02/09/2026
Duk wanda yake rashin lafiya kowace iri ce; ko yake da wata buƙata, ko kuma yake cikin damuwa yake burin Allah ya yaye masa; to ya riƙi sallar dare.
Annabi Alaihissalam ya faɗa cewa sallar dare al’adar mutanen kirki ce, sannan maganin cutukan jiki ne.
Ko raka’a nawa mutum yake son yi zai iya, amma duk sanda yayi raka’a biyu sai yayi sallama sannan ya cigaba.
Amma idan san samu ne; mutum yayi raka’ar da zai dinga iyayi kullum, kada ya ɗebo raka’a masu yawa ya zo kuma ya dinga kasawa.