29/03/2025
Assalamualaikum.
Jita jitar Dakatar da Shugaban Kungiyar dalibai Garin sharada da Sakatarenta labarine Mara's tushe
Kungiyar Daliban Garin Sharada ta magantu Dan gane da wani rahoto na karya da ƴandadi social Media ke yaɗawa na dakatar da zabbaben shugaban daliban na garin
Sharada Comr Musa Mansur Sharada da sakataren sa Comr. Aminu Kabir.
Kungiyar Daliban Garin Sharada tana sanar da kowa cewa wannan; sanarwa ko rahoto, ƙanzon kurege ne, kuma maras asali b***e tushe, wanda wasu marasa kishin wannan kungiya da garin sharada s**a hada, domin ɓata sunan wannan ƙungiya mai albarka, ta qara da cewa: har izuwa yanzu babu wani official takarda data ishe wa mahukuntan wannan kungiya mai albarka, sannan kuma wadanda s**a gabatar da wannan takarda suna cikin dakatarwar da aka musu a baya. Har yanzu basu zo sun kare kansu daga waccan tuhuma da ta janyo aka takatar dasu ba, b***e kuma har su dauki wannan mataki. Don haka; shugaban wannan kungiya zai bukaci majalisar wannan kungiya data gaggauta daukar matakin ladaftarwa akan Irin wannan wakilai masu neman bata sunan wannan kungiya mai albarka da masu goya musu baya.
A halin yanzu mai girma president da mataimakan sa sun shagaltu wajen kawo ayyukan ci gaba da kara darajar wannan kungiya mai albarka kamar su
1) Tattara Tarihin wannan kungiya.
2) Special Event (Inter-school Durbar)
3) Education Activities
I. Jamb training at SHASA standard extra moral lesson dake GGSS Aisha Ababule Sharada Fegi.
II. CBT training for Jamb candidates at SHASA secretariat.
III. Computer training at SHASA secretariat.
IV. Organizing spelling Bee Competition.
V. Organizing Inter School Quiz Competition.
VI. Inter Islamiyya Musabaqa.
Dadai sauransu.
Muna addu'a Allah ya kara temakawa wannan kungiya da shugabannin ta.
Ameeen thumma Ameen.
Nagode.
*Mai magana da yawun bakin Shugaban Kungiyar Daliban Garin Sharada.*
Comr. Yazid Idris Abubakar
29/03/2025