27/07/2021
UNGOGO TECHNICAL OLD BOYS ASSOCIATION (UNTOBA) CLASS 2016
A jiya Lahadi 25th July, 2021 ne wannan mai Albarka ta gudanar da taron shekara shekara data saba gudanarwa tare da zabar shugabannin kungiyar.
Taron ya samu halartar dibbin tsofaffin Daliban daga bangarori da dama na ciki da wajen Jihar Kano don sada zumunci.
An gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da annushuwa, sannan an tattauna muhimman batutuwa game da cigaban kungiyar tare da makarantar.
An kuma gabatarda kunshin shugabanni da aka zaba da zasu jagoranci shugabancin kungiyar.
An gabatar da Comr. Muhammad Bello Abdullahi a matsayin shugaban kungiyar sai mataimakinsa Comr. Umar Muhammad, sai Comr. Abdulmumin Usman a matsayin Magatakarda, Comr. Yusif Auwal a matsayin Ma'aji na daya, Comr. Mustapha Baffariya a matsayin Ma'aji na biyu. Cikin kunshin shugabannin akwai Comr. Murtala Garba Sa'id a matsayin shugaban jami'in hulda da Jama'a na daya da dai sauran su.
Da yake Jawabi shugaban kungiyar na rikon kwarya Comr. Muhammad Bello Abdullahi yayi kira ga daukacin shugabanni dasu bada hadinkai wajen samar da cigaba a cikin wannan kungiya.
Daga karshe yayi kira ga membobin wannan kungiya dasu bada hadinkai wajen samar da cigaban wannan kungiya mai Albarka sannan yayi Addu'ar fatan Alkhairi ga shugabannin tare da fatan Alkhairi yayi Jagora wajen sauke nauyin da yake kansu.
Sannan a yayin taron an umarci Comr. Mustapha Baffariya da yayi karin haske game da irin cigaban da wannan kungiya ta samu a fannin hanyoyinta na sada zumuntar zamani kasancewar yana daya daga cikin membobin kwamitin (Media and Publicity) inda ya bayyana cewa tabbas wannan kungiya ta samar da cigaba ta fannin hanyoyinta na sadarwa, duba da yadda da yawa 'ya' yan kungiyar s**a sami halartar taron fiye da yadda yake kasancewa a shekarun baya, inda ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon cigaban da aka samu.
Taron yayi armashi sosai, inda aka samu halartar membobin kungiyar daga sassan Jihar nan da dama.
Write by
Com. Mustafa baffariya
Treasure ll
Sign by
Murtala Garba sa,id
P r o 1
Yusuf Tijjani p r o 2
Comr. Jazuli Habibu Getso
P. R.O III
Reported by
Com. Umar Garba Sada
Member media and publicity committee
27h July, 2021.