19/02/2026
NAFILOLIN MANZON ALLAH SAW
وعَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّه عنْهَا ، أَنَّ النَّبِيَّ ﷺ كانَ إِذا لَمْ يُصَلِّ أَرْبعاً قبْلَ الظهْرِ، صَلاَّهُنَّ بعْدَها .
رَوَاهُ الترمذيُّ وَقَالَ : حديثٌ حسنٌ
An karbo daga Aisha RA tace,manzon Allah SAW yakasanve idan bayi raka'a huɗu kafin sallar Azahar ba,yana yinsu bayanta.
Turmuz yace hadisine ingantacce.
وَعَنها قالتْ : كانَ النبيُّ ﷺ يُصَليِّ في بَيْتي قَبْلَ الظُّهْر أَرْبَعاً ، ثم يخْرُجُ فَيُصليِّ بِالنَّاسِ ، ثُمَّ يدخُلُ فَيُصَليِّ رَكْعَتَينْ ، وَكانَ يُصليِّ بِالنَّاسِ المَغْرِب ، ثُمَّ يَدْخُلُ بيتي فَيُصليِّ رَكْعَتْينِ ، وَيُصَليِّ بِالنَّاسِ العِشاءَ ، وَيدْخُلُ بَيْتي فَيُصليِّ ركْعَتَيْنِ . رواه مسلم .
Daga Nana Aisha RA tace:manzon Allah SAW ya kasance yana raka'a huɗu a gidana kafin sallar azahar,sannan ya fita yayiwa mutane sallab,sannan ya shigo yayi raka'a biyu,ya kasance yana yiwa mutane sallar magariba,sannan ya shigo gidana sannan yayi sallah raka'a biyu,sannan yayiwa mutane sallar isha,sannan ya shigo gidana yayi raka'a biyu. Muslim ya rawaito
عنْ عليِّ بنِ أَبي طَالبٍ رضي اللَّه عنْهُ ، قالَ : كانَ النَّبي ﷺ يُصلِّي قَبْلَ العَصْرِ أَرْبَعَ رَكعَاتٍ ، يَفْصِلُ بَيْنَهُنَّ بِالتَّسْليمِ عَلى الملائِكَةِ المقربِينَ ، وَمَنْ تبِعَهُمْ مِنَ المسْلِمِين وَالمؤمِنِينَ . رواه الترمذي وقالَ : حديثٌ حسنٌ .
An karbo daga Aliyu bin Ɗalib RA yace:manzon Allah SAW ya kasance yanayin sallah kafin la'asar raka'a hudu,sannan ya rarrabe a tsakaninsu da sallama akan mala'iku nakusa,da wanda s**a bisu musulmai da muminai. Turmizi ya rawaito kuma yace hadisine hassan.
وعَن ابن عُمَرَ رَضِيَ اللَّه عنْهُمَا ، عنِ النَّبيِّ ﷺ ، قالَ : « رَحِمَ اللَّه امْرَءاً صلَّى قبْلَ العَصْرِ أَرْبعاً » .
رَوَاه أبو داود ، والترمذي وقالَ : حديثٌ حَسَنٌ .
An karbo daga ibn Umar RA,daga manzon Allah SAW yace:(Allah ya gafartawa mutumin da yayi sallah kafin la'asar raka'a huɗu".
Abu Dawud ya rawaito da turmizi yace hadisine hassan.
وعنْ عليِّ بن أَبي طالبٍ ، رَضِيَ اللَّه عنهُ ، أَنَّ النبيَّ ﷺ كانَ يُصَلِّي قَبْلَ العَصرِ رَكْعَتَيْنِ .
رَوَاه أبو داود بإسناد صحيح .
An karbo daga Aliyu bin Abi Ɗalib RA,manzon Allah SAW ya kasance yanayin sallah kafin la'asar raka'a biyu.
Abu Dawud ya rawaito da sanadi inganyacce
وَعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مُغَفَّلٍ رَضِيَ اللَّه عنهُ ، عَنِ النَّبيِّ ﷺ قالَ : «صَلُّوا قَبلَ المَغرِب » قَالَ في الثَّالثَةِ : « لمَنْ شَاءَ » رواه البخاريُّ .
An karbo daga Abdullahi bin Mugaffal RA,daga manzon Allah SAW yace:"kuyi sallah kafin sallar magariba" yace ana uku:"ga wanda yaso". Bukhairi ya rawaito...
وعن أَنسٍ رَضيَ اللَّه عَنْه قالَ :كُنَّا نُصَلِّي عَلى عَهدِ رسولِ اللَّهِ ﷺ رَكعَتيْنِ بعدَ غُروبِ الشَّمْس قَبلَ المَغربِ ، فقيلَ : أَكانَ رسولُ اللَّهِ ﷺ صَلاَّهُمَا ؟ قال : كانَ يَرانَا نُصَلِّيهِمَا فَلَمْ يَأْمُرْنَا وَلَمْ يَنْهَنا . رَوَاه مُسْلِمٌ .
An karbo daga Anas RA yace:mun kasance munayin sallah a zamanin manzon Allah SAW raka'a biyu bayan faduwar rana kafin magariba,sai akace:shin manzon Allah SAW yana sallatarsu? Sai yace: ya kasance yana ganinmu muna sallatarta bai umarcemuba kuma bai hanamuba". Muslim ya rawaito
وعن أَنسٍ رَضيَ اللَّه عَنْه قالَ : لَقَدْ رَأَيْتُ كِبارَ أَصحابِ رسولِ اللَّهِ ﷺ يَبْتَدِرُونَ السَّوَارِيَ عندَ المغربِ . رواه البخاري
An karbo daga Anas RA yace:"yaga manya manyan sahabban manzon Allah SAW suna gaggawar samun ginshiƙi a lokacin sallar magariba". Bukhairi ya rawaito
وعنه قَالَ : كُنَّا بِالمَدِينَةِ فإِذا أَذَّنَ المُؤَذِّنُ لِصَلاةِ المَغرِبِ ، ابْتَدَرُوا السَّوَارِيَ ، فَرَكَعُوا رَكعَتْين ، حَتى إنَّ الرَّجُلَ الغَرِيبَ ليَدخُلُ المَسجدَِ فَيَحْسَبُ أَنَّ الصَّلاةَ قدْ صُلِّيتْ من كَثرَةِ مَنْ يُصَلِّيهِما . رَوَاهُ مُسْلِمٌ .
Daga gareshi yace:"mun kasance a madina idan mai kiran sallah ya kira dan yin sallar magariba,suna gaggawar samun ginshiƙai,suyi salla raka'a biyu,har sai in mutum baƙo ya shigo masallaci sai yayi zatan anyi sallah(magariba)saboda yawan masu sallah". Musulim ya rawaito
فيهِ حديثُ ابنِ عُمَرَ السَّابقُ : صَلَّيْتُ مَعَ النَّبِيِّ ﷺ رَكعَتَينِ بَعْدَ العِشَاءِ ، وحديثُ عبدِ اللَّهِ بنِ مُغَفَّل : « بَيْنَ كلِّ أَذَانيْنِ صَلاةٌ » متفقٌ عليه . كما سبَقَ .
Daga cikin hadisin Ibn Umar daya gabata:nayi sallah tareda manzon Allah SAW raka'a biyu bayan sallar isha,daga hadisin bin Mugaffal:"a tsakanin kowane kiran sallah guda biyu sallah". Muttafaƙun alaihi.kamar yanda yazo a baya..
~Safiyya Sani Abdullahi✍️