22/12/2023
*Mu'ujuzar al-Qur'ani*
Idan ka lura zaka ga acikin Al-qur'ani akwai wata Surah sunan ta "Suratun Nuwh", Surar annabi Nuhu, idan ka lura itace Surah ta 71, sannan zaka ga tana da ayoyi guda 28, bari mu ga wasu abubuwa guda biyar acikin wannan Surar.
Suratun Nuhu itace surah ta 71, tana da ayoyi 28.
Saba'in da 'daya a kwashe 28?
71-28 = 43
Zai baka 43, wannan lamba 43, shine adadin yawan sunan annabi Nuhu dake cikin Al-qur'ani gaba daya, an kira sunan "Nuhu" sau 43.
Abu na biyu, idan ka lura zaka ga cewa daga Suratun Nuhu zuwa 'kasa, zuwa 'karshen Al-qur'ani (Suratun Nass) zaka ga akwai surori 43 ne dai dai.
Abu na uku, Suratun Nuhu tana da ayoyi 28, acikin Al-qur'ani kuma Surori guda 28 ne dai dai s**a ambaci sunan "Nuhu".
Abu na hudu, idan ka koma suratul Ankabut a ayah ta 14, zaka ga Allah yana cewa "Hakika mun tura annabi Nuhu zuwa ga mutanen sa, sai ya zauna acikin su shekaru dubu daya ba hamsin (shekaru 950) kenan.
Idan ka koma Suratun Nuhu zaka Surar tana da haruffa guda 950 dai dai idan ka cire sunan Nuhu guda daya dake farkon Surar.
Abu na biyar, idan kaje aya ta farko a Suratun Nuhu, zakaga ayar tana da haruffa guda 49 ne:
Da farko mun ga cewa sunan annabi Nuhu yazo sau 43 acikin Al-qur'ani, toh tunda ayah ta farko tana haruffa 49, sai muce 49 a kwashe 43 zai baka saura 6.
Toh aya ta biyu a Suratun Nuhu tana da kalmomi 6.
Wannan iyakan abinda Allah ya banu ikon bincikowa kenan na Mathematical Miracle na Al-qur'ani a Suratun Nuhu, wata rana zamu sake komawa kan Surar in sha Allah, zamu gano wasu abubuwan da a yanzu Allah bai nuna mana ba.
"Ka gaya musu da ace mutane da Aljanu zasu hadu domin suzo da wani Littafi irin wannan al-Qur'anin ba zasu su iya ba, koda sashen su yana taimaka sashe".