11/03/2023
Kai daga ganin Fuskokin da suke cikin wannan Fim ɗin mai dogon Zango mai suna (Manyan Mata) kasan cewa ba karamin Shiri s**a yi ba, kuma ba karamin Kuɗi s**a Tanada ba domin cimma Burin su.
Acikin Fuskokin da na gani a kwai Jarimar da ta fada da bakin ta cewa, bazata iya fitowa a fim ba, matukar ba a Bata kudi sama da Miliyan Daya ba, kuma ku duba Sauran manyan Jaruman maza, ta nan zaku gane cewa Akwai Lauje cikin Naɗi, kuma Dole Bazasu fita daga Zargi ba cewa Kwangila aka basu domin Su yi wa Harkar Almajiranci Zagon ƙasa.
Kuma zakuga Akwai Manyan Jarumai Wadanda an dade ba'a gan su a cikin Fim ba, hakan yake nuna ba karamin Kudi aka basu ba domin fitowa a wannan Fim din....
Idan kun Lura da kyau ba iya harkar Almajirai suke yi wa Zagon ƙasa ba, har da Zamantakewar Auratayya a kasar Hausa. Wanda hakan zai iya zama barazana a Zamantakewar Aure. Da kuma Lalata Tarbiyya da Raina Iyaye.
Kusan duk abin da s**a nuna a wannan Fim ɗin da ya shafi Almajiranci, ba su yi Karatun ta Nutsu ba, kuma ba su yi Binkice ba, sannan basu zauna da Ahlin Tsangaya ba domin su ji ta bakinsu. Kawai sun yi gaban kansu ne domin cimma wata Mummunanr Manufa tasu ta sawa Al'ummar Hausawa Ƙyamar Tsarin Almajiranci, kuma In Sha Allahu Burin su bazai taba cika ba, domin tun kafin su zo duniya ake yaƙar wannan tsarin Allah Ya na kare shi, kuma yanzu ma Allah zai kare mu daga duk wani Sharrin mai Sharri.
Yana da kyau Gwamnati da Malaman Addini su saka ido a kan wannan Fim ɗin, idan da dama a dakatar dasu..
Mu a Bangaren mu Yan Uwa Almajirai muna Tattaunawa a kan Matakin da zamu ɗauka.
Allah Ya bamu Nasara.
Yasir Gwani Badamasi (P.r.o.)