15/09/2022
PI NETWORK YAUSHE NE ZA TA FASHE?
KASHI NA 3
MAI JIRAN GAWON SHANU
Pi Network ya zo da mataki huɗu na membobi. Duk wanda ya shiga a karon farko sunansa Pioneer. Idan ya girma zai zama Contributor. Daga nan zai koma Ambassador. Mataki na ƙarshe shi ne Node. Duk wanda ka ji yana kiransa kansa Pioneer, to ya ɗauka shi ya-ku-bayi ne, ba shi cas ba shi da as. Node kuwa, har zuwa yau ba su wuce su dubu 120 ba a cikin mutane miliyan 35 da ɗoriya.
Irin wannan matakai fa, irinsu ne a tsarin kasuwancin nan da aka laƙabawa suna MLM watau tsoma ɗari ka zare biyar, sauran kuma ka bar su cikin ruwa.
Cem ya ƙara da cewa, "kullum zancensu shi ne sai an kai adadi kaza amma har yau s**an ba da wani uzuri da ya hana su motsawa. Suna sane sarai, duk ranar da s**a bada umarnin a yi cinikayya da tsabobin Pi, to daga ranar komai zai dagule."
Kenan a yanzu komai na tafiya daidai bai dagule ba. Haka yake. Domin kuwa wani ɗan Kirifto da ya kira kansa DanseMap na ganin cewar su Nikolas na cin duniyar su da tsinke daga albarkacin manhajarsu ta Pi wadda a kullum ake samun miliyoyin mutane suna kai mata ziyara. Wanda hakan ke ba su damar samu daga tallace - tallacen google.
Wani abu kuma da ke nuna cewar har yanzu jiran gawon shanu muke yi, masana Kirifto na ganin cewar shi harkar Kirifto ba wai adadin mutane ne ke nuna ƙarfinsa ba, illa dai ƙarfin fasahar da aka yi amfani da ita da kuma na'urorin da ke sarrafa shi. Idan ka ɗauki limamin kirifto karansi watau Bitcoin, akwai na'urorin node aƙalla dubu 100 da a kullum suke tasarrrafin lissafin da ya kai zambar dubu sau dubu sau dubu sau dubu ɗari!
Kai ɗan adam Pioneer, ina za ka iya wannan lissafi haka?
Mafi yawan waɗanda s**a yi imani da fashewar Pi na cewar imma dai mutum ba shi da ilmin kirifto ko kuma hassada ke damunsa.
Akan hakan Mista Cem ya bayyana cewa, "... kamar ni, tun 2017 nake aiki da kuma bincike akan kirifto." An nuna cewar Cem ya yi rubutu kusan guda 635 akan kimiyya da fasahar zamani ciki har da kirifto karansi.
Hakan