cikinsu. Na tara kimanin Pi 600 da ɗoriya. A ɗayan akawun ɗin da ya salwanta kuma ina da Pi dubu 5 da ɗoriya.
Tun a farkon shekarar 2021 ake sa ran za ta farfashe kowa ya sakata ya wala, amma har yanzu shiru.
Shin a ina gizo ke saƙar ne? Me ya sa har yanzu muke zaman jiran gawon shanu muna ta hasashe tare rubuta wasiƙar bilhu?
Mu haɗu a rubutu na gaba.
Danladi Z. Haruna.
PI NETWORK: YAUSHE NE ZA TA FASHE?
KASHI NA BIYU
Tun a farkon shekara ta 2020 ake ta hasashen za a soma aiki da Pi a matsayin kuɗin intanet, wannan ta sa wasu ɗaliban Malam Nikolas musamman na ƙasashen Asiya, s**a yi awon gaba suke ta buɗe kantuna da sunan Pi Mall inda aka ce suna saye da sayarwa ta amfani da kuɗin Pi.
Da alama wannan abu yayi wa malamin daɗi, don haka ya ja wasu d
28/06/2022
25/06/2022
RAN SARKI Y DADE
Jiya aka daura auren budurwata natafi zan kashe kaina yan fashi s**a biyoni zasu kasheni.