30/08/2025
WAAZIN KASA DA KASA....
Shin Wannan Waazin Ya Samo Asaline Daga Manzan Allah Ko Shima Bidia ne? Naga Yan Kungiya Sun Mayar da Abin Kamar Addini Suna Ririta Abin Saboda Ana Samun Kudin Shiga A wajan Gwamnati.
Abinda Nakeso Kowa Yagane Shine Mutanannan Makaryatane. Inkaji Suna Zagin Abu To Kudinka Zaka Kashe Kayi Hidma Amma Indai Kudi Zaa Samu To Tabbas Wannan Harkar Sune Akan Gaba.
29/08/2025
NASIHA TARE DA JAN HANKALI.....
Ina Kira Ga Sha'iranmu Musamman Mata A wannan Lokaci Na Maulidi Su Kasance Suna Zuwa duk Inda Zasuje da Shiga Ta Kamala Wacce Ana Ganinsu Ansan Cewa Masoya Annabi S.a.w ne Ba Abokan Shedan ba, Saboda Tabbas Masu Kallo A Wajan Sune Zasu Shaida Ke Wacce ce daga Ciki.
Karki Tawo Tu6ai Tu6ai dake Ragaje Ragaje Ana Ganin Surar Jikinki Kice Ke Sayyidace , Sayyidar Shedan dai Domin Tabbas Wannan Shigar Taki Zata Iya Sakawa Mutane Shakku Akan Soyayyarki Saboda Baki Zama Kamila ba B***e Har Ki Zama Sayyida.
Ku Kuma Shairai Maza Idan Kunzo Kunga Ana Bayani Kuma Ku Tsaya Ku Saurara Kudaina Cewa Kunada Uziri Agabatar daku Saboda Shima Wanda Ya Rigaku ai Yanada Nashi Uzirin.
Ko Kuma Kuzo Kunawa Shehunai Da Mallamai Ganin Hadarin Kaji Kuna jin Kuma ai Wasune , Yana Dakyau Duk A Gyara, Ko Kuma Waje Yana Nutse Kuzo Ku Hargitsashi.
Sannan Muma Yan Kallo Muna Samun Nutsuwa Saboda Wallahi Maulidi Babbar Makarantace Wacce Ake Samun Ilmi Mai Yawan Gaske Wanda Zaka Dade A Karatu Bakazo Wajanba, Tabbas Maulidi Makaranta ce Amma Ga Wanda Ya Nutsu Ya Saurari Malamai.
Allah Yabamu Dacewa Ya Kara Mana Soyayya.
Allah Ya Horewa Kowa Abin Hidima Albarkacin Annabi Muhammadu S.a.w
Bilal Auwal Sulaiman ✍
20/08/2025
Na yi manyan laifuka da s**a ɓata ran bayin Allah, s**a fusata su. Idan na tuna, nakan ji na tsani kaina, na tsani rayuwata, har na ga kamar ba ni da wani amfani a cikin duniyar nan.
Na fi kowa cancantar azabar Allah a cikin al'umma – saboda miyagun ayyukan da na aikata waɗanda s**a sa muminai s**a fusata da ni. Amma duk da haka, ina fatan samun gafarar Allah da bayinsa managarta. Na san Allah bai halicceni domin ya azabtar da ni ba, manufarsa a kaina rahama ce. Idan laifukana sun cika sama da ƙasa, rahamarsa gareni ta yi yawan da bazai misaltu ba.
Mai karatu, idan na taɓa cutar da kai ko na yi maka laifi, ka gafarta min, ka yafeni. Na san kai ba za ka so ka ganni cikin azabar Allah ba. 🙏
02/02/2024
Allah Ya Jaddada Rahama Agareka Babana Abin Alfaharina.😭