09/06/2022
. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai sarkin da yake kaddara abinda yaga dama ga wanda yaga dama a lokacin da yaga dama, wanda ya kaddara wa wannan makaranta mai albarka yin bikin saukar alqur’ani mai girma a jiya laraba 8/6/2022, tsira da amincin allah su kara tabbata ga shuga annabin tsira alaihissalamu wassalat.
Muna godiya ga mai martaba sarkin kano uban kanawa ,alfaharin kanawa ,mai horo abi allah , Alh aminu ado bayero bisa karrama wannan makaranta da sanya mata ranar sauka kuma ya karramata da halartarsa mai albarka, muna addu’a allah ya sakawa masa da alkhairi ya biya bukatunsa ya jikan magabatansa, allah yaja zamaninsa.
Kuma muna godiya ga mai martaba sarki bisa gwangaje dalibai masu sauka da alkur’anai izu sittin sittin da fatan allah yakai ladana karatun da duk za’ayi ga ruhin mai martaba sarki marigayi, allah yakai ga ruhin mai babban daki.
Muna godiya ga dukkan mahalarta da fatan kowa yaje gida lafiya allah ya sakawa kowa da alkhairi.
Album 1
9/6/2022